Coronavirus: 'Duk wanda ya ziyarci New York to ya killace kansa'

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Amurka ta ce duk wani wanda ya san ya fita daga birnin New York a cikin 'yan kwanakin da suka gabata to ya kebe kansa na mako biyu.
Birnin shi ne yankin da wannan annoba tafi yaduwa a Amurka da kashi 2 cikin 3 na sabbin alkaluman masu dauke da cutar da aka tabbatar a kasar.
Akwai fargabar mutanen da ke ziyartar sauran yankunan kasar su sake yada anobar.
A wani taron manema labarai a fadar White House, Jami'an lafiya sun yi gargadin cewa babu mamaki mutanen da suka bar yankin a cikin 'yan kwanaki da suka gabata sun harbu da cutar.
Gwamnan jihar, Andrew Cuomo, ya kwatanta yadda cutar ke bazuwa da 'jirgin kasa mai bala'in gudu', da yanzu hakan jiharsa tafi fuskantar barazana













