Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda aka fafata a wasannin mako na 18 a Premier

Muna kawo maku sharhi da bayanai ka-tsaye game da wasannin Premier mako na 18.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail

  1. Man United ta sha kashi a hannun ta kasan teburi, Watford 2-0 Man Utd

    Manchester United ta sha kashi a hannun Watford da ke karshen tebur da ci 2-0.

    Wannan ce nasara ta biyu da Watford ta samu a kan Man United a gasar Premier - cikin wasa 13 da ta buga da United Watford ta yi rashin nasara sau 11.

    A minti 45 na farko babu wani abin a zo a gani da kungiyoyin suka taka domin kuwa ba kai hari na-ci ba ko daya.

    Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne kwallon ta sauya, inda Ismaila Sarr dan kasar Senegal ya jefa kwallo ta farko.

    Dan wasan dai ya buga kwallon ne ba tare da wata cikakkiyar dama ba, amma golan United De Gea ya yi mata kamun kaza kuma ta fada raga.

    David de Gea ya yi kuskuren da ya kai ga cin kwallo har sau shida tun fara kakar Premier ta bara, sama da kowanne mai tsaron raga kenan a Premier.

    Minti hudu da cin kwallon farko Sarr ya samu finareti ta bangaren Wan-Bissaka bayan ya doke shi, kuma babu bata lokaci alkalin wasa ya busa bugun daga-kai sai-mai-tsaron-raga.

    Troy Deeney ne ya ci finaretin, kuma ya ci kwallo a wasansa hudu cikin biyar da ya buga tsakaninsu da Man United a Premier a gida - dukkanninsu daga bugun finreti.

    Wannan ne karon farko ma da Watford ta ci kwallo a cikin wasa hudu a Premier ta bana.

    Duk da wannan nasarar da Watford ta samu har yanzu tana kasan teburi, makinta daidai da Norwich ta biyun karshe.

    Ita kuma Manchester United na nan a matsayi na takwas da maki 25.

  2. Wasa na gaba, Tawagar Chelsea

    Frank Lampard ya yi sauyi uku a tawagar da ta sha kashi a hannun Bournemouth a karshen makon da ya wuce.

    Marcus Alonso da Mateo Kovacic da Fikayo Tomori sun maye gurbin Emerson da Jorginho da Christian Pulisic.

    Chelsea XI: Arrizabalaga, Azpilicueta, Rudiger, Zouma, Tomori, Alonso, Kovacic, Kante, Mount, Willian, Abraham

    'Yan benci: Caballero, Christensen, Jorginho, Hudson-Odoi, Pulisic, Batshuayi, James.

  3. Wasan da za mu kawo muku na gaba, Tawagar Tottenham

    Jose Mourinho bai yi wani wani sauyi a taagar da ta ci Wolves 2-1 a makon da ya wuce.

    Tanguy Ndombele, wanda ya gaza buga wasa uku, ya warke kuma yana benci.

    Tottenham XI:Gazzaniga, Aurier, Sanchez, Alderweireld, Vertonghen, Sissoko, Dier, Lucas Moura, Alli, Son Heung-Min, Kane.

    'Yan benci: Vorm, Rose, Winks, Lo Celso, Foyth, Eriksen, Ndombele

  4. Wasa ya kare, Watford 2-0 Man Utd

    Manchester United jiya i yau.

  5. Man Utd ta raba filin biyu, Watford 2-0 Man Utd

    An tare a bangaren Watford amma wasan bai sauya ba United na neman yadda za ta sa ko kwallo daya ne a raga.

  6. Rashfoooord, Watford 2-0 Man Utd

    Ben Foster ya hana Rashford zira kwallo mai kyau a raga daga yadi na 8.

  7. Watford 2-0 Man Utd, Watford 2-0 Man Utd

    Tun bayan shigowar Pogba wasan United ya sauya an dan samu ci gaba kadan.

    Pogba ya buga dogon fasin zuwa ga matashin yaro Greenwood, sai dai dan wasan ya buga kwallon ta yi yawa, ta haura raga.

  8. Wasan da za mu kawo muku na gaba, Tawagar Tottenham

    Jose Mourinho bai yi wani wani sauyi a taagar da ta ci Wolves 2-1 a makon da ya wuce

    Tanguy Ndombele, wanda ya gaza buga wasa uku, ya warke kuma yana benci.

    Tottenham XI:Gazzaniga, Aurier, Sanchez, Alderweireld, Vertonghen, Sissoko, Dier, Lucas Moura, Alli, Son Heung-Min, Kane.

    'Yan benci: Vorm, Rose, Winks, Lo Celso, Foyth, Eriksen, Ndombele

  9. Wasa na gaba, Tawagar Chelsea

    Frank Lampard ya yi sauyi uku a tawagar da ta sha kashi a hannun Bournemouth a karshen makon da ya wuce.

    Marcus Alonso da Mateo Kovacic da Fikayo Tomori sun maye gurbin Emerson da Jorginho da Christian Pulisic.

    Chelsea XI: Arrizabalaga, Azpilicueta, Rudiger, Zouma, Tomori, Alonso, Kovacic, Kante, Mount, Willian, Abraham

    'Yan benci: Caballero, Christensen, Jorginho, Hudson-Odoi, Pulisic, Batshuayi, James.

  10. Pogbaaa, Watford 2-0 Man Utd

    Paul Pogba ya dada kwallo amma Foster ya kame ta caraf.

  11. United ta kara canji, Watford 2-0 Man Utd

    Scott McTominay ya fita Mata ya maye gurbinsa.

  12. '70, Watford 2-0 Man Utd

    Rashford ya jibga wa Ben Foster kwallo daga bugun tazara, sai dai mai tsaron ragar ya dawo da ita.

  13. Watford ta yi canji, Watford 2-0 Man Utd

    Wannan ne canji farko.

    Doucoure ya fita Chalobah ya shigo.

  14. De Gea, Watford 2-0 Man Utd

    Tun fara wasan Premier bara, babu wani dan wasa da ya yi kuskuren da ya kai da cin kwallo kamar golan United David de Gea wanda ya yi kuskure 6.

  15. '67, Watford 2-0 Man Utd

    Martial ya buga kwallo amma 'yan bayan Watford ba su bari ta je ko'ina ba.

    An bugo kwana amma United ba ta amfana da ita ba.

  16. Murna, Watford 2-0 Man Utd

    Kwallo biyu cikin minti hudu.

  17. Troy Deeney, Watford 2-0 Man Utd

    Troy Deeney ya zira kwallo a wasansa hudu cikin biyar da ya buga tsakaninsu da Man United a Premier a gida, kuma duka daga bugun finreti ya ci su.

    Wannan ne karon farko ma da Watford ta ci kwallo a cikin wasa hudu.

  18. United ta yi canji, Watford 2-0 Man Utd

    Pogba ya karbi Lingard.

  19. Watford 2-0 Man Utd, Watford 2-0 Man Utd

    Abin tambayar anan cire James ne ya kamata ko kuma sauya Ligard da Martial da ba sa komi a wasan?

  20. United ta yi Canji, Watford 2-0 Man Utd

    Mason Greenwood ya karbi Daniel James