Abubuwan da suka faru a Nigeria da sassan duniya kan coronavirus

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma wasu sassan duniya, musamman rahotanni kan annobar coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Abubuwan da ya kamata ku sani kan coronavirus

    Coronavirus
    Coronavirus
    Coronavirus
    Coronavirus
  2. Coronavirus: An rufe gari na biyu mafi girma a DRC

    An rufe gari na biyu mafi girma a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, Lumumbashi, bayan da mutum biyu suka kamu da cutar.

    Gwamnan jihar ya ce mutanne biyu 'yan asalin kasar sun isa Lumumbashi ne a jirgin sama daga Kinshasa, babban birnin kasar ranar Lahadi da rana.

    Ya kara da cewa mutane da 77 ne suke cikin jirgin.

    Daga baya, Mista Kyabula ya sanar da cewa za a dakatar da ayyuka da zirga-zirga gaba daya a lardin Haut-Katanga tsawon kwanaki biyu.

    Ya kuma haramta zirag-zirga duka motoci.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  3. Labarai da dumi-dumi, Coronavirus: Mutum daya ya mutu a Najeriya

    Hukumar da ke hana yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC ta ce mutum daya daga cikin mutum 35 da suka kamu da cutar Coronavirus ya mutu.

    A shafinta na Twitter, hukumar ta ce mutumin mai shekara 67 ya koma Najeriya daga kasar Burtaniya.

    NCDC ta kara da cewa da ma marigayin yana fama da cutar suga da daji inda ake yi masa gashi a asibiti.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  4. Coronavirus: Aisha Buhari ta yi wa Atiku jaje

    Uwar gidan shugaban Najeriya, Aisha Buhari ta jajanta wa tsohon mataimakin shugaban kasar, Atiku Abubakar dangane da dansa da cutar coronavirus ta kama.

    Aisha Buhari a shafinta na Twitter ta yi addu'ar Allah ya bai wa dan nasa sauki.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  5. Mutum 16 sun kamu da coronavirus a Kamaru

    Sakamakon binciken da aka gudanar akan wasu mutane 26 da ake kiyautata zaton cewa suna dauke da cutar corona, an tabbatar da 16 daga cikin na dauke da cutar.

    Hakan ya kaiga a yanzu mutane 56 ne suka kamu da cutar tun daga ranar 6 ga watan maris, ranar da aka gano mutum na farko (wani bafaranshe) da ya kamu da cutar.

    A yanzu dai wannan cutar ta bazu ne a manyan birane 3 na Kamaru da suka hada da Yaoundé cibiyar gwamnati, da Douala cibiyar harkokin kasuwanci da Bafoussam babban birni na uku a kasar.

    Duk da cewa kusan mako guda kenan da Hukumomi suka dauki wasu matakai na yunkurin dakile bazuwar cutar Corona, amma kuma bisa ga dukkan alamu adadin mutanen da suka kamu da cutar na ta yawaita kusan a ko wace rana.

    Coronavirus

    Asalin hoton, Getty Images

  6. An samu karin mutum biyar masu Coronvirus a Najeriya

    Hukumar da ke hana yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC ta ce ya zuwa yanzu mutum 35 ne suka kamu da annobar Coronavirus.

    Hukumar ta ce Karin mutanen da aka samu guda biyar sun hada da biyu a birnin Abuja da biyu a Legas da kuma mutum daya a jihar Edo.

    Hukumar ta NCDC ta kara da cewa mutum 33 sun kamu da cutar sosai, inda aka sallami mutum biyu bayan sun warke.

    coronavirus

    Asalin hoton, NCDC

  7. Farawa

    Masu bibiyarmu barkan ku da warhaka. Da fatan za ku ci gaba da kasance wa shafinmu na bbchausa.com domin samun bayanai da dumi-dumi kan cutar coronavirus da ma sauran batutuwa a Najeriya da sassan duniya. Mun gode

  8. Mu kwana lafiya

    Karshen rahotannin ke nan daga Umar Mikail.

    Mu zama lafiya.

  9. Yadda za ku tuntubi hukumomi a Najeriya kan coronavirus

    Coronavirus

    Asalin hoton, NCDC

    A kokarinta na ci gaba da yaki da Covid-19, hukumar NCDC a Najeriya ta ce daga gobe Litinin 23 ga Maris za ta fara amfani da dandalin Whasapp domin bai 'yan Najeriya damar tuntubarta.

