Canji kan anji, Everton 0-0 Arsenal
Koci Duncan Ferguson ya sake yin canji kan canji a karo na biyu a jere amma wannan karon Moise Kean da aka sauya a wasan baya shi ne ya karbi Tosun.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Muna kawo maku sharhi da bayanai ka-tsaye game da wasannin Premier mako na 18.
Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail
Koci Duncan Ferguson ya sake yin canji kan canji a karo na biyu a jere amma wannan karon Moise Kean da aka sauya a wasan baya shi ne ya karbi Tosun.
Lacazette ya yi satar gida
Alexanda Lacazette ya canji Aubameyang.
An bai wa Sigurdsson katin gargadi.
Everton ta yi canji - Moise Keane ya karbi Delph
Arsenal ta shiga tasku a minti na 67, inda Raicharlison ya shiurya wata kwallo a yadi na 18 dinsu, Calvin-Lewin ya buga ta dawo, aka sake bugawa ta daki jikin Chambers sannan ta fita kwana. Har sai da VAR ta duba ko 'yan bayan sun taba kwallo da hannu.
Irin wadannan damarmaki za su bai wa masu masaukin bakin nasara indai za su ci gaba da samun su.
Arsenal ta samu dama sai gudu ta ke yi a wasan musamman ta bangaren Nelson.
Matashi Joe Willock ya karbi matashi Smith Rowe.
Calvin-Lewin ya bugo kwallo daga bangaren dama amma 'yan Arsenal sun fitaer da ita waje. An bugo kwana amma babu hadari, David Luiz ya fitar da ita daga ragarsu.
Saka na taka rawar da ta dace a wannan wasa, duk da dai ya karbi katin gargadi amma hakan bai kashe karsashin dan wasan ba.
Aubameyang ya buga wa Pickford kwallo a kusa-kusa bayan bugun kwana da aka yi amma golan ya bige ta. Da tuni 1-0.
Shi ne hari na-ci na farko da aka kai a zagaye na biyu na wannan wasa.
Kocin Everton ya tube rigarsa irin yadda ya yi a wasan Manchester United, da alamun nasara yake nema ido rufe a wasan.
Kirin ya hana Chambers ya ci kwallo amma mai tsaron raga Pickford ya jefa kwallon kwana.
Da alamar Rana na damun golan.
Yeri Minna ya yi babban aikin hana Saka sheko kwallo daga bangaren hagu, inda ya buge ta zuwa bugun kwana.
Daga Arsnal har Everton za su yi wasansu na gaba ne da sabbin masu horaswa kamar yadda suke na yau da na rikon kwarya.
Carlo Ancelotti a Everton yayin da Mikel Arteta zai karbi Arsenal.
Dukkansu yanzu haka suna cikin filin wasan da ake yi.
Babu dai wadda ta yi canji a hutun rabin lokacin da aka tafi.
Daga Arsnal har Everton za su yi wasansu na gaba ne da sabbin masu horaswa kamar yadda suke na yau da na rikon kwarya.
Carlo Ancelotti a Everton yayin da Mikel Arteta zai karbi Arsenal.
Dukkansu yanzu haka suna cikin filin wasan da ake yi.
An tafi hutun rabin lokaci