Abubuwan da suka faru a Nigeria da sassan duniya kan coronavirus
Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma wasu sassan duniya, musamman rahotanni kan annobar coronavirus.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail
Majalisar dattawa ta dage zama saboda Coronavirus
Majalisar Dattawan Najeriya ta dage zamanta har sai nan da makonni biyu saboda coronavirus.
Shugaban Majalisar Dattawan Ahmad Lawan ne ya bayyana haka bayan wani zama da majalisar ta a yau.
Kasar a halin yanzu ta gano mutum 40 masu dauke da cutar inda har ta yi sanadiyar mutuwar mutum daya biyu kuma sun warke.
Lawan ya bukaci 'yan kasar da su ci gaba da bin ka'idojin da hukumar da ke yaki da yaduwar cututtuka ta NCDC ta gindaya.
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnan jihar Gombe na tattaunawa da sarakunan gargajiya
Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya yana taro da sarakuna da sauran masu ruwa da tsaki a jihar domin tattauna yadda za a shawo kan annobar coronavirus.
A wurin taron nan dai dukkan mahalarta sun zauna a nesa da juna.
Asalin hoton, Gombe Government
Asalin hoton, GBGH
Asalin hoton, GMBH
Asalin hoton, GMGH
Asalin hoton, GMGH
Covid-19: Mutum 102,000 sun warke a fadin duniya
Sabbin alkaluma kan coronavirus a fadin duniya na nuna cewa kasashen duniya kusan 190 ne aka tabbatar da bullar cutar.
Sama da mutum 300,000 da ke dauke da cutar na a wajen China, kasar da a can ne cutar ta fara bulla kamar yadda bayanai daga jami'ar John Hopkins suka nuna.
Cikin mutum 382,000 da aka tabbatar sun kamu da cutar a fadin duniya, mutum 102,000 sun warke inda mutum 16,600 kuma sun mutu.
Sai dai ana ganin asalin yawan mutanen da ke dauke da cutar ta coronavirus ya wuce yadda ake tunani sakamakon wasu da ke dauke da cutar musamman wadanda alamominta ba su fito fili a tattare da su ba a musu gwaji ba.
Za a dage wasannin Olympics
Asalin hoton, Getty Images
Akwai yiwuwar dage wasannin Olympics na Tokyo 2020 a yau din nan kamar yadda sashen BBC na wasanni ya fahimta.
Mai magana da yawun kwamitin wasannin na kasa da kasa ya ce " kwamitin na tattaunawa da gwamnatin Japan, da masu shirya gasar da duk masu ruwa da tsaki kan yiwuwar dage wasannin kuma za a sanar da halin da ake ciki nan ba da jimawa ba."
A daren Litinin ne kwamitin wasannin gasar Olympic na kasar Amurka ya ce babu makawa za a dage wasannin.
Za a dai fara wasannin ne ranar 24 ga watan Yulin 2020, bisa yadda aka tsara.
Thailand za ta sa dokar ta-baci kan coronavirus
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin kasar Thailand ta shirya tsaf domin sanya dokar ta-baci sakamakon ci gaba da yaduwar annobar coronavirus a tsakanin 'yan kasar.
Firai minista, Prayuth Chan-cha ya ce za a sa dokar ta-baci ta wata guda a ranar Alhamis.
Hakan dai a cewar firai ministan za ta bai wa gwamnati damar daukar karin matakan sanya mutane bin dokokin kare kai daga kamuwa da coronavirus.
Wannan dai na zuwa ne bayan da aka karin mutum 106 da cutar ta harba, inda mutum uku suka mutu.
Kawo yanzu dai mutum 827 ne suka harbu da cutar a fadin kasar, inda jimillar mutum hudu suka mutu.
Coronavirus: Sojoji sun tsinci gawarwakin tsoffi yashe a Sipaniya
Asalin hoton, Getty Images
Sojojin da aka tura birnin Madrid na Sipaniya domin taimaka wa wajen yaki da yaduwar annobar coronavirus sun tsinci tsoffi dauke da wannan cuta da aka yi watsi da su.
