Abubuwan da suka faru a Nigeria da sassan duniya kan coronavirus
Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma wasu sassan duniya, musamman rahotanni kan annobar coronavirus.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail
Alkaluman coronavirus a nahiyar Turai
Alkaluman mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a nahiyar Turai na karuwa kamar wutar daji.
Hakan ne ya sa kungiyar Tarayyar Turai za ta yi taro amma ta kafar intanet.
Ga alkaluman wasu daga cikin manyan kasashen na tarayyar Turai:
Burtaniya - 9500+
Jamus - 37,300+
Faransa 25,200+
Italiya - 74,300+
Sipaniya - 49,700+
Ethiopia za ta saki fursunoni 4000 saboda coronavirus
Asalin hoton, Getty Images
Fiye da fursunoni hudu ne za su samu 'yanci a kasar Ethiopia a dai-dai lokacin da gwamnati take ci gaba da daukar matakan dakile bazuwar coronavirus.
Ministan shari'ar kasar ya fadi cewa fursunonin da ke daure kan wasu kananan laifuka da mata masu reno na daga cikin wadanda za a saki.
Har wa yau, 'yan kasashen waje da ake tuhuma da sumoga da fasakauri wadanda aka mayar da su kasarsu ta asali su ma za a sake su.
Daga cikin mutanen da za a saki har da dan jarida Fekadu Mahtemework.
Kenya ta haramta safarar gwanjo saboda coronavirus
Asalin hoton, Getty Images
Kenya ta haramta yin safarar kayan gwanjo zuwa kasar wanda aka fi sani da suna mitumba a yunkurinta na yaki da yaduwar cutar cornavirus.
Jaridar Daily Nation da ake bugawa a kasar ta ambato sakatariyar kasuwancin kasar Betty Maina, tana cewa: "An dakatar da safarar kayan gwanjo nan take domin kare lafiyar 'yan kasar Kenya da kuma karfafa kasuwar cikin gida."
Mutane da dama na sayen kayan da aka taba yin amfani da su a Turai da Kudancin Amurka da China - saboda sun fi saukin kudi sama da sababbi.
Kazalika 'yan kasar da dama sun dogara da kasuwancin mitumba domin samun na kai wa baka.
A ranar Laraba ne Ms Maina ta gana da 'yan kasuwar gwanjon, inda ta karfafa masu gwiwa tare da shawartarsu da su sayi kayan daga ma'aikatun cikin gida.
Sai dai wasu ba su ji dadin matakin ba. Dan majalisa mai wakiltar Kamukunji a kasar, inda cibiyar kasuwar mitumba take, ya bayyana rashin dadinsa a Twitter.
"Duk da cewa dole ne gwamnati ta dauki matakin kare rayukan al'umma, amma na yi mamakin rufe kasuwar Mitumba. Dubban 'yan Kenya sun dogara da ita domin samun kudin shiga."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Coronavirus: India za ta fitar da $22.6bn domin tallafawa talakawa
Asalin hoton, Getty Images
Kasar India ta sanar da fitar da $22.6bn domin tallafa wa talakawan kasar a yayin da ake ci gaba da daukar matakai masu tsauri domin dakile coronavirus.
ministar kudin kasar Nirmala Sitharaman ta ce za a yi amfani da kudaden ga mutanen da ke bukatar tallafin gaggawa da ya hada da abinci kamar samar da shinkafa da alkama kyauta da kuma aike musu da kudaden da za su rike a hannayensu.
Gwamnatin ta kuma ce za ta dauki nauyin magunguna da kulawa ta musamman ga dukkanin ma'aikatan lafiyar kasar da ke kula da masu dauke da cutar coronavirus.
Dama dai tattalin arzikin kasar na daf da shiga wani hali kafin rufe kasar sakamakon cutar ta coronavirus.
Kawo yanzu dai India ta samu mutuwa 13 sakamakon annobar coronavirus sannan tana da mutum 673 da suka kamu da ita.
Ana kuma fargabar cewa cutar ka iya yaduwa a fadin kasar.
Coronavirus: Halin da Burtaniya ke ciki
Asalin hoton, Getty Images
Idan muka leka kasar Burtaniya, za mu ga cewa kawo yanzu an samu mutum 463 da suka mutu sakamakon cutar coronavirus.
