Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda aka fafata a wasannin mako na 18 a Premier

Muna kawo maku sharhi da bayanai ka-tsaye game da wasannin Premier mako na 18.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail

  1. Brighton 0-1 Sheff Utd, Brighton 0-1 Sheff Utd

    Har da wadannan kwallo biyu da Sheffield United ta ci Brighton a yau, kungiyar ta ci kwallo hudu a wannan Premier bayan alkalin wasa ya bayar sai na'urar VAR ta hana, sama da kowanne kulob a kakar ta bana.

  2. Patrick van Aanholt, Newcastle 0-0 Crystal Palace

    Patrick van Aanholt ne tauraron Palace a yau din nan. Dan kasar Netherlands din ya bugo wata kwana mai hadarin gaske amma sai dai ta yi kadan, da tuni ya ciu kwallo da kansa daga bugun kwana.

  3. Sheff Utd ta yi canji, Brighton 0-1 Sheff Utd

    Oliver McBurnie ya fita Lys Mousset ya shigo a madadinsa.

  4. GOAL '60, Norwich 1-1 Wolves

    Romain Saiss ya rama wa Wolves kwallonta.

  5. '60, Brighton 0-1 Sheffield United

    Sheffield United ta zira kwallo a raga amma na'urar VAR ta hana. Ina ganin da tuni Brighton ta jiyo kanshin shan kashi duk da cewa a gidantra ake wannan wasa.

  6. GOAL, Aston Villa 0-2 Southampto3

    Shikenan!

    Danny Ings ya kara kwallo ta uku.

  7. Brighton ta yi canji, Brighton 0-1 Sheffield United

    Brighton ta yi sauyi a hutun rabin lokaci - an sako Aaron Connolly da Glenn Murray kuma aka cire Leandro Trossard da Pascal Gross.

  8. An dawo hutun rabin lokaci

    • Aston Villa 0-2 Southampton
    • Bournemouth 0-0 Burnley
    • Brighton 0-1 Sheffield United
    • Newcastle 0-0 Crystal Palace
    • Norwich 1-0 Wolves
  9. Cantwell, Norwich 1-0 Wolves

    Kwallon da Cantwell na Norwich ya ci ita ce ta 5 da ya zira a raga a bana.

    Matashin dan wasan Ingilan ya bayar da gudummawa wurin cin kwallo 7 a kakar bana (ya ci 5, ya bayar an ci 2) jumulla.

  10. Danny Ings, Aston Villa 0-2 Southampton

    Danny Ings na Southampton ya ci kwallo 6 a cikin wasa 7 na Premier da ya buga.

  11. Hutun rabin lokaci

    • Aston Villa 0-2 Southampton
    • Bournemouth 0-0 Burnley
    • Brighton 0-1 Sheffield United
    • Newcastle 0-0 Crystal Palace
    • Norwich 1-0 Wolves
  12. An tafi hutun rabin lokaci, Brighton & Hove Albion 0 - 1 Sheffield United

  13. An tafi hutun rabin lokaci, Norwich City 1 - 0 Wolverhampton Wanderers

  14. An tafi hutun rabin lokaci, Newcastle 0-0 Crystal Palace

  15. Ba kasafai ba, Norwich 1-0 Wolves

    Pukki ya samu kwallo mai kyau amma ya zubar, wannan abu ne da ba kasafai ake ganin shi ba. Yana buga kwallo sai ga ta caraf a kirjin golan Wolves Rui Patricio.

  16. Newcastle 0-0 Crystal Palace, Newcastle 0-0 Crystal Palace

    Luka Milivojevic ya buga kwallon amma ta tashi sama, a wani bugan tazara da Crystal Palace ta samu.

  17. Newcastle 0-0 Crystal Palace, Newcastle 0-0 Crystal Palace

    Wasan da alamu karfi ya zo daya.

  18. AFC Bournemouth 0 - 0 Burnley, AFC Bournemouth 0 - 0 Burnley

    Har yanzu Ryan Fraser na kwance bayan doke shi da James Tarkowski ya yi, da kyar zai iya ci gaba da wasan

  19. GOAL '31, Aston Villa 0-2 Southampton

    Jack Stephens ya kara ta biyu a ragar Aston Villa.

  20. Todd Cantwell, Norwich 1-0 Wolves

    Todd Cantwell ya taimaka wa kungiyarsa kai tsaye wurin cin kwallo 7 a wannan kakar, ya ci 5 ya bada biyu anci, sama da yadda ya yi a gasar Championship a bara, inda ya ci 1 ya 2 aka ci.