Abubuwan da suka faru a Nigeria da sassan duniya kan coronavirus
Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma wasu sassan duniya, musamman rahotanni kan annobar coronavirus.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail
Labarai da dumi-dumi, Coronavirsu: Mutum uku sun sake mutuwa a Scotland
Mutum uku sun sake mutuwa a yankin Scotland na Birtaniya bayan gwaji ya tabbatar suna dauke da coronavirus.
Yanzu mutum 10 ne jumulla suka mutu a cewar rahoton gwamnatin Scotland.
Nan gaba kadan Ministar Scotland za ta yi taron manema labarai.
Covid-19: An samu sabbin mutum 119 da suka kamu a Saudiyya
Asalin hoton, Getty Images
Kasar Saudiyya a ranar Lahadi ta tabbatar da sake samun sabbin masu dauke da coronavirus har 119 inda jimlar masu dauke da cutar ya kai 511, kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito.
Cikin mutum 119, 72 daga cikinsu na cikin garin Makkah, 34 na a birnin Riyadh, hudu na a Dammam. hudu na Al-Qatif sai kuma uku na Al-Ahsa kamar yadda mai magana da yawun ministan lafiyar kasar ya bayyana.
Akwai kuma wasu da aka samu a Khobar da Dhahran da kuma Qassim kamar yadda ya bayyana.
COVID-19: An mayar da dakin taro asibiti a Madrid
Asalin hoton, Getty Images
An kafa asibitin wucin gadi da zai dauki gadaje 5,500 a Madrid babban birnin Spain domin shawo kan coronavirus.
Wannan asibiti shi ne mafi girma a Turai a halin yanzu kuma an kafa shi a wani babban dakin taro a Madrid.
Garin Madrid na cikin garuruwan da ke dauke da masu coronavirus da suka fi yawa a fadin duniya.
Daraktan da ke kula da aikin Antonio Zapatero ya shaida wa jaridar El Mundo cewa ana shirin kai mutum 300 asibitin a halin yanzu.
Kasar Spaniya na da kusan mutum 28,572 da ke dauke da cutar a halin yanzu, wanda hakan ya sa ta zama daya daga cikin kasashen da annobar ta fi tasiri.
Sama da mutum 1,700 ne suka mutu sakamakon wannan cuta a kasar
Covid-19: Iran ta yi watsi da tallafin Amurka
Asalin hoton, Anadolu Agency
Shugaban addini a Iran Ayatollah Khamenei ya yi watsi da bukatar Amurka na tallafa wa kasarsa wajen yaki da coronavirus.
A wani jawabi da ya yi a talabijin, Ayatollah Khamenei ya bayyana cewa Amurka abokiyar gaba ce ga Iran kuma ya yi tsokaci kan wani batu da babu tabbas da ke cewa Amurka ce ta kirkiro annobar Covid-19.
Ya bayyana cewa duk da ba shi da tabbacin Amurka ce ta kirkiro annobar, amma babu wanda zai amince da Amurka ta kawo masa tallafin magani.
Ya ce ''akwai yiwuwar maganin da Amurka za ta bayar kan iya kara baza cutar''.
Wasu daga cikin jami'an gwamnatin ta Iran sun zargi Amurkar da 'munafunci' inda suka ce Amurkar ta ki cire takunkuman da ta saka wa kasar amma kuma ta wani gefe tana neman ta taimaka mata wajen yaki da coronavirus.
Mutum 12 na dauke da Coronavirus a Tanzania
A halin yanzu, mutum 12 ne ke dauke da cutar coronavirus a Tanzania kamar yadda shugaban kasar John Magafuli ya bayyana.
Ya shaida cewa takwas daga ciki 'yan asalin Tanzania ne, hudu kuma baki ne da suka shigo kasar.
Ya shaida cewa marasa lafiyar na samun sauki kuma ana kula da su.
Shugaba Magafuli ya yi wannan bayani ne a wani jawabi da ya yi wa kasar inda kuma ya bayyana matakan da ya kamata a dauka wajen kare kai daga yaduwar cutar.
Ya bayyana cewa daga ranar Litinin, duk wani bako ko kuma wani dan kasar ta Tanzania da zai shiga kasar sai an killace shi na kwanaki 14 an tabbatar bai dauke da cutar.
Ya kuma ce mutum ne zai dauki nauyin wurin da za a killace shi da abincin da zai ci.