An dai samu kari daga 422 da ake da su ranar Laraba kuma abin da hakan ke nufi shi ne a kullum ana samun karuwar mutuwar mutum 41 fiye da yadda yake a makonnin da suka gabata.
Yawan masu dauke da cutar kuma ya kai 9,529 a ranar Laraba sabanin 8,077 a ranar Talata.
An yi wa mutum 97,019 gwajin cutar, inda gwajin ya nuna mutum 87,490 ba su da kwayar cutar a jikinsu.
Coronavirus ta kashe mutum fiye da 1000 a Amurka
Asalin hoton, Getty Images
Yawan alkaluman mutanen da suka mutu sakamakon cutar coronavirus a Amurka sun zarta 1000.
Wasu sashen tattara alkaluma na jami'ar John Hopkins ne ya tabbatar da haka.
Yanzu haka kididdigar baya-bayan ta nuna mutum 1,050 ne suka mutu sannan an samu wadanda suka kamu 69,171 a fadin kasar.
Duk da wannan yanayin dai, shugaban Amurka, Donald Trump na son ganin jama'a sun koma bakin aiki musamman 'yan kasuwa kafin lokacin sallar Easter.
To sai dai da alama irin makudan kudaden da majalisar dokokin kasar ta ware domin shawo kan annobar na nuna shirin Amurkar na zama cikin ko-ta-kwana.
Majalisar dai ta amince da fitar da tsabar kudi har $2tn a matsayin tallafi.
Yadda coronavirus ta sauya gaisuwar jama'a
Asalin hoton, Jubril Gawat
Bayanan hoto, Tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu na gaisa wa da wasu mukarraban gwamnatin jihar Legas, bayan fitowa daga taron manema labarai kan cutar coronavirus a jihar.
Coronavirus: Mutum 738 sun mutu a rana daya a Spaniya
Asalin hoton, Getty Images
A yanzu haka Spaniya ta zarce China a yawan mutanen da suka mutu sanadiyyar annobar coronavirus.
Gwamnatin kasar ta ce mutum 738 ne suka mutu sakamakon cutar cikin kwana daya - mutum sama da 3400.
A yanzu haka dai Italiya ce kasar da aka fi samun yawan mutanen da suka mutu saboda cutar sai Spaniya da take a matsayi na biyu.
Bayanai kuma na cewa Fiaii Ministar kasar, Carmen Calvo ita ma ta kamu da cutar.
Coronavirus: Shugaban Brazil da gwamnoninsa na takaddama kan fitar jama'a
Asalin hoton, Getty Images
Akasarin gwamnonin Brazil sun yi fatali da bukatar Shugaban kasar, Jair Bolsonaro na sake bude shaguna da makarantu yayin da coronavirus ke ci gaba da bazuwa a sassan kasar.
A daren Talata ne dai Mr Bolsonaro ta kafar talbijin ya bayyana cutar Covid-19 a matsayin wata 'yar mura tare da kira ga jama'ar kasar su koma harkokinsu na yau da kullum sannan su yi watsi da tsarin zama a gida da wasu gwamnoni da magajin gari suka dauka.
Shi ma gwamnan Sao Paulo ya ce abin da shugaban ya fada sam ba dai-dai ba ne cewa matakin gwamnonin na durkusar da tattalin arzikin kasar ne.
Mr Bolsonaro dai na shan suka sannan kuma cikin kwana daya, ya rasa goyon baya daga wasu manyan mukarrabansa.
Shugaba Trump na son bude harkokin kasuwanci duk da coronavirus
Asalin hoton, Getty Images
Amurka ta ce ya zuwa yanzu akwai sama da mutum 60,000 da suka kamu da coronavirus a kasar - rabin mutanen a birnin New York suke.
Gwamnan jihar, Andrew Cuomo, ya ce akwai alamun farko da ke nuna cewa hana tarukan jama'a na iya taimaka wa wajen dakile yaduwar cutar.
Amma ya yi gargadin cewa har yanzu birnin na bukatar karin gadaje a asibiti da karin dubunnan na'urorin taimakawa numfashi.
Ya yi hasashen cewa bukatun gadaje da kuma na'urorin shakar numfashin na iya karuwa cikin kusan mako uku.