    Lambar da za a same su ita ce 07087110839. Sai kuma lambar da za a iya kira kyauta 08099555577 da kuma adireshin imel a kan info@ncdc,go.ng.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  10. Coronavirus: Wadanda suka mutu a Faransa sun kai 674

    Mutum 674 sun mutu a Faransa sakamakon cutar coronavirus bayan an bayar da rahoton 112 da aka tabbatar da mutuwarsu cikin awa 24 da ta gabata.

    "Cutar ta kashe sannan tana ci gaba da kisa," in ji Jerome Salomon, wani jami'in hukumar lafiya a ranar Lahadi.

    Jumullar mutum 16,018 ne suka kamu da cutar a kasar ta Faransa, sai dai Mista Salomon ya ce wasu na ganin adadin mutanen ya fi haka.

    Gwamnati ta hana zirga-zirga tun daga ranar Talata sai dai fa mai matukar muhummanci. Mista Salomon ya shawarci mutane da su "kara hakuri".

  11. Likitoci sun janye yajin aiki a Najeriya saboda coronavirus

    Likitoci

    Asalin hoton, Getty Images

    Likitoci a Najeriya sun jingine yajin aikin da suka shiga sakamakon rashin biyansu albashi na tsawon watanni.

    A wata sanarwa da kungiyar likitocin mai suna Nigeria Association of Resident Doctors ta fitar ranar Lahadi, likitocin sun ce sun janye yajin aikin ne "saboda tausayin al'umma".

    Sanarwar ta ce "ganin irin halin da ake ciki na yaduwar cutar coronavirus da kuma kokarin da gwamnati take yi a bangaren lafiya," za su jingine boren da suke yi.

  12. 'Babu coronavirus a Jami'ar Bayero ta Kano'

    Jami'ar Bayero ta Kano

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar Jami'ar Bayero ta Kano ta ce ba gaskiya ba ne labarin da aka rika yadawa cewa an samu bullar cutar Covid-19 (coronavirus) a jami'ar.

    Da tsakar ranar yau Lahadi ne dai aka fara yada wani labari da ke cewa Ma'aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta tabbatar da wasu dalibai biyu sun kamu da Covid-19 a Jami'ar Bayero.

    Wani shafin intanet ne da ke dauke da sunan sashen Ingilishi na BBC ya wallafa labarin, wanda aka rika yadawa a shafukan sada zumunta.

    A cikin wata hira da ya yi da Sashen Hausa na BBC, Shugaban Jami'ar, Farfesa Muhammad Yahuza ya ce labarin na kanzon kurege ne sannan ya ce babu ma dalibai a dakunan kwanan jami'ar.

    "Wannan labari ba shi da tushe ballanta makama," in ji Farfesa Yahuza.

    Ya ci gaba da cewa: "An dauki hoton boge ne na shafi mai sunan BBC ana yadawa domin a nuna kamar daga BBC yake.

    "A halin yanzu ma babu dalibai a dakin kwana na Jami'ar Bayero. Kamar yadda aka sani an yi yajin aiki na sati biyu. Kafin haka kuma dalibanmu suna hutun tsakiyar zango. Mun bayar da hutun mako daya sai kuma aka tafi yajin aikin."

    Farfesa Yahuza ya kuma yi Allah-wadai da wadanda suka kirkiri labarin karyar sannan ya yi kira ga masu yadawa da su guji yin hakan.

    Zuwa lokacin wallafa wannan labarin, hukumomi a Najeriya ba su bayyana batun bullar cutar coronavirus ba a arewacin kasar ban da mutum hudu a Abuja.

  13. Labarai da dumi-dumi, Coronavirus: An rufe makarantun Islamiyya da na Allo a Kano

    Gwamnatin jihar Kano ta bayar da umarnin rufe makarantun Islamiyya a jihar.

    Shugaban makarantun Islamiyya da tsangayu na Jihar Kano Gwani Yahuza Dan Zarga ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi, inda ya ce an dauki matakin ne domin kauce wa yaduwar cutar coronavirus.

    "Kwamishinan ilimi ya yi taron manema labarai ya fada sannan kuma ya kara yi mani gargadi cewa na fada wa masu makarantu da su bi wannan doka ta gwamnati," in ji Gwani Yahuza.

