Abubuwan da suka faru a Nigeria da sassan duniya kan coronavirus
Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma wasu sassan duniya, musamman rahotanni kan annobar coronavirus.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail
Hotuna: Yadda coronavirus ta sauya rayuwa a Birtaniya
Hotunan yadda annobar coronavirus ta sauya rayuwa a Birtaniya. A cikin wadannan hotunan, kusan kowanne wuri a kasar ya zama fayau babu kowa.
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
Coronavirus: An bai wa sojoji umarnin tabbatar da doka a Tunisia
Shugaban Tunisia ya bai wa dakarun sojojin kasar umarnin bi tituna-tituna domin tabatar da cewa mutane sun yi biyayya ga dokar hana fita saboda kauce wa yaduwar coronavirus.
Shugaba Kais Saied ya ce za a bar mutane su fita daga gidajensu ne kawai idan za su sayi abubuwan bukata ta musamman.
Su ma hukumomin Jordan da Lebanon sun umarci sojoji su tabbatar 'yan kasashensu sun zauna a gidajensu.
COVID 19: Gwamnatin Borno ta hana kai ziyara sansanin 'yan gudun hijira
Gwamnatin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ta haramta kai ziyara sansanin 'yan gudun hijira tsawon mako hudu.
Sanarwar da Isa
Gusau, mai magana da yawun gwamnan jihar, ya aike wa manema labarai ranar Litinin ta ambato shugabar hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar, Hajiya Yabawa Kolo, tana cewa an dauki matakin saboda fargabar yaduwar coronavirus.
Ya zuwa yanzu dai, cutar ta kama mutum 35 a Najeriya ko da yake babu wanda ya kamu da ita a jihar Borno.
Sanarwar ta kara da cewa an dauki matakin ne bayan Hajiya Yabawa ta gana da shugabannin sansanonin 'yan gudun hijirar 51 a Maiduguri ranar Litinin.
A cewart, daukar matakin ya zama wajibi ganin cewa kasashen da ke makwabtaka da Najeriya ta kan iyaka da jihar Borno, irin su Chadi da Kamaru sun kamu da cutar.
Asalin hoton, Twitter/@PROFZULUM
Bayanan hoto, Gwamna Babagana Zulum ya ce ba za a bar kowa ya shiga sansanin 'yan gudun hijira ba
Coronavirus: Ta yaya mutum zai san yana da cutar?
Kalli wannan bidiyon mai dauke da bayanai kan yadda mutum zai san ko yana tare da wasu alamomi masu nuna cewa ko yana dauke da coronavirus.
Bayanan bidiyo, Ta yaya mutum zai san yana da coronavirus?
Labarai da dumi-dumi, Bazuwar coronavirus na ci gaba da gigita duniya - WHO
Shugaban Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO ya ce annobar coronavirus na ci gaba da yaduwa.
Da yake magana a taron manema labarai a Geneva, shugaban WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce: “An shafe kwana 67 daga ranar da aka smau mutum na farko da ya kamu da cutar zuwa samun mutum 100,000 masu dauke da ita, kwana 11 daga mutum 100,000 zuwa karin wasu 100,000, sannan aka samu kwana hudu tsakanin wannan adadin zuwa katrin wasu 100,000 din.''
Ya cezai yi wa shugabannin kasashe 20 masu karfin tattalin arziki na duniya G20 jawabi a farkon wannan makon don neman hadin kansu wajen yin aiki tare wajen shawo kan matsalar.
An dakatar da sallah a babban masallacin Najeriya
Hukumar kula da babban masallacin Abuja da ke Najeriya ta ce za a dakaar da yin dukkan salloli a masallacin saboda fargabar yaduwar cutar coronavirus.
Wata sanarwa da hukumar masallacin ta fitar ranar Litinin, ta ce an dakatar da yi sallolin hamsas salawati da na Juma'a da taruwar jama'a da dukkan wasu ayyuka da za su sa jama'a su taru.
Kazalika, hukumar ta ce za a rufe kasuwannin da ke ci a gefen masallacin.
A cewarta, za a dakatar da dukkan wadannan abubuwa ne daga ranar Litinin 23 ga watan Maris.
Ta yi addu'ar Allah Ya kawo sauki ga wannan annoba.
