Abubuwan da suka faru a Nigeria da sassan duniya kan coronavirus

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma wasu sassan duniya, musamman rahotanni kan annobar coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Coronavirus: Kamfanonin jiragen sama na dakatar da aiki a Najeriya

    Azman Air

    Asalin hoton, Azman Air

    Kamfanin ziirga-zirgar jirgen sama na Air Peace ya ce ya soke ayyukan jigilar fasinja a Najeriya na tsawon kwana 23 a yunkurinsa na kauce wa yaduwar coronavirus.

    Kamfanin ya ce dakatarwar za ta fara aiki ne daga ranar Juma'a 27 ga watan Maris.

    Shi ma kamfanin Azman ya sanar da dakatar da aiki na tsawon mako biyu.

    A wata sanarwa da ya fitar, kamfanin ya ce matakin zai fara aiki ne daga ranar Juma'a 27 ga Maris.

  2. Sabon shirin BBC kan coronavirus

    BBC

    Muna sanar da ku cewa za mu dinga kawo muku labarai da bayanai a bidiyo kan annobar coronavirus daga ranar Litinin zuwa Juma'a.

    Za mu fara ne daga yau Laraba, kuma Abdulbaki Jari ne zai dinga bayani a bidiyon. Ku kasance da BBC Hausa a ko yaushe.

    Haka kuma sauran sassan BBC na Igbo da Yoruba da Pidgin ma za su dinga sakawa a shafukansu na sada zumunta.

  3. Coronavirus: Atiku ya nemi gwamnati ta bai wa kowanne magidanci N10,000

    Alhaji Atiku Abubakar

    Asalin hoton, Atiku Abubakar

    Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya bukaci gwamnatin Shugaba Buhari ta bai wa duk wani magidanci a kasar tallafin N10,000 domin rage radadin annobar coronavirus.

    A nasa bangaren,Atiku ya bayar da tallafin naira miliyan 50 domin yaki da annobar tare da yin kira ga 'yan majalisar dokokin Najeriya su dawo aiki "nan take" domin yin doka ta musamman kan bai wa 'yan kasar tallafi.

    Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi wannan kira ne ranar Laraba.

    "Yayin da muke da magidanta kusan miliyan 30 a Najeriya, ya kamata gwamnati ta samar da hanyoyin da za ta bai wa kowane magidanci naira 10,000 a matsayin tallafi na kayan abinci," Atiku ya bayyana a wata sanarwa da ya wallafa da kansa a shafinsa na intanet.

    Ya ce "kamfanin Priam Group ya bayar da naira miliyan 50 a madadina a matsayin tallafi".

    Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce wannan kudi wani bangare ne na kudirin dokar da majalisar tarayyar Najeriya ya kamata ta yi na musamman da ya kira "Stimulus Package Act" da zai tallafa wa 'yan Najeriya, musamman wadanda suka yi fama da cutar.

    Saboda haka ne Atiku ya yi kira ga 'yan majalisar su dawo bakin aiki "nan take" domin yin waccan doka.

  4. Gwamnan Edo ya yi gwajin coronavirus

    Godwin Obaseki

    Asalin hoton, Godwin Obaseki

    Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki ya ci gaba da aiki a ofishinsa duk da cewa ya yi gwajin cutar coronavirus.

    Gwamnan wanda ya wallafa hotonsa a shafin Twitter da tsakar ranar Laraba, ya ce babu abin da zai hana shi aiki.

    "Ina ci gaba da aiki a killace yayin da nake jiran sakamakon gwajin cutar Civd-19," in ji gwamnan.

    Tun a ranar Talata ne gwamnan ya haramta taron mutanen da suka wuce 20 tare da rufe kasuwanni a jihar.

    Shi ma gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi ya yi gwajin, inda yake jiran sakamako.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  5. Coronavirus ta hana biyan albashi a Adamawa

    Ahmadu Fintiri

    Asalin hoton, @AhmaduFintiri

    Gwamnatin Jihar Adamawa a Najeriya ta ce za ta jinkirta biyan ma'aikata a jihar albashi mafi karanci na naira 32,000 sakamakon matsin tattalin arziki da cutar coronavirus ta saka ta a ciki.

