Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda aka fafata a wasannin mako na 18 a Premier

Muna kawo maku sharhi da bayanai ka-tsaye game da wasannin Premier mako na 18.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail

  1. Katin gargadi, Man City 2-1 Leicester

    An bai wa Ndidi katin gargadi.

  2. Sterling, Man City 2-1 Leicester

    Raheem Sterling ya samu Finareti 17 a Premier tun farkon fara buga gasar a watan Maris 2012, sama da duk wani dan wasa dake buga gasar.

  3. An dawo hutun rabin lokaci, Man City 2-1 Leicester

  4. An tafi hutun rabin lokaci, Man City 2-1 Leicester

  5. An kara minti '2, Man City 2-1 Leicester

  6. GOAL '42, Man City 2-1 Leiceste

    Gundogan ne ya zira kwallo ta biyu da bugun Finareti.

  7. An bai wa City Finareti, Man City 1-1 Leicester

    Gündogan ya dauka zai buga.

  8. De Bruyne, Man City 1-1 Leicester

    Ya bude wasu kofofin kuga shot da ya dade bai bude ba sai a wannan wasan.

  9. Katin gargadi

    Caglar Soyuncu ya karbi katin gargadi saboda ya janye De Bruyne.

  10. Man City 1-1 Leicester, Man City 1-1 Leicester

    Vardy ya ci Manchester City kwallo biyar a Premier tun daga 2014-15. Ya shiga sahun wadanda suka fi yawan zira mata kwallo tare da Sadio Mane.

  11. GOAL '30, Man City 1-1 Leicester

    Riyad Mahrez ne ya dada kwallo sai ta yi kararrawa a tsakanin kafafuan Soyunchu, abin da ya canza wa mai tsaron raga Schmeichel tunani kuma kwallon ta wuce babu yadda ya iya yi.

  12. Man City 0-1 Leicester, Man City 0-1 Leicester

    City ta fusata da alamun sai ta rama kwallonta hankalinta zai kwanta.

  13. GOAL '20 Vardyyyyyyyy, Man City 0-1 Leicester

    Jamie Vardy ya yi abin da ya saba. Dama daya kwallo daya.

    In ba Vardy ba wanene?

    Kwallo ta farko a raga ta farko ga Leicester City ta 17 kenan ga wanda ya fi kowa cin kwallo a kakar bana.

  14. Man City 0-0 Leicester City, Man City 0-0 Leicester City

    Kwallo ta fi zama a kafar City amma tsoron da ke da akwai shi ne, yadda Leicester ta kware a kai kora idon ana wasa da ita.

    Dama daya Jamie Vardy zai samu ya banbanta sakamakon wasa.

  15. Mahrez ya kama da wuta, Man City 0-0 Leicester City

    Mahrez kwallo yake buga wa irin ta cinnaka bai san na gida ba, ya zuwa yanzu shi ne ke bai wa Leicester Matsala a wannan wasa.

  16. De Bruyne, Man City 0-0 Leicester City

    De Bruyne ya dada kwallon ta daki turke.

  17. Man City 0-0 Leicester City, Man City 0-0 Leicester City

    Evans ya matukar kokari da ya hana Raheem Sterling buga kwallon.

  18. Man City 0-0 Leicester City, Man City 0-0 Leicester City

    Wannan wasa ne mai cike da kalubale.

    Idon City ta ci ta kara matsar Leicester a teburin gasar da tazarar maki daya tsakaninsu.

    Idon kuma Leicester ta ci zai zama ta kara yi wa City nisa da tazarar maki bakwai.

    Idon kuma aka tashi canjaras makin teburin na nan yadda yake maki hudu tsakainin kungiyoyin biyu.

    Ko anci Leicester City ko ta ci tanan a matsayi na biyu haka ita ma Manchester City ta na nan a matsayi na uku.

  19. An take wasa, Man City 0-0 Leicester City

  20. Tawagar Leicester