A wani taron manema labarai, Shugaba Trump ya sake nanata kudirinsa na son bude harkokin kasuwanci a kasar nan da bukukuwan Easter duk da gargadin da jami'an kiwon lafiya ke yi cewa lokacin ya yi kur-kusa.
Ana ci gaba da gardama kan asalin cutar coronavirus
Asalin hoton, Getty Images
An gaza cimma yarjejeniya game da asalin cutar coronavirus a ganawar ministocin harkokin waje na kungiyar G7.
Fadar White House dai ta dage cewa kamata ya yi sanarwar kungiyar ta kunshi kalmomin kwayar cutar Wuhan - birnin Sin da cutar ta barke.
Sai dai kasashe mambobin kungiyar sun yi watsi da bukatar Amurkar, matakin da suke ganin zai kawo rarrabuwar kai ne.
Tun da farko, sakataren harkokin wajen Amurkan Mike Pompeo ya fada wa taron cewa jami'an diflomasiyya sun san da yunkurin China na haifar da makarkashiya game da asalin kwayar cutar da kuma ikirarin cewa sojojin Amurka ne suka shigar da cutar kasar Sin.
Masu coronavirus a Najeriya sun zama 51 - NCDC
Cibiyar takaita yaduwar cutuka a Najeriya ta tabbatar da samun karin mutum biyar da suka kamu da cutar coronavirus a kasar.
Bayanan da cibiyar ta wallafa a shafinta na Twitter cikin daren Alhamis, na cewa biyu daga cikin mutanen a Babban birnin tarayya Abuja suke, sai biyu a jihar Legas, da kuma wani a jihar Rivers.
Da wadannan alkaluma, Rivers ta zama jiha ta baya-bayan nan da aka samu bullar cutar coronavirus ke nan a Najeriya.
Ta ce mutum uku daga cikinsu matafiya ne da suka dawo gida Najeriya yayin da biyun kuma sun yi hulda ne da masu dauke da cutar.
Zuwa yanzu dai, hukumomin lafiya a Najeriya sun tabbatar da samun mutum 51 wadanda annobar coronavirus ta kama.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Budewa
Jama'a barkan ku da warhaka a shafinmu na bbchausa.com da ke kawo muku bayanai da dumi-dumi kan halin da duniya ke ciki dangane da annobar coronavirus da ma sauran batutuwa a Najeriya da sassan duniya. Muna fatan za ku ci gaba da kasancewa da mu. Allah ya takaita mana wannan annoba.
Rufewa
Masu bibiyarmu a wannan shafin da haka muka kawo karshen kawo muku labarai da rahotanni kai-tsaye. Sai kuma gobe Alhamis idan Allah ya kaimu za mu ci gaba da kawo muku wasu labarai da rahotanni.
Ku duba kasa domin karanta wasu labaran da muka wallafa a wannan shafin.
Bayanan baya-bayan nan daga Turai
Yau ma wata ranar ce mai ban mamaki a Turai sakamakon yadda yawan masu kamuwa da coronavirus ke karuwa da kuma karuwar adadin masu mutuwa sakamakon cutar a kasashe.
Ga wasu abubuwan da ya kamata ku sani:
Yawan mace-mace a Spain ya wuce na China inda kasar ce ta biyu a mutuwar masu coronavirus bayan Italy. Kasar ta samu karuwar masu mutuwa da suka kai 738 cikin sa'o'i 24 inda a halin yanzu mutum 3,434 suka mutu sakamakon cutar. Mataimakin Firai ministan kasar Carmen Calvo na daga cikin wadanda aka samu dauke da cutar ta coronavirus. An kai ta asibiti a ranar Lahadi.
Italiya ta bayyana cewa mutum 683 ne suka mutu sakamakon coronavirus a sa'o'i 24 da suka wuce kuma an samu sabbin mutane 5,210 masu dauke da cutar. Wannan ya nuna cewa an samu raguwa da mutum 60 sakamakon cutar a ranar Talata inda mutum 743 ne suka mutu. Mutanen da suka mutu a kasar sakamakon cutar sun kai 7,503 tun bayan barkewar cutar. Sai dai rahotanni na cewa shugaban hukumar bayar da agaji ta kasar Angelo Borrelli na fama da masassara.