    Daraktan yada labaran gwamnan jihar, Mista Solomon Kumangar ya shaida wa BBC cewa halin da suke ciki yanzu ya sa ba za su iya cika alkwarin da suka yi wa 'yan kungiyar kwadago ba.

    "Da mun yi wa 'yan kungiyar kwadago alkawarin cewa za mu fara biyansu amma ganin abin da wannan cutar ta haifar shi ne gwamnati ta dauki matakin cewa dole ta rage kashe kudade, wanda kuma ya hada da albashin ma'aikata," Solomon Kumangar ya fada.

    Gwamnatin ta bayyana cewa za ta waiwayi alkawarin da ta yi wa ma`aikatan na biyan sabon albashi mafi kankanta ne idan al`amura sun daidaita a nan gaba kadan.

    Kazalika ta ce sai da ta tattauna da kungiyar kwadagon jihar kafin ta yanke shawarar jinkirta biyan sabon albashin.

  6. Coronvirus: Guardiola ya bai wa Spain tallafin ₦400m

    Pep Guardiola

    Asalin hoton, Getty Images

    Kociyan Manchester City, Pep Guardiola ya bayar da tallafin yuro miliyan daya (kusan naira miliyan 400) domin yaki da coronavirus a kasar Sifaniya.

    Guardiola, wanda ke gidansa na Sifaniya, yana aiki da lauyoyinsa domin tsara yadda za a yi amfani da kudin.

    Za a bai wa kwalejin kiwon lafiya ta Barcelona ne da kuma gidauniyar Soler Daniel domin wayar da kai game da cutar.

    Sifaniya ce kasa ta biyu da cutar ta fi shafa a duniya - bayan Italiya - bayan samun rahoton wadanda suka mutu a kasar sun zarce na China.

    Mutum 4,434 ne suka mutu a kasar, yayin da 47,610 ke dauke da cutar.

  7. Mali ta samu mutanen farko da suka kamu da coronavirus

    Coronavirus in Mali

    Asalin hoton, get

    Kasar Mali ta tabbatar da samun mutum biyu da suka kamu da cutar coronavirus wadanda dukkannin su ka koma kasar daga balaguro a Faransa.

    Mutanen dai akwai 'yar shekara 49 a birnin kasar Bamako da kuma wani dan shekara 62 mazaunin Kayes da ke yammacin Mali.

    Gwamnatin kasar dai ta ce za ta dauki nauyin kula da su.

    Ana fargabar kasar ta Mali wadda take fama da yake-yake ka iya fuskantar matsala

  8. Coronavirus: Kada ya cinye mutum bayan ya keta dokar hana fita a Rwanda

    Kada a Rwanda

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani mutum a kasar Rwanda da ya keta dokar hana fita ya fita kafin kifi ya mutu sakamakon wani kada da ya hadiye shi, kamar yadda magajin garin Kamonyi ya shaida wa BBC.

    Alice Kayitesi ya ce lamarin ya faru ne a safiyar ranar Laraba a kogin Nyabarongo.

    "Ya karya dokar zama a gida, yana cikin mutane 'yan kalilan da suka karya dokar dakile coronavirus," in ji Kayitesi.

    Mahukunta a Rwanda sun saka dokar hana fita ranar Lahadi, yayin da Covid-19 ke ci gaba da addabar kasashen duniya.

    Rwanda ta tabbatar da mutum 40 da suka kamu da cutar zuwa yanzu - kasa ta biyu ke nan bayan Najeriya.

