Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda aka fafata a wasannin mako na 18 a Premier

Muna kawo maku sharhi da bayanai ka-tsaye game da wasannin Premier mako na 18.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail

  1. , Watford 0-0 Man United

    Man United ta fara kai kora amma 'yan bayan Watforrd suna ci gaba da tsare gida.

    Babu wani tabbas ko Man United za ta guje wa rashin nasara a karo na biyar bayan ta sha kashi sau hudu a wannan kakar.

    Amma na tabbata tawagar za ta yi bakin kokarinta.

  2. Ole Gunnar Solskjae, Watford 0-0 Man Utd

    Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjae" yana da matukar muhimmanci dawowar kowa daga ciwo"

    Pogba na daya daga cikin manyan 'yan wasanmu kwararru, yau yana cikin tawagarmu."

  3. , Watford 0-0 Man United

    Watford ce ta fara bugo kwana a wasan sai dai kwallon da Will Hughes ya bugo ba ta da wani hadari ga United.

  4. Rawar da kungiyoyin suke takawa, Watford 0-0 Man United

  5. Barka, Watford 0-0 Man United

    Jama'a barkanku da shigowa ci gaban wasannin mako na 18 a Premier Ingila.

  6. Man City ta gwada wa Leicester kwanji, Man City 3-1 Leicester

    Manchester City ta lallasa Leicester City da ci 3-1 ta kuma rage maki uku da ke tsakaninsu yayin suke rububin zama a cikin 'yan hudun saman teburi.

    Tun daga farko har karshe City ce ta rike kwallon da kaso mai yawa.

    Leicester ce ta fara jefa kwallo a wasan ta kafar dan wasanta Jamie Vardy a minti na 22 da fara wasan.

    Wannan ce dai kwallo ta 17 ga dan wasan da ke kan gaba a yawan kwallaye a gasar Premier, kuma yana cikin wadanda suka fi yawan cin Mancester City a gasar shi da Sadio Mane.

    Bayan minti takwas da cin kwallon sai tsohon dan wasan kungiyar ta Leicester Riyad Mahrez ya farke wa City a minti na 30.

    Manchester City ta ci gaba da kai hare-hare ta ko'ina, abin da yasa ta samu finareti ta kafar dan wasan gabanta Raheem Sterling.

    Ilkay Gundogan ne ya buga finaretin kuma kafin hutun rabin lokaci wasa ya zama 2-1.

    A minti na 69 da dawowa De Bruyne ya tayar da kayar baya, ya kai wata kwallo cikin yadi na 18 inda Gabriel Jesus ya samu damar kara ta uku a ragar Leicester kuma nan take wasa ya koma 3-1.

    Kwallon da ya ci ita ce ta farko da ya ci wa Manchester City a wasa 12 na gida a duka gasar da take bugawa, tun wacce ya ci a wasan Schalke 04 a watan Maris - duk 14 da ya ci wa kungiyar kafin yau ya ci ne a wasan City na waje.

    Yanzu dai maki daya ne kacal ya rage tsakanin Leicester City da Manchester City a teburin Premier, inda Liverpool ta ba su tazarar maki 10.

  7. Wasa ya kare, Man City 3-1 Leicester

  8. Man City ta yi canji, Man City 3-1 Leicester

    De Bruyne ya fita ya bai wa Aguero ya dana.

  9. Man City ta yi canji, Man City 3-1 Leicester

    An cire Sterling an sako Foden.

  10. Man City ta yi canji, Man City 3-1 Leicester

    Ikay Gundogan ya fita an sako Rodrigo

  11. Gabriel Jesus, Man City 3-1 Leicester

    Kwallo ta farko kenan da Gabriel Jesus ya ci wa Manchester City a wasa 12 na gida a duka gasar da take buga wa, tun wacce ya ci a wasan Schalke a watan Maris. Ko wacce cikin 14 da ya ci wa kungiyar kafin yau, ya ci ne a wasan da City ke zuwa bakunci.

  12. Leicester ta yi canji, Man City 3-1 Leicester

    Praet ya shigo a madadin Tielemans.

  13. Katin gargadi, Man City 3-1 Leicester

    Gundogan ya karbi katin gargadi, bayan doke Vardy yayin kai wata kora.

  14. Kwana, Man City 3-1 Leicester

    Kwana biyar City ta dakko Leicester kuma na da daya.

  15. GOAL '68, Man City 3-1 Leicester

    Gabriel Jesus ne ya kara ta uku.

    Wake ne kawai ke tashi a Etihad.

    Da alamu wasa ya kare domin Leicester ba ta muga kwallon da za ta iya farkewa.

  16. Leicester na ganin ta kanta, Man City 2-1 Leicester

    Hari kawai ake kai wa Leicester, kalli yadda ake buga kwalon a bangarenta.

  17. Leicester ta yi canji, Man City 2-1 Leicester

    Barnes ya fice Albrighton ya shiga.

  18. Barnes na bukatar canji, Man City 2-1 Leicester

    Bayan wani hari da aka kai Barnes ya hade da golan City Ederson ya kuma sau rauni.

  19. Katin gargadi, Man City 2-1 Leicester

    De Bruyne ya karbi katin gargadi saboda rashin da'a.

  20. Mahrez ya kai hari, Man City 2-1 Leicester

    Daga Mendy zuwa De Bruyne da nan kuma zuwa Mahrez ganin birgewa kwallon.