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya daga taron sauyin kundin tsarin mulkin kasar wanda zai ba shi damar ci gaba da mulki sai dai bai bayar da lokacin da za a gudanar da taron ba. Ya bayyana wasu sabbin matakai da za a bi wajen yaki da wannan cuta inda ya shaida wa ko wane ma'aikacin kasar ya zauna a gida sai dai manyan ma'aikata. Sai dai a wani banagaren, jami'ai a Moscow sun bayyana cewa wasu dattijan jami'an gwamnati biyu a kasar sun mutu. Sai dai ba a bayyana cutar da ta kashe su ba. Har yanzu ba a samu rahoton cutar ta yi ajalin wani a kasar ta Rasha ba. Alkaluma na baya-bayan nan sun nuna karuwar cutar a fadin kasar.
Majalisar dokokin Jamus ta amince da wasu makudan kudi da za a yi amfani da su wajen ceto tattalin arzikin kasar. Matakan da za a dauka za su lashe kusan Euro biliyan 750 wadanda suka hada da tallafa wa ma'aikatan gwamnati da tallafa wa masu kananan sana'o'i da sauran marasa karfi. Za a kaddamar da wannan shiri ne ta hanyar ciwo bashi wanda hakan wani abu ne da Jamus din ta dade bata yi ba a shekaru da dama.
Kasar Poland ta kara yawan kwanakin rufe iyakokinta da kusan kwanaki 20 inda ta ce sai 13 ga watan Afrilu take sa ran bude iyakokin.
Za a ci gaba da hada-hadar kayayyaki ta kan iyakokin kasar kamar yadda gwamnatin kasar ta bayyana.
Coronavirus: Bayanan baya-bayan nan daga Gabas ta Tsakiya
Asalin hoton, AFP
Falasdinawa sun ba da sanarwar rasa rai karo na farko saboda cutar
Covid-19. Wata mata ce mai shekara 60 mazauniyar yankin Bidu ta mutu kusa da
Ramallah, a cewar hukumomin falasdinawa. An kuma ba da rahoton cewa mutum 66 sun kamu da cutar a gabar yamma da kogin Jordan da kuma mutum biyu a
Zirin Gaza.
A Isra’ila inda mutum biyar suka mutu,wasu
2,030 suka kamu, gwamnati ta amince da sababbin matakan hana fita domin takaita
yaduwar cutar ta coronavirus. Za a bukaci mutane kada su ringa yin nisan fiye
da mita 100 daga gidajensu, sannan za a kyale mutane su ringa yin ibada ne
kawai a budadden waje, haka kuma za a takaita zirga-zirgar jama’a zuwa kaso
daya cikin hudu na yadda aka saba.
A ranar Laraba kuma an rufe cocin Holy Sepulchre a
tsohon Birnin Kudus - inda kiristoci da dama suka yi amanna cewa a nan
aka gicciye Yesu Kiristi, aka binne shi, sannan ya taso, a matsayin wani mataki
na dakile yaduwar cutar ta coronavirus.
An fara gwada mutane a yankin arewa maso gabashin Syria
da ke hannun ‘yan tawaye, inda Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta kai kayakkin
gwaji 300. Gwamnati ta sanya dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 12 a yankunan da
ke karkashinta, sannan ta rufe duka iyakokinta, kwana daya bayan an tabbatar da
cewa an samu mutumin da ya harbu da cutar a kasar da yaki da daidaita.
Mutuma na biyu ya mutu a Saudi Arabia saboda
kamuwa da cutar, kuma kasar ta tsaurara dokar hana fita da ta fara aiki ranar
Litinin. A yanzu za a ringa hana mutane shiga ko fita daga babban birnin kasar
Riyadh, da biranen Makkah da Madina masu tsarki.
A Masar, mako daya an fara aiki da takaitacciyar dokar hana fita tituna daga
karfe bakwai na yamma zuwa shida na safe. An kara kara wa’adin rufe makarantu
zuwa tsakiyar watan Afrilu. Hukumomin sun ba da rahoton mutum 402 da suka kamu
da cutar ta Covid-19 inda kuma mutum 20 suka mutu
Coronavirus: Bayanan baya-bayan nan daga Afirka
Daga cikin bayanan na baya-bayan nan har da batun tuhumar da ake yi na kisan kai a Afirka Ta Kudu da batun wani mutum da kada ta kashe a lokacin da ya ki bin umarnin hana shiga da fita da aka yi a Rwanda.