  9. Halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya

    Halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya:

    • Iran:Shugaba Hassan Rouhani ya ce gwamnati za ta kara tsaurara matakan dakile Covid-19. Ya ce a ciki akwai han zirga-zirgar jama'a wadanda za su zama "masu tsauri ga al'umma". Duk da cewa cutar ta fi gigita Iran sosai fiye da saura a yankin Gabas ta Tsakiya, kasar ba ta sanya dokar hana fita ba. Mutum 2,077 ne gwamnati ta ce cutar ta kashe kuma 27,017 ne ke dauke da cutar. Sai dai ana ganin adadin ya fi haka.
    • Isra'ila: Gwamnati ta sanya wasu karin dokoki da za su fara aiki daga karfe 5:00 (4:00 agogon Najeriya). Kafafen yada labaran kasar sun ce ana sa ran za a umarci mutane da kada su yi nisan mita 100 da gidajensu. Mutum biyar ne suka mutu a Isa'ila sannan 2,030 suka kamu.
    • Daular Larabawa (UAE): Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Emirates ne babban kamfani na farko da ya dakatar da aiki kwata-kwata saboda coronavirus. Hakan ya faru ne bayan UAE ta kulle dukkanin filayen jiragen samanta, sakamakon mutum 248 da suka kamu sannan biyu suka mutu
  10. Jordan ta sassauta dokar hana fita

    Gabas ta Tsakiya

    Asalin hoton, AFP

    A kasar Jordan, inda mutum 153 suka kamu da Covid-19, an sassauta dokar hana fita.

    A ranar Litinin ne gamnati ta ce ba za a bar mutane su fita daga gidajensu ba sannan kuma jami'an tsaro za su kai wa jama'a abinci kamar ruwa da burodi har gida.

    Amma a ranar Talata, Firai Minista Omar Razzaz ya ce za a kyale mutane su fito da rana amma ba a kan abin hawa ba domin zuwa sayayyar kayan abinci da kuma magunguna.

  11. Gwamnan Ekiti na jiran sakamakon gwajin coronavirus

    Fayemi

    Asalin hoton, Nigeria Presidency

    Gwamnan Jihar Ekiti Kayode Fayemi ya yi gwajin cutar coronavirus, yayin da tuni ya fara zaman kadaici bisa tsammanin ko yana dauke da cutar.

    Yanzu haka gwamnan yana jiran sakamakon gwajin da ya yi.

    Tun a daren Talata ne Gwamnan ya killace kansa sakamakon wata ganawa da ya yi da wasu mutum biyu, wadanda aka gano suna dauke da cutar, kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter.

    "Na yi gwajin Covid-19 bayan na killace kaina tun daga daren jiya (Talata). Lafiya kalau nake zuwa yanzu, amma na yi zaman tattaunawa da wasu mutum biyu da aka gano suna dauke da cutar."

    Kazalika, gwamnan ya yi kira ga sauran wadanda suka yi zaman tare da shi da su je su yi gwajin.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  12. Labarai da dumi-dumi, Yarima Charles ya kamu da cutar coronavirus

    Yarima Charles

    Asalin hoton, Getty Images

    Yarima Charles – wanda shi ne babban dan Sarauniya Elizabeth ya kamu da cutar coronavirus.

    Yariman mai shekaru 71 ya soma samun kulawar likitoci.

    Ya nuna alamun cutar amma kuma yana cikin koshin lafiya.

    A wata sanarwa da fadar sarauniyar Ingila ta fitar, ta ce "ya dade yana nuna alamun cutar amma kuma yana cikin koshin lafiya inda yake gudanar da ayyukansa daga gida a 'yan kwanakin da suka gabata."

    Mai magana da yawun fadar ya ce "mai dakin Yarima Charles ta yi gwaji amma kuma ba ta dauke da cutar ba."

    Sai dai sanarwar ta kara da cewa "babu wani tabbaci na inda Yarima ya samo cutar ta coronavirus sakamakon irin gogayyar da ya yi da mutane da dama a 'yan makonnin da suka gabata."

    Yanzu haka dai Prince Charles da mai dakinsa na killace a gidansu da ke Scotland.

  13. Zaman wariya a majalisar zartarwar Indiya

    Indiya

    Asalin hoton, @AmitShah

    Yayin zaman majalisar zartarwarsa, Firai Ministan Indiya, Narendra Modi ya ce dokar hana fita ce kadai maganin yaduwar coronavirus.

