Watakila mu hana balaguro tsakanin jihohin Nigeria– Lai Mohammed

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Najeriya ta ce akwai yiwuwar ta hana zirga-zirga tsakanin jihohin kasar a ci gaba da yaki da yaduwar coronavirus a kasar, wadda mutum 51 suka kamu da cutar.
Ministan Yada Labarai da Al'adu, Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudanar a Abuja ranar Alhamis, inda ya ce sun dauki tsauraran matakan ne doimin tabbatar cewa gwamnati ba ta gaza ba wurin kare rayukan al'umma.
"'Yan kasa maza da mata, daga cikin tsauraran matakan da muka dauka akwai hana zirga-zirga tsakanin jihohin kasa, rufe duk tashoshin mota, dakatar da sufurin jirgin kasa, yin amfani da kayayyakin kashe gobara da sauran ababen hawa domin yin feshin magani a birane da kaunyuka," ministan ya fada.
Ya kara da cewa dama tuni aka dakatar da zirga-zirgar jirgin kasan fasinja a kasa baki daya.
"Za mu ci gaba da bayar da bayanai kan sabbin matakan da muke dauka, amma ku sani duk matakin da muka dauka na kare muradun kasa ne da 'yan kasa baki daya," in ji Lai Mohammed.
Har wa yau, ministan ya ce zuwa yanzu akwai wuraren killace jama'a uku a Abuja - mai gado 40 da mai gado 60 da mai gado 160 - sannan kuma suna ci gaba da neman wasu wuraren domin killace wadanda aka samu da cutar a birnin.
Kazalika, ya ce akwai mutum 4,370 da mahukunta ke bin sawu domin sanin tabbacin ko sun kamu da cutar ko kuma a'a, sannan ya nemi wadanda suka san sun yi mu'amala da masu dauke da ita da su kai kansu ga hukumomi domin yin gwaji.