Akwai masu dauke da cutar coronavirus a nahiyar Afirka kusan 2,000, amma kasashen da ba su da tsarin lafiya mai inganci suna shirya wa mummunan yanayin da za su iya shiga:
Ana tuhumar wani mutum mai shekara 52 da ke da shagon aski, da laifin kisan kai a Afirka Ta Kudu, sakamakon kin bin umarnin likita na killace kansa a garin Ladysmith, a cewar 'yan sanda. Gwajin da aka yi masa ya nuna yana dauke da cutar, sannan an tsare shi a asibiti
A Afirka Ta Kudun dai mutane sun fara rige-rigen sayen kayayyaki gabanin dokar hana shiga da fita da aka sanya ta mako uku da za ta fara aiki ga 'yan kasar miliyan 50 a ranar Juma'a
A Lagos din Najeriya kuwa, an rufe dukkan shaguna da kasuwanni, sai dai an bar masu sayar da kayan abinci da magunguna kawai. Sannan fitaccen marubuci mai lambar yabo ta Nobel Wole Soyinka ya yi wa malaman addini kaca-kaca kan zuga mabiyansu don kin bin dokar hana taruwa a waje daya da yawa
A Rwanda kuwa kada ce ta cinye wani mutum ne da ya je kogi don kamo kifi, bayan da ya ki bin umarnin zama a gida da gwamnati ta sanya doka a kai, kamar yadda jami'ai a yankin suka shaida wa BBC
Kasashen Libya da Mali da ake yawon tashin hankali sun samu masu dauke da cutar a karon farko
Jean-Joseph Mukendi wa Mulumba, wani babban lauyan kare hakkin dan adam a Jamhuriyyar Dimokradiyyar Kongo kuma matimaki na musamman ga shugaban kasar da Rwanda ya muut sakamakon cutar Covid-19
A Zimbabwe kuwa, likitoci ne suka ki yin aiki suka ce har sai an ba su rigunan kariya da za su sa lokacin da suke duba masu cutar coronavirus saboda gudun kamuwa
Kasar Habasha ta saki fursunoni fiye da 4,000 don hana yaduwar cutar a gidajen yari
An dakatar da rage ma'aikatan BBC 450 saboda Covid-19
Sashen BBC News ya dakatar da shirinsa na korar ma'aikata 450 a yayin da yake matukar bukatar 'yan jaridar da za su rika bayar da labarai da rsahotanni kan annobar coronavirus.
A watan Janairu ne aka sanar da cewa za a kori ma'aikatan a wani shiri na tattalin kudin da suka kai £80m ya zuwa shekarar 2022.
Shirye-shiryen da za a rufe sun hada da BBC Two's Newsnight, BBC Radio 5 Live da kuma shirin World Update programme.
Darakta Janar na BBC Tony Hall ya shaida wa ma'aikata ranar Laraba cewa an dakatar da korar ma'aikatan.
Lord Hall ya ce "mun dakatar da shirinmu na rage ma'aikata da muka yi shirin yi don tattali kudi. Muna so mu ci gaa da aikin da muke yi cikin kwarewa da hikima."
Covid-19: An samu raguwar mutuwa a Italy
Italiya ta bayyana cewa mutum 683 ne suka mutu sakamakon coronavirus a sa'o'i 24 da suka wuce kuma an samu sabbin mutane 5,210 masu dauke da cutar.
Wannan ya nuna cewa an samu raguwa da mutum 60 sakamakon a ranar Talata inda mutum 743 ne suka mutu.
Mutanen da suka mutu a kasar sakamakon cutar sun kai 7,503 tun bayan barkewar cutar.
Sai dai rahotanni na cewa shugaban hukumar bayar da agaji ta kasar Angelo Borrelli na fama da masassara.
Covid-19 a dakika 60
Bayanan bidiyo, Bayanai kan coronavirus tare da Abdulbaqi Jari