Da dama mutanen da cutar tayi ajalinsu a kasar sun kasance a yashe a gidan tsoffi.
Tuni aka kaddamar da bincike kan wannan al'amari.
A ranar litinin Sipaniya ta ba da rahotan mutuwar sama da mutum 460 - akasari a birnin Madrid.
Halin da annobar ta jefa kasar ya tilasta mata samar da wurin sanyi inda ake tara gawawwaki yanzu haka.
Sipaniya ce kasa ta biyu a Turai bayan Italiya da wannan annoba tafi yi wa illa.
An kafa dokar fita a Burtaniya saboda coronavirus
Asalin hoton, Getty Images
Birtaniya ta kafar dokar hana fita a matsayin wani sabon matakin dakile bazuwar annobar coronavirus tsakanin al'ummarta.
A jawabin da ya gabatar ga al'ummar kasar, Firaminista Boris Johnson ya umarci a gaggauta rufe dukkan shaguna ban da na bukatun yau da kullum.
Mista Johnson ya ce mutane na da damar fitowa ne kawai idan akwai bukatar sayen kayan amfanin yau da kullum ko na neman taimako a fanin lafiya, ko ga masu bukata ta musamma ko motsa jiki sau daya a rana.
A can kuma Jamus an haramta tarukan mutane sama da biyu, kuma 'yan sanda na da damar tarwatsa duk wani taro.
Mutane 55 Coronavirus ta kashe a Burtaniya a cikin sa'o'i 24 .
'Nan ba da jimawa ba za mu shawo kan coronavirus a Amurka'
Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Trump ya shaida wa manema labarai cewa hasashensu ya sauya, don haka yana sa ran matakan da suke dauka wurin yaki da coronavirus a kasar za su kasance na makonni ne kawai, ba wai watanni ba kamar yadda suka yi tunani da farko.
Ya ce al'ummura za su koma kamar yadda suke nan ba da jimawa ba a Amurka'
"Na yi tunanin za a samu karin mutanen da za su rasa rayukansu bayan matakan da aka dauka na tsayar da al'amura cak da hana fita sakamakon yaduwar cutar."
Kwararu a fanin lafiya sun yi gargadi cewa ya zama tilas Amurka ta ci gaba da tsarin takaita cudanya kafin a cimma karfin yaduwar cutar tsakanin al'ummarta.
Coronavirus ta kashe Dibango
Asalin hoton, bbc
Daya daga cikin fitattun mawakan Afirka Manu Dibango mai shekara 86 ya mutu bayan kamuwa da cutar coronavirus.
An dai kai mawakin wanda dan asalin kasar Kamaru zuwa wani asibiti a kasar Faransa.
Dibango ya fara waka da busa a 1950, inda kuma ya yi suna a duniya.
Duk da cewa haifaffen kasar Kamaru ne, Dibango ya gudanar da harkokin wakokinsa a kasashen Faransa da Belgium da Jamaica da kuma jamhuriyar dimokradiyyar Congo da Ivory Coast baya ga kasarsa wato Kamaru.
Dibango ne dai ya kwarara wa fitattun mawaka irin su Michael Jackson da Rihanna da sauransu gwiwar yin waka.
Mutum 40 ne suka kamu da coronvirus a Najeriya - NCDC
Hukumar da ke takaita yaduwar cututtuka ta Najeriya, NCDC ta ce ya zuwa karfe 11 da daren Litinin, an samu mutum 40 da suka kamu da cutar coronavirus.
Hukumar ta ce a daren Litinin din ne aka samu karin mutum hudu da ke dauke da cutar, inda mutum uku suka kasance a birnin Legas sannan mutum a Abuja.
Mutum biyu daga cikin hudun sun koma kasar ne daga bulaguro daga kasashen waje, in ji hukumar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Coronavirus ta fantsama zuwa Myanmar
Asalin hoton, Getty Images
A karon farko an samu bullar coronavirus a Myanmar, inda wasu maza biyu da suka koma kasar daga ketare suka shiga da cutar.