Asalin hoton, Abuja National Mosque
Coronavirus: Yadda matasa suka yi ganganci da rayuwarsu
Gungun matasa a Amurka sun je wata liyafa a jihar Florida duk da shawarwarin da hukumomi suka bayar na takaita taruwar mutane da yawa don hana yaduwar cutar a kasar.
Hukumomin lafiya na shawartar mutane da kada su yi taron mutum sama da 10 a lokaci daya domin hana yaduwar cutar a cikin al'umma.
Shugaba Trump ya yi kira ga matasa da su sauya tsarin rayuwarsu domin kada su dauki cutar su yadawa 'kakanninsu da iyayensu'.
Bayanan bidiyo, Matasan Amurka na zuwa fati duk da coronavirus
Coronavirus: An rufe Masallacin Kudus
An rufe kofofin shiga harabar Masallacin Kudus da Hubbar Masallacin Kudus.
Wuri ne mai tsarki a birnin Kudus da Musulmi ke kira Haram al-Sharif yayin da Yahudawa ke kiransa Temple Mount.
Masu ibada sun kasa shiga masallacin tsawon kwanaki, kuma ana iya sallah ne a waje a wani mataki na bayar da tazara don yaki da coronavirus.
Amma ranar Lahadi, hukumomi sun ce za su dakatar da aikin ibada a duka sassa na harabar.
Kafofin yada labaran Isra'ila sun ruwaito cewa za a hana Yahudawa shiga wurin.
Wannan wuri shi ne musabbabin rikicin a Kudus.
A yadda aka saba, duk wani sauyi da aka kawo a masallacin na iya jawo tashin hankali amma an ga karuwar maraba da mutane ke yi ga sauye-sauye da matakan kariya saboda coronavirus.
An samu karin mutum 51 masu dauke da coronavirus a Saudiyya
Asalin hoton, Getty Images
Saudiyya ta sanar da karuwar mutum 51 masu dauke da cutar coronavirus a kasar ranar Litinin.
Kawo yanzu, yawan mutanen da ke dauke da cutar a kasar ya kai 562.
Hukumomi sun bukaci mazauna kasar su zauna a gida tsaknain karfe bakwai na dare zuwa shidda na safe, kuma kada su fita har sai in fitar ta zama dole.
Ma'aikatar harkokin cikin gida ta sanar da cewa duk wanda ya karya dokar hana fitar ta tsawon kwanaki 21 zai fuskanci hukuncin biyan tara Riyal 10,000, kwatankwacin Dala 2, 663.
Gwamnatin jihar Neja ta sa dokar fita
Gwamnatin jihar Neja ta sanar da sanya dokar hana fita daga karfe takwas na safe zuwa takwas na safe.
Gwamna Sani Bello ya ce dokar za ta fara ne daga ranar Laraba mai zuwa.
Sani Bello ya kuma ce gwamnatin ta haramta duk wani taron jama'a da ya wuce mutum 12 sannan kuma an hana masu bara da tallace-tallace a kan titunan.
Coronavirus gaskiya ce- Pantami
Ministan sadarwa na Najeriya, Dakta Isa Ali Pantami ya ce "zan
iya bayar da raina fansa domin kawo karshen annobar coronavirus."
Dakta Pantami ya bayyana hakan ne a wani bidiyo da yake yawo a
kafafen sada zumunta, inda yake kokarin nusar da almajiransa da ke halartar
zaman karatun da yake yi a masallacin Annur Mosque da ke unguwar Wuse a Abuja.
Sheikh Isa Pantami ya shaida wa almajiransa cewa annobar
coronavirus gaskiya ce kuma ya kamata jama'a su bi dokokin gwamnati da jami'an lafiya.
Coronavirus ta mayar da titunan London tamkar kufai
A yayin da annobar coronavirus ke ci gaba da yi wa duniya fyadar 'ya'yan kadanya, tituna da gine-gine a birnin London sun kasance tamkar kufai.
Jama'a dai na ci gaba da zama a gidajensu domin gudun kamuwa ko kuma yada cutar.
Kafin annobar dai titunan sun kasance masu yawan hada-hadar jama'a.
Gwamnatin Kano ta hana taron jama'a
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da dage duk wani taron jama'a a jihar, a wani matakin kare al'ummar jihar daga annobar coronavirus.
Gwamna Ganduje ya tabbatar da hakan ne yayin wani taron manema labarai a ranar Litinin.
