Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda aka fafata a wasannin mako na 18 a Premier

Muna kawo maku sharhi da bayanai ka-tsaye game da wasannin Premier mako na 18.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail

  1. Tawagar Manchester City

  2. An ci kwallo a dukkanin wasannin yau ban da na Arsenal.

    Muna tafe da wasa tsakanin Manchester City da Leicester City da karfe 6:30.

    Muna maganar vsu Jamie vardy ne da Raheem Sterling da abokan aikinsu.

  3. An tashi daga wasa biyar

    • Aston Villa 1-3 Southampton
    • Bournemouth 0-1 Burnley
    • Brighton 0-1 Sheffield United
    • Newcastle 1-0 Crystal Palace
    • Norwich 1-2 Wolves
  4. An tashi daga wasa, Brighton 0-1 Sheffield United

  5. Wasa ya kare, Norwich 1-2 Wolves

  6. Wasa ya kare, Bournemouth 0-1 Burnley

  7. Wasa ya kare, Newcastle United 1 - 0 Crystal Palace

  8. An tashi daga wasa, Aston Villa 1-3 Southampton

  9. Jack Grealish dai, Aston Villa 1-3 Southampton

    Jack Grealish ya sake dada kwallo daga nesa, duk da cewa wannan karon ba ta shiga ba amma da kyar gola Alex McCarthy ya ture ta.

  10. Katin gargadi, Norwich 1-2 Wolves

    An bai wa Matt Doherty katin gargadi.

  11. Minti '6 aka kara, Norwich 1-2 Wolves

  12. GOAL '90+2, Bournemouth 0-1 Burnley

    Jay Rodriguez ya ci cikin mintinan karshe, kamar ba za a ci kwallo a wasan ba. kwallo mai cike da zakwadi da murna.

  13. Jack Grealish, Aston Villa 1-3 Southampton

    Jack Greelish ya taimaka an ci kwallaye a kakar bana sama da dukkanin 'yan wasan kasar Ingila. Ya ci kwallo 5 sannan ya taimaka an ci 4.

  14. Katin gargadi, Newcastle United 1 - 0 Crystal Palace

    Miguel Almiron ya karbi katin gargadi saboda cire riga da ya yi yayin murna.

  15. Southampton ta yi canji, Aston Villa 1-3 Southampton

  16. Sheff Utd ta yi canji, Brighton 0-1 Sheff Utd

    An cire Norwood an sako Mo Besic

  17. GOAL '82, Newcastle 1-0 Crystal Palace

  18. GOAL '80, Norwich 1-2 Wolves

    Raul Jimenez ya kara zira ta biyu a ragar Norwich.

  19. GOAL '75, Aston Villa 1-3 Southampton

    Jack Grealish ya ci kwallo mai kyan gaske bayan 'yan bayan Southampton sun tsige ta daga bugun kwana, shi kuma ya ajiye ta a kirji sannan ya shauda ta raga.

    Ko za su farke?

  20. Alkalin wasa, Norwich 1-1 Wolves

    Na'urar da take taimakawa alkalin wasa ta hannunsa ce ta fado, ta kuma ja tsaiko game da wasan, amma ana kan gyara masa domin tabbatar da zai ji abin da ake fada daga dakin duba kwamfuyuta.

    Ga shi nan ma ana sauya ta duka ya kuma dawo.

    Wasa ya ci gaba.