Kafin wannan lokaci Myanmar ce kasa ta karshe a kudu maso gabashin Asiya, ban da Laos da ta kasance babu cutar duk da cewa ta hada iyaka da China.
Koda yake kwararu a fannin lafiya sun ce rashin kayan gwaji na iya boye gaskiya ko adadin masu dauke da cutar.
A Makon da ya gabata Myanmar ta dauki matakin rufe iyakokinta na tuddai da kuma haramta taruka, sai dai shagunan sayar da barasa da na cin abinci sun ci gaba da kasancewa a bude.
Coronavirus: China za ta sassauta dokar hana fita a Wuhan
Asalin hoton, Getty Images
Jami'ai a China sun sanar da cewa za a sassauta dokar hana fita a birnin Wuhan daga ranar 8 ga watan Afrilu.
Jami'an gwamnati na rikon kwarya a kasar sun ce daga wannan lokaci za a bai wa jami'an lafiyar kar-ta --kwana damar ficewa daga birnin.
Kafin wannan sanarwa China ta bayar da rahotan samun sabbin mutane da suka harbu da Coronavirus a birnin na Wuhan.
Hakan ya kawo karshen kwanaki biyar da aka shafe ba tare da samun wani sabon mutum da ya kamu da cutar a birnin da annobar ta soma ba.
Jami'ai a yankin sun ce a cikin sa'o'i 24 da suka gabata an samu mutum 8 da suka kamu da cutar.
Sai dai hudu daga cikinsu matafiya ne da suka koma kasar daga ketare.
Niger na daukar matakai kan coronavirus
Asalin hoton, Getty Images
A jamhuriyar Nijar yayin da aka samu mutum na 3 da ya harbu
da cutar Coronavirus, hukumomin kasar na karfafa matakan dakile yaduwarta
tsakanin al'umma .
Baya ga motoci na musamman na daukar masu cutar da hukumomin suka samar sun kuma kaddamar da aikin fasa kasuwani da wasu wurare na haduwar
jama'a tare da yin feshin maganin kashe kwayoyin cuta a wuraren.
Har wa yau, an kuma samar da kayan wanke
hannu a wasu muhimman wurare a birnin Yamai .
Gwamnatin Najeriya ta rufe filin jirgin saman Abuja da Legas
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Najeriya ta rufe filayen jirgin sama na Abuja da Legas bisa la'akari da yadda annobar coronavirus ke ci gaba da yaduwa kamar wutar daji.
Yanzu haka dai kididdigar hukumar da ke hana yaduwar cututtuka ta kasar ta nuna an samu mutum 40 da aka hakkake sun kamu da wannan annoba.
Wannan rufewar dai ta shafi tashi da saukar jiragen da suke zuwa daga kasashen waje, inda za a ci gaba da gudanar da zirga-zirgar cikin gida.
A makon da ya gabata ne dai hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar ta sanar da rufe filayen guda biyu da ta ce za a yi ranar Litinin.
A wata sanarwa da babban darektan hukumar, Kaftin Musu Nuhu ya sanya wa hannn, hukumar ta ce rufe filin jirgin Abuja da Legas kari ne a kan rufe filin jirgin Kano da na Enugu da kuma na Fatakwal wadanda suka hanyoyi ne da annobar ka iya shiga kasar ta cikinsu.
A ranar Asabar din da ta gabata ne dai hukumar ta rufe na Kano da Enugu da kuma Fatakwal.
Nuhu ya kara da cewa rufe filayen jirgin zai kasance har zuwa ranar 23 ga watan Afrilu, sai dai ya ce za a iya sauka da tashi a yayanyin bukatar gaggawa a dukkanin filayen jiragen.