    "An dauki matakin ne domin kare lafiyarsu sannan kuma matakin ya shafi dukkanin makarantun Islamiyya da na tsangaya (makarantun allo)."

    Gwani ya ce daga gobe Litinin ne matakin zai fara aiki, sannan kuma ya yi kira ga malamai da masu makarantun da su dukufa da addu'o'i da niyyar Allah ya kawo karshen cutar ta Covid-19.

  14. Labarai da dumi-dumi, Coronavirus: Karin mutum uku sun kamu a Legas

    Hukumar NCDC ta tabbatar da sake samun wasu mutum uku da suka kamu da coronavirus a Jihar Legas ta Najeriya.

    Mutum biyu daga cikinsu sun dawo ne daga kasar waje, yayin da daya kuma ya harbu daga maras lafiyar da ya yi mu'amala da shi.

    Jumullar wadanda suka kamu da cutar a Najeriya sun zama 30 ke nan bayan an tabbatar da mutum takwas da suka kamu a yau Lahadi 22 ga watan Maris.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  15. Yadda za ku kare wayoyinku daga coronavirus

    Musamman a wannan karni, hannaye sun fi taba wayar hannu sama da kusan komai a rayuwarmu.

    To sai kuma ga shi coronavirus na kawo wa rayuwarmu barazana.

    Ku dai kalli yadda ya kamata ku rika yi wa wayoyinku a wannan yanayi.

    Bayanan bidiyo, Yadda za ku kare wayoyinku daga Coronavirus
  16. Ba zaman gidan ba kawai...

    Tsohon bidiyo ne amma amfaninsa ya isa

    Dan wasan bayan Arseanl Shkodran Mustafi ke nan yake nuna koya wa yaransa abin da ya kamata a don kare kai daga coronavirus - a zauna a gida, a rika wanke hannu - shi ke nan.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  17. Labarai da dumi-dumi, Coronavirus: An bai wa ma'aikata hutu a Jihar Legas

    Daga gobe Litinin 23 ga watan Maris, ma'aikata a jihar Legas za su fara zaman gida har na tsawon kwana 14.

    Gwamnatin jihar ce ta sanar da hakan a shafinta na Twitter, inda ta ce ma'aikata tun daga matsayi na daya har zuwa 12 ne hutun ya shafa.

    Mutum 19 daga cikin 27 da suka kamu da cutar a Najeriya a Jihar Legas suke.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  18. Coronavirus: Birnin Delhi na India ya zama kufai

    Delhi

    Asalin hoton, Getty Images

    An hana shiga da fita a babban birnin Indiya, Delhi har zuwa 31 ga watan Maris.

    Sanarwar ta zo ne a 'yan awanni bayan kasar baki dayanta ta fuskanci dokar hana fita ta awa 14 ta kashin-kai, kamar yadda Firai Minista Narendra Modi ya bukata.

    Matakan sun hada da dakatar da tashi da saukar jiragen cikin gida da na waje zuwa Delhi, hana zirga-zirgar motocin haya da kuma rufe dukkanin ma'aikatu da ofisoshi da wuraren ibada.

    Kazalika an garkame iyakokin birnin da makobtansa.

  19. Coronavirus: An nade shimfidun Masallatan Harami

    Masallacin Harami

    Asalin hoton, Haramain Sharifain

    Shugaba mai kula da masallatan Harami na Makka da na Madina, Sheikh Sudais ya bayar da umarnin a nade kafet din masallatan.

    Hukumomi ba su bayyana dalilin nade shimfidar ba amma hakan ba zai rasa nasaba da coronavirus ba.

    Shafin masallatan na kafar sada zumunta ya wallafa hotunan ma'aikata na nade shimfidun cikin masallatan guda biyu.

  20. Coronavirus: Mutum shida sun sake kamuwa a Falasdinu

    Kasar Falasdinu ta bayar da rahoton cewa mutum shida sun sake kamuwa da coronavirus, abin da ya sa suka zama 59 jumulla a kasar.

    A wani taron manema labarai da ya gudanar wanda kuma kamfanin dillancin labarai na SPA ya ruwaito, mai magana da yawun gwamnatin Falasdinu, Ibrahim Melhem ya ce: "A yau (Lahadi) adadin wadanda suka kamu ya kai mutum 59 sannan 17 sun warke."