Covid-19: Kayayyakin da Jack Ma ya yi alkawari sun soma isowa Afrika
Taragon farko na
miliyoyin kayayyakin gwaji da na kariya daga cutar Coronavirus wadanda attajirin nan dan kasar China, Jack Ma ya yi alkawarin bai wa kasashen Afirka - sun iso kasar
Habasha.
Ana sa ran za a yi amfani da kayayyakin wajen yaki da
cutar coronavirus a kasashe Afrika 54.
Kayayyakin sun iso Habasha ne daga
birnin Guangzho na China.
Mista Ma wanda shi ne ya kafa kamfanin Ali Baba, ya yi
alkawarin bai wa kowacce kasa a Afrika rigar kariya guda dubu daya, da injinan
gwaji guda dubu 20 da kuma abin kare fuska guda dubu 100,000 a matsayin
gudunmuwarsa wajen yaki da Covid-19.
A yanzu haka a nahiyar Afirka akwai mutane fiye da
1,000 dauke da cutar a kasashe 43.
Tuni Mista Ma ya bada gudunmuwa irin haka ga Amurka da
wasu kasashen Turai da na Asiya domin kawo karshen yaduwar cutar Coronavirus.
Asalin hoton, @AfricaCDC
Sama da mutum 300,000 na dauke da cutar Covid-19 a duniya
Asalin hoton, Getty Images
A karshen makon nan, rahotanni sun tabbatar da cewa sama da mutum 300,000 sun kamu da coronavirus a fadin duniya, a nahiyar Afrika kuma sama da mutum dubu daya.
Kasar Italiya ce kan gaba a yawan masu dauke da wannan annoba a fadin duniya da mutum sama da dubu 50.
Sama da mutum 4,800 ne suka mutu sakamakon wannan cuta a kasar ta Italiya.
Hukumar da ke kula da yaduwar cututtuka a nahiyar Afirka ta bayyana cewa mutum 108 sun warke daga cutar.
Sai dai ana ta samun bullar annobar daya bayan daya a kasashen na Afirka inda yawan masu dauke da cutar ke karuwa.
Coci-coci sun bijire wa umarnin gwamnati a Korea ta Kudu
Asalin hoton, Getty Images
Coci-coci da dama a Korea ta Kudu sun bijire wa umarnin gwamnatin kasar na soke duk wasu taruka na addu'o'i da aka saba yi ranar Lahadi a kasar.
Gwamnatin kasar ta yi hakane domin shawo kan annobar coronavirus wadda ta bulla a kasashe da dama na duniya.
Kamfanin dillancin labarai na Yonhap ya ruwaito cewa daruruwan coci-coci a kasar sun gudanar da taron addu'o'i, sai dai wasu malaman addini sun bukaci mabiya da su bayar da tazarar mita daya a tsakanin juna da kuma saka abin rufe fuska domin kare kai.
Hukumomi a Korea ta Kudu sun sha nanata cewa za su saka matakai masu tsaurin gaske idan mutanen kasar suka ci gaba da yin watsi da umarnin gwamnatin kasar na kauracewa yin tarurruka.
A ranar Lahadi Korea ta Kudu ta tabbatar da samun sabbin mutum 98 masu dauke da cutar coronavirus a kasar inda adadin ya ragu matuka sakamakon a watan Fabrairu an taba samun mutum 909 da suka taba kamuwa a rana guda.
Jihohin da aka samu Covid-19 a Najeriya
Legas - 19
Abuja - 4
Ogun - 2
Ekiti - 1
Oyo - 1
Jimla- 27
Wadanda suka warke- 2
Labarai da dumi-dumi, An sake samun mutum daya da ya kamu a Abuja
Bayan mutum hudu da hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya ta bayyana cewa sun kamu da Coronavirus a ranar Lahadi, an sake samun mutum daya a Abuja.
Cikin mutum hudu na farko da aka samu a yau, uku 'yan jihar Legas ne daya kuma daga jihar Oyo.
A halin yanzu mutum 27 aka tabbatar suna dauke da cutar a Najeriya inda kuma aka sallami mutum biyu daga cikinsu bayan sun warke.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Farawa
Bayani kan maƙala
Marubuci, Mustapha Musa Kaita
Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist
Masu bibiyarmu a wannan shafin barkanmu da wannan rana ta Lahadi.
Wannan shafin zai rinka kawo muku labarai da bayanai kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya musamman kan annobar coronavirus.