Farawa
Masu bibiyarmu da fatan kun wayi gari lafiya. Ya ya aka ji da zulumin annobar coronavirus? Allah ya takaita mana. Wadanda suka kamu kuma Allah ya ba su lafiya. Allah kuma ya kare sauran jama'a. Da fatan za ku kasance da mu a yau ma domin kawo muku irin abubuwan da ke wakana dangane da cutar coronavirus a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rufewa
A nan muka zo karshen labarai da rahotanni da muke kawo muku kan cutar coronavirus a wannan rana. Sai ku tare mu ranar Talata inda za ku ji sabbin bayanai kan wannan annoba.
Amma idan kuka duba kasa, za ku iya karanta labaran da muka kawo muku a wannan rana. Kazalika za ku iya ci gaba da bibiyarmu a shafukanmu na sada zumunta da muhawara.
Mu kwana lafiya.
Coronavirus: An bayar da umarnin rufe kotunan Najeriya
Alkalin Alkalan Najeriya, Mai shari'a Tanko Mohammed, ya bayar da umarnin dakatar da dukkan zaman shari'a da kotunan kasar ke yi, sai dai a kan lamari na gaggawa saboda fargabar cutar COVID-19.
Mai shari'a Mohammed ya bayyana haka ne a sanarwar da ya fitar ranar Litinin.
Kotunan za su dakatar da zaman nasu ne daga ranar Talata 24 ga watan Maris, a cewar Alkalin Alkalan.
Najeriya na cikin kasashen da aka samu bullar cutar ta COVID-19 inda mutum 36 suka kamu, kuma daya daga cikinsu ya mutu.
Asalin hoton, Twitter/Nigeria Presidency
Bayanan hoto, Mai shari'a Tanko Mohammed ya ce za a rufe dukkan kotuna ne ranar Talata
Za a rufe daukacin Afirka ta Kudu saboda coronavirus
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya sanar da cewa za a rufe dukkan kasar daga ranar Alhamis domin shawo kan yaduwar coronavirus.
Mr Ramaphosa ya bayyana haka ne a jawabin talbijin da ya yi wa 'yan kasar ranar Litinin.
Ya ce mutane za su zauna a gidajensu tsawon kwana 21.
Hakan na nufin dukkan 'yan kasar ta Afirka za su "zauna a gidajensu sai dai idan akwai dalilai masu karfi" da za su sanya su fita, a cewar sakon da ofishin shugaban asar ya wallafa a Twitter.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Coronavirus: Zamfara za ta rufe dukkan ma'aikatunta
Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya ta bayar da umarnin rufe dukkan hukumomi domin kauce wa kamuwa da coronavirus.
Gwamna Bello Matawalle ne ya bayyana haka a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Litinin.
"Na bayar da umarni cikin gaggawa na rufe dukkan ofisoshin gwamnati da ma'aikatu da hukumomi.
Kazalika za a rufe makarantun allo. Dukkan ma'aikatan gwamnati su yi zamansu a gida, sannan an haramta taron da ya wuce na mutum 20", in ji gwamnan.
Ya zuwa yanzu dai an samu mutum 36 da suka kamu da cutar ta Najeriya, amma babu wanda ya harbu da ita a jihar ta Zamfara.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Labarai da dumi-dumi, Za a rufe dukkan iyakokin Najeriya saboda coronavirus
Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa za a rufe dukkan iyakokin kasar na tudu a yunkurin dakile yaduwar cutar coronavirus.
Shugaban kwamitin yaki da cutar coronavirus kuma Sakataren gwamnatin kasar Mr Boss Mustapha ne ya sanar da daukar wannan mataki ranar Litinin da yamma.
Ya ce daga Litinin din nan zuwa mako hudu da ke tafe, iyakokin kasar na tudu za su kasance a garkame domin hana yada cutar ta coronavirus.
A cewarsa, an dakatar da taron majalisar ministoci da ake yi dukkan Laraba.
Mr Boss Mustapha ya shawarci dukkan mazauna Abuja da Lagos su zauna a gidajensu sannan su guji halartar taron jama'a.
Da ma dai gwamnatin Najeriya ta bayar da umarnin rufe dukkan filayen jiragen saman kasar daga ranar 23 ga watan Maris.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.