Asalin hoton, KNSG
Coronavirus: Mutum na farko ya mutu a Zimbabwe
Wani mai shekaru 30 ya zama mutum na farko da ya kamu da cutar coronavirus a Zimbabwe, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta bayyana a wani sako da ta wallafa a Twitter.
A ranar Asabar ne aka tabbatar wa dan jarida Zororo Makamba yana dauke da cutar.
Ya kai ziyara Amurka a karshen watan da ya gabata kuma ya koma kasar bayan ya shiga Afirka ta Kudu na dan wani lokaci, in ji kamfanin dillancin labarai na AFP.
Coronavirus: An hana hawa motocin haya a Maroko
Asalin hoton, Getty Images
An hana hawa abubuwan haya a Maroko don hana yaduwar coronavirus.
Gwamnati ta dauki wadannan kwararan matakan ne don yaki da annobar, yayin da yawan muaten da suka kamu da cutar ya kai 108 a kasar.
Hukumomi sun yanke shawarar hana zirga-zirga tsakanin mutane tsakanin motocin haya da na kashin kai.
Wannan ya hada da jiragen kasa da jiragen sama da jiragen ruwa.
Gwamnan jihar Bauchi ya killace kansa
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ya killace kansa tun bayan hada jirgi da ya yi da dan gidan tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar wanda ya kamu da cutar coronavirus.
Mai magana da yawunsa, Ladan Salihu ne ya bayyana haka a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Ladan ya ce "mun hau jirgi daya da dan gidan na Atiku daga Lagos zuwa Abuja, inda suka yi musabiha hannu da hannu. Tuni aka yi wa gwamna da mu 'yan tawagarsa gwaji. Muna fatan sakamakon gwajin zai yi kyau."
Wata majiyar gwamnati ta ce an dauki samfirin majinar gwamnan da na wasu 'yan tawagarsa zuwa birnin Abuja domin yin gwaji.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Coronavirus: Aisha Buhari na son iyaye su 'zauna a gida'
Asalin hoton, Twitter
Uwar gidan shugaban Najeriya, Aisha Muhammadu Buhari ta ce ya kamata iyayen yara su zauna a gida kamar yadda 'ya'yansu ke gidan bayan rufe makarantu.
Aisha wadda ta wallafa wannan kira a shafinta na Twitter ta ce, "abun a yaba ne yadda aka rufe makarantu aka kuma umarci yara su zauna a gida domin gudun ka da su kamau da cutar coronavirus."
Ta kara da cewa " ba ta ga hikimar hana yara zuwa makaranta ba yayin da mahaifansu ke fita waje saboda za su iya dauko musu cutar."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Coronavirus: Tattalin arzikin duniya zai shiga garari na tsawon shekaru
Kungiyar habaka tattalin arziki da ci gaba ta kasashen duniya OECD ta yi gargadi cewa za a dauki tsawon shekaru kafin a farfado daga annobar coronavirus.
Sakatare janar na kungiyar Angel Gurría, ya ce tabarbarewar da tattalin arzikin ke ciki ya zarce na wanda ake tunanin shiga.
Ya shaida wa BBC cewa ''tsammanin warabbuka'' ne kawai zai sa a yi amannar cewa kasashe za su farfado nan kusa daga halin da aka fada.
OECD ta yi kira ga gwamnatoci su tanadi wasu dokoki na kashe kudi don tabbatar da cewa an magance wannan cuta.
Asalin hoton, Getty Images
Coronavirus: 'Yan majalisar Australiya na bai wa juna tazara
Gwamnatoci a fadin duniya na bai wa mutanen shawarar bai wa juna tazara don rage yaduwar coronavirus.
Wannan shawarar ta shafi kowa, har da 'yan majalisa kamar yadda hoton da ke kasa ya nuna a majalisar dokokin Australiya a Canberra, babban birnin kasar.
An takaita yawan mutanen da za su zauna a zauren majalisar kuma su rika bai wa juna tazara.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Minista Scott Morrison a tsakiya ya bai wa sauran 'yan majalisa tazara
Mutanen da Coronavirus ta kama da jihohinsu
Hukumar da ke hana yaduwar cututtuka ta Najeriya, NCDC ta fito da jerin alkaluman mutanen da annobar Coronavirus ta kama a jihohin kasar.
Bisa alkaluman hukumar, ya zuwa yanzu za a iya cewa idan ban da birnin Abuja, dukkannin mutanen da cutar ta kama sun fito daga kudancin kasar ne.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.