    Ya bayyana hakan a ranar Talata, inda ya ayyana dokar na tsawon kwana 21.

    Kamar yadda kuke iya gani, a majalisar zartarwar tasa sun yi zaman wariya ne domin kare kai daga kamuwa da cutar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  14. 'Farfesa Osinbajo bai harbu da coronavirus ba'

    Osinbajo

    Asalin hoton, Getty Images

    Mai bai wa shugaban Najeriya, shawara kan harkokin siyasa, Ujudu Babafemi ya ce sakamakon gwaji guda 10 da aka yi wa mataimakin shugaban, Farfesa Yemi Osinbajo sun nuna ba ya dauke da kwayar cutar coronavirus.

    A shafinsa na Facebook, Babafemi ya ce baya ga mataimakin shugaban kasar, dukkan masu taimaka masa ma sun tsira daga kamuwa daga cutar.

    Kafin nan dai mai taimaka wa farfesa Osinbajo, kan yada labarai, Laolu Akande ya wallafa cewa mataimakin shugaban na killace kansa kamar yadda hukumar lafiya ta duniya ta nuna.

    Ko a jiya ma sai da Laolu Akande ya wallafa wani hoton mataimakin shugaban yana gudanar da harkokinsa ta hanyar intanet sanye da takunkumin kariya.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  15. Halin da ake ciki a kasashen Turai

    Turai

    Asalin hoton, Twitter/@ajadmiah2

    Gwamnatoci a Nahiyar Turai na daukar tsauraran matakai na dakile yaduwar cutar coronavirus. Sai dai har yanzu akwai farbgabar cewa sai an kara zage dantse.

    Ga halin da ake ciki a wasu daga cikin kasashen da cutar ta fi kamari:

    • Italiya: Kasar da ta fi gigituwa daga cutar, ta kara girman hukuncin da ake yi wa duk wanda ya karya dokar dakile yaduwar cutar, abin da ya hada da tarar dubban yuro da daurin shekara biyar ga duk wanda yake dauke da cutar kuma ya ki killace kansa. Firai Minista Giuseppe Conte ya karyata batun cewa dokar hana fita za ta kai har watan Yuli.
    • Spain: Firai Minista Pedro Sanchez zai nemi majalisar dokokin kasar su tsawaita dokar ta-bacin da ake ciki na tsawon mako biyu nan gaba - har zuwa 11 ga Afrilu. Spain ce kasa ta biyu da cutar ta fi yi wa illa a Turai bayan Italiya, inda mutum fiye da 5,000 daga cikin 40,000 da suka kamu da cutar a kasar ma'ikatan lafiya ne.
    • Faransa: A ranar Talata ne Faransa ta zama kasa ta biyar da mutum sama da 1,000 suka mutu tun bayan barkewar annobar, kuma shugaban hukumar lafiya ta kasar Jerome Salomon ya ce adadin zai iya zarce haka. Mutum 1,000 din da suka mutu wadanda suka mutu a asibiti ne kawai.
  16. Coronavirus: Mutum 709 sun harbu da cutar a Afirka ta Kudu

    Cyril Ramaphosa

    Asalin hoton, Getty Images

    Alkaluman mutanen da cutar coronavirus ta harba sun kai 709 daga 544 da kasar ta sanar ranar Talata.

    Ministan lafiyar kasar, Zweli Mhinze ne dai ya sanar da hakan.

    Yanzu haka Afirka ta Kudun ce kasar da tafi kowacce yawan masu cutar a Afirka.

    Hakan ne ya sa jama'a yin rige-rigen sayen kayan abinci domin ajiye a gida saboda gudun ko-ta-kwana.

    Ana dai sa ran gwamnati nan ba da jimawa ba za ta sanar da tsauraran matakan dakile bazuwar cutar a cikin kasar da suka hada da umartar jama'a su kasance a cikin gidajensu kamar abin da ke faruwa a wasu kasashen Turai.

    A gobe Alhamis ne dai wannan zaman gidan zai fara aiki.

  17. Boko Haram ta kashe sojojin Chadi 92

    Chad

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban kasar Chadi ya ce mayakan Boko Haram sun kashe sojoji 92 a wani kazamin hari.

