Watford 2-0 Man Utd, Watford 2-0 Man Utd
Lissafi ya kwace wa United, kwallo biyu a ragarta.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Muna kawo maku sharhi da bayanai ka-tsaye game da wasannin Premier mako na 18.
Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail
Lissafi ya kwace wa United, kwallo biyu a ragarta.
Wan-Bissaka ne ya hambare Isama'ila Sarr a cikin yadi na 18, ba wata-wata alkalin wasa ya busa.
Deeney ya hau kan kwallon, ya buga ya kori golan de Gea.
A irin wannan ranar ce a 2001, Ruud van Nistelrooy ya fara cin kwallo uku wato Hat-trick a wasan da United ta ci Southampton 6-1.
Wayne Rooney ne kawai ya fi shi yawan hat-trick a Premier inda ya yi 6 a United.
Da yawa daga magoya bayan United na jin inama ace har yanzu akwai irin wannan dan wasa a tawagarsu.
De Gea ya tafka kuskure.
Ismaila Sarr ne ya dada kwallo ta daki kafar Luke Shaw kuma ta nufi De Gea amma mai tsaron ragar ya kasa kama ta.
Duka bangarorin ba su yi canji ba, sannan kuma kar ku manta ba a kai hari na-ci ba a minti 45 na farko.
An tafi hutun rabin lokaci a filin wasa na Vicarage Road.
Deeney ya bige Lindelöf bayan Lindelöf din ya hana shi buga kwallo a cikin yadi na 18 din United.
An kara minti 1 a kan 45.
Abdoulaye Doucoure yana buga kwallo yadda ya kamata.
Saura kiris Doucouré ya kokarta amma bai iya take kwallon da aka bugo masa ba a cikin yadi na 18.
Har yanzu dai ba a buga shot na-ci ba.
Ba mamaki ci kawai za mu gani!
An bai wa Luke Shaw katin gargadi shima.
Shaw ya rike Sarr a bangaren dama, Watford ta samu bugun tazara mai kyau.
An bugo kwallon amma Harry Maguire ya fitar da ita.
An bai wa Etienne Capoue katin gargadi, wannan ne kuma katin farko da aka bayar a wasan.
Manchester United ta fi yawan rike kwallon, sai dai fasin din da take bayarwa ba ya kyau sosai.
Lingard ya zubar da kwallo mafi kyau da aka samua wasan nan - daga shi sai gola amma ya tashi kwallo sama a yunkurinsa na yin cin 'yan gayu.
Man United ta matsa wa bangaren hagun nan, ina iya ganin Wan-Bissaka da Martial da Lingard suna warkajaminsu.
Martial ya yi satar gida. Amma wasan ya yi kyau sosai duk da cewa babu kowa a cikin raga idan ya bugo.
Ya zuwa yanzu wasan dai babu wani abin a zo a gani cikinsa, ba yawan hare-hare, kwallon ta fi yawa a tsakiyar fili.
Manchester United ta ci wasa 11 cikin 12 na Premier da ta buga da Watford - a kan Wigan ne kawai ta samu nasara sama da wannan, inda ta ci wasa 15 cikin 16 da ta buga da ita.
Luke Shaw ya dado kwallo cikin yadi na 18 din Watford amma babu kowa balle a zira ta a raga.
Har yanzu ba a kai hari-ci ba a wannan wasa.