Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda aka fafata a wasannin mako na 18 a Premier

Muna kawo maku sharhi da bayanai ka-tsaye game da wasannin Premier mako na 18.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail

  1. GOAL '23, Brighton & Hove Albion 0 - 1 Sheffield United

    Bayan kashe kwallon John Egan da aka yi, yanzu Oliver McBurnie ya jefa wata kuma alkalin wasa ya karba.

  2. GOAL '21, Aston Villa 0-1 Southampton

    Ings ne ya ci wa Southampton kwallon.

  3. GOAL, Norwich 1-0 Wolves

    Cantwell ya zira wa Wolves kwallo a raga. Matashin dan wasan Ingila bai yi wata-wata ba ya ci kwallon a minti na '17.

  4. An tilasata wa Aston Villa yin canji da wuri, Aston Villa 0-0 Southampton

    Wasan John McGinn ya zo karshed bayan da alama ya ji rauni a idon-sawunsa. Villa ba ta ji dadi ba yayin da aka sako Marvelous Nakamba ya maye gurbinsa.

  5. An take wasa shida

    • Everton 0-0 Arsenal
    • Aston Villa 0-0 Southampton
    • Bournemouth 0-0 Burnley
    • Brighton 0-0 Sheffield United
    • Newcastle 0-0 Crystal Palace
    • Norwich 0-0 Wolves
  6. Arsenal ta tashi wasa babu ci, Everton 0-0 Arsenal

    Wasa ya tashi babu ci tsakanin Arsenal da Everton a filin wasa na Goodison Park a makon Premier na 18.

    Wannan ne wasa na farko da aka tashi ba tare da an zira wa Arsenal kwallo ba a cikin 15 da ta buga na baya-bayan nan a Premier. Sai da aka yi minti 44 Arsenal ba ta kai hari na-ci ba, wanda shi ne mafi tsawo da ta taba yi a Premier tun watan Mayun 2015.

    Everton ta yi yunkurin samun maki uku ganin cewa a gidanta ake yin sa, sai dai ba ta amfana da damarmakin da ta samu ba duk da cewa ba su da yawa.

    Masu horarwa na rikon kwarya Duncan Ferguson da kuma Freddie Ljungerg ne suka jagoranci kungiyoyin kuma shi ne wasansu na karshe a matsayin kociyoyi a kumngiyoyin.

    Tun a jiya Juma'a Arsenal ta bayar da sanarwar daukar Mikel Arteta domin maye gurnbin Unai Emery, yayain da shi kuma Carlo Ancelotti zai maye gurbin Marco Silva a Everton.

    Yanzu haka Arsenal tana mataki na 9 a teburi da maki 23, yayin da Everton take mataki na 15 da maki 19.

  7. Tawagar Southampton, Aston Villa ? - ? Southampton

  8. Tawagar Aston Villa, Aston Villa ? - ? Southampton

  9. Tawagar Sheffield United, Brighton & Hove Albion ? - ? Sheffield United

  10. Tawagar Brighton, Brighton & Hove Albion ? - ? Sheffield United

  11. Tawagar Bournemouth, AFC Bournemouth ? - ? Burnley

  12. Tawagar Burnley, AFC Bournemouth ? - ? Burnley

  13. Arsenal, Everton 0-0 Arsenal

    Wasa ya tashi babu ci, amma gaskiya ban tsammaci za a tashi haka ba.

    Wannan ne wasa na farko da aka tashi ba tare da an zira wa Arsenal kwallo ba a cikin 15 da ta buga na baya-bayan nan.

  14. Kocin rikon kwarya, Everton 0-0 Arsenal

    Dole a yaba wa Ferguson bisa kokarin da ya yi a wasannin da ya rike Everton a Premier.

    Watakil hakan ya bude masa damar samun aikin horaswa a wata kungiyar a nan gaba, amma dai ana sa ran zai yi aiki da Ancelotti a Everton din.

    A sauka Lafiya Duncan Ferguson da Freddie Ljunberg.

  15. An tashi daga wasa, Everton 0-0 Arsenal

  16. Ragas, Everton 0-0 Arsenal

    Chambers da Richarlison sun yi zubar gado bayan tashi neman kwallo da suka yi a sama.

  17. Katin gargadi, Everton 0-0 Arsenal

    An bai wa Willock katin gargadi sakamakon ketar da ya yi.

  18. Katin gargadi, Everton 0-0 Arsenal

    Wai me Arsenal ke kokarin yi ne haka, sai taba bal ake a baya.

    An bai wa Calum Chambers katin gargadi bayan ya gaza buga kwallon da aka ba shi, maimakon haka ya buga kafar Mason.

  19. An kara minti '3, Everton 0-0 Arsenal