    Shugaba Idris Deby ya ce harin da aka kai a safiyar litinnin shi ne mafi muni a cikin shekaru biyar da mayakan ke kai hare-hare.

    Mista Deby ya ziyarci inda aka kai hari a yammacin Chadi da ke kusa da iyakokin Nijar da Najeriya.

    An kashe gomman sojojin Chadi tun da hare-haren Boko Haram ya yadu tsakanin kasashen da suka hada iyaka da Najeriya a 2015, sannan akwai dubbai da suka rasa matsugunansu

  18. Mutum '2000' ne suka kamu da coronavirus a Afirka

    Coronvirus

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya wallafa cewa akalla akwai mutum 2000 da suka kamu da cutar coronavirus a nahiyar Afirka, inda mutum 62 suka mutu sakamakon cutar.

    Kasar Afirka ta kudu ce dai take da yawan alkaluman wadanda suka kamu inda mutum 709 suka harbu.

    Kasashen Soa Tome and Principe da Kamaru sun sanar da mutuwar farko sakamakon cutar.

    'Yan Kamaru na kuma yin alhinin fitaccen mawakin nan dan kasar Dibango Manu wanda cutar ta yi ajali kasar Faransa.

    Rwanda ta sanar da samun mutum hudu da suka harbu, inda yanzu haka suke da jumullar mutum 40.

    Yanzu haka Najeriya na da wadanda coronavirus ta harba guda 46.

    Rahotanni na cewa shugaban kasar Muhammadu Buhari yana killace, sannan kuma shugaban ma'aikatansa, Abba Kyari ya harbu da cutar.

    Daya daga cikin gwamnonin jihohin kasar, Bala Muhammad wanda shi ne gwamnan Bauchi, shi ma cutar ta kama shi.

    Ita kuwa Cote d'Ivoire na da mutum 73 da ke dauke da cutar.

    Ghana ma ta samu masu dauke da cutar ta coronvirus a cikin kasar guda 53 ya zuwa yanzu.

    A jamhuriyar Niger, mutum daya ya mutu sakamakon cutar.

  19. Coronavirus ta bulla a Libya

    Hukumar dakile yaduwar cututtuka a Libya ta sanar da bullar cutar coronavirus karo na farko a kasar.

    Wasu rahotanni da ba a tabbatar ba sun ce mutumin da ya harbu da cutar na kwance a asibitin birnin Tripoli.

    Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin da ke samun goyon-bayan kasashen duniya da bangaren 'yan hamayya da ke gabashin kasar sun kafa matakai masu tsauri, da rufe iyakokinsu na sama da kasa a makon da ya gabata.

    Akwai damuwar da ake nunawa ga fanin lafiyar kasar, ganin yadda yaki ya daidaita ta.

    Libya

    Asalin hoton, Getty Images

  20. Coronavirus: An wuce gona da iri a Brazil - Bolsonaro

    Jair Bolsonaro

    Asalin hoton, get

    Shugaba Jair Bolsonaro na Brazil ya zargi hukumomin jihohi da daukan matakai sama da kima a kokarin dakile yaduwar Coronavirus a kasar.

    A lokacin da yake jawabi a kafar talabijin din kasar, Bolsonaro ya kalubalanci matakin rufe makarantu, sannan ya ce akwai bukatar kasar ta koma yadda abubuwa suke a baya, ma'aikata su koma bakin aikinsu.

    Mista Bolsonaro ya fuskanci suka daga kwararru a fanin kimiyya da kuma 'yan kasar da dama da suka nuna fushinsu ta kowanne bangare, bayan kammala jawabannasa da suka kasance wa 'yan kasar banbarakwai.

    Wakiliyar BBC ta ce yana kammala jawabansa mutane suka soma kada murafan tukwane a cikin fushi daga saman benaye.

    Birnin na biyu mafi girma a kasar, Sao Paulo ya shiga mako na biyu ba shiga ba fita, duk da cewa shugaban kasar ya yi watsi da matakin