An ci gaba da wasa, Tottenham 0-2 Chelsea
Tottebham ta yi canji, Dier ya fita an sako Erikson a madadin shi.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Muna kawo maku sharhi da bayanai ka-tsaye game da wasannin Premier mako na 18.
Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail
Tottebham ta yi canji, Dier ya fita an sako Erikson a madadin shi.
Akwai babban aiki a gaban Tottenham an zira mata kwallo biyu a gidanta.
Bayan wani taho-mu-gama da aka yi tsakanin golan Tottenham Gazzaniga da dan bayan Chelsea Alonso, an duba VAR an gano golan ya yi wa dan wasan keta, abin da ya kai ga bugun daga-kai-sai-mai-tsaron-raga - Kuma Willian da ya ci kwallon farko shi ne ya kara ta biyu.
Golan ya tashi a sama kamar wani shaho.
Willian ya kara kwallo ta biyu. Chelsea za ta tafi hutun rabin lokaci da nasara.
Mourinho bai ga cin ba domin kuwa tuni ya bar fili kamar yadda ya saba.
Yau Tammy Abraham ya buya a wasan ba a ganinsa.
Dele All da Mateo Kovacic sun yi rigima a tsakiyar fili kuma lafari ya ba su katin gargadi - "gaba ma kwa kara," in ji lafarin.
Mousa Sissoko ya je har wajen Kepa mai tsaron ragar Chelsea ya yi taho-mu-gama da shi.
'Yan wasan biyu sun tashi bayan sun yi warwas a kasa.
An kare minti 30 na farko a zagayen farko na wasan.
An bai wa Zouma kati saboda ya hana wasa ya ci gaba.
Son ya buga kwallo sama - ba mamaki ta kai bene hawa na 3 - a cikin yadi na 18.
Kane ya kai hari kuma ba don kwallo ta yi sama da yawa ba da tuni 1-1.
Sissoko ya yi kokari da kwallon da ya haddasa.
Idon Chelsea ta ci wannan wasan ba karamar tazara za ta kara bayarwa ba tsakaninta da kungiyoyin da ke harin matsayi na hudu, wadnda suka hadar da Tottenham din ita kanta, Manchester Unite Wolves da kuma Sheffield United.
Sanchez ya saka wa Mount matsi kuma ya hana shi cin kwallon da Abraham ya ba shi a cikin yadi na 18.
Chelsea ta matse Spurs zuwa yanzu.
Eric Dier ya hana Willian bugo kwallo daga bangaren dama. An bugo kwana amma 'ayn Tottenham sun tsige ta.
Jose Mourinho bai taba yin rashin nasara ba a wasa 13 da ya buga da kungiyoyin da ya taba jagoranta a baya - ya ci wasa 12 - ciki har da wasa uku da ya ci Chelsea lokacin yana Inter Milan sannan ya ci Man United sau biyu.
Willian ya dada kwallon kuma ta ratsa ta tsakanin yan baya ta shige.
Chelsea ta yi bugun kwana na farko amma babu hadari ga Tottenham.
Tammy Abraham ya buga shot din farko a wasan, amma ba za ku so ganin shot din ba domin babu kyan gani.
Na tabbata ba abin da zai kuma maimaitawa kenan ba idan ya samu wata damar.
Han kalin masu masaukin baki kwance ya ke.