Abubuwan da suka faru a Nigeria da sassan duniya kan coronavirus

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma wasu sassan duniya, musamman rahotanni kan annobar coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Coronavirus: Jami'an tsaron Uganda na korar mutane daga tituna

    Uganda

    Asalin hoton, Getty Images

    Kasar Uganda ta sanar da samun karin masu dauke da coronavirus mutum hudu abin da ya kara yawan masu dauke da cutar zuwa 18.

    Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da gwamnatin kasar ta sa dokar kulle ta mako biyu, inda jami'an tsaro ke fatattakar duk wanda suka gani a waje.

    Shugaba Yoweri Museveni ya ce an gano sabbin masu dauke da cutar da aka samu ne bayan an gudanar gwajin cutar a kan mutum 197 da suka koma kasar daga Dubai.

    Yanzu haka dai harkokin kasuwa a Kampala, babban birnin kasar sun tsaya cak.

    Ana fargabar cewa matalauta ka iya shiga wani hali sakamakon sai sun fita suke neman abin da za su saka a bakinsu bayan kuma gwamnati ba ta ba su tallafi ba.

  2. Coronavirus: Za a rufe Kinshasa na Congo

    Felix Tshisekedi

    Asalin hoton, Getty Images

    Daga gobe Asabar ne za a rufe Kinshasa babban birnin Congo. Gwamnan jihar ya ce dole ne kowa ya zauna a gida na tsawon kwana hudu sai dai ban da likitoci da sauran jami'an lafiya.

    Za a bar mutane su sayi kayan abinci cikin kwana biyu masu zuwa sannan za a maimaita wannan tsarin na tsawon makwanni uku nan gaba.

    Gwamnan ya bukaci jama'ar Kinshasa da su kwantar da hankalinsu.

    A farkon makon nan ne shugaba Felix Tshisekedi ya ba da umarnin dakatar da shige da fice a babban birnin wanda ya ke da sama da mutum 50 masu coronavirus.

  3. Coronavirus: Amurka ta sa lada ga wanda ya kama mata shugaban Venezuela

    Nicolas Maduro

    Asalin hoton, gett

    Gwamnatin Venezuela ta zargi Amurka da tuhumar Shugaba Nicolas Maduro domin boye gazawarta wajen dakile bazuwar coronavirus.

    Masu gabatar da kara a Amurka sun ba da tayin dala miliyan 15 ga duk wasu bayanan da za su kai ga kama Mr Maduro.

    Sun zargi Maduro da manyan jami'ansa da hada baki da 'yan tawayen Columbia wajen shigar da tan din hodar iblis zuwa Amurka.

    Ministan wajen Venezuela Jorge Arreaza ya ce gwamnatin Trump na kokarin samun goyon baya ne daga 'yan Latin da ke zaune a Florida gabanin zaben shugaban kasar da za a yi a watan Nuwamba.

  4. Coronavirus: Rasha ta hana zirga-zirgar jirage

    Russia flight ban

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Rasha ta dauki matakin hana zirga-zirgar jiragen sama a kasar.

    Sai dai wannan mataki bai shafi jiragen da ke aikin gaggawa ba musamman masu dawo da 'yan kasar ta Rasha gida daga wasu kasashen.

    Wannan shi ne mataki na baya-bayan nan da Rasha ta dauka a kokarin yaki da cutar coronavirus.

    Tun a makon daya gabata ne aka rufe hanyoyin layin dogo da na teku tare da hana baki shiga Rasha.

  5. Coronavirus: Mutum biyu sun mutu a Afirka ta Kudu

    Police

    Asalin hoton, Getty Images

    Kasar Afirka ta Kudu ta samu mutum biyu na farko da suka mutu sakamakon coronavirus.

    ministan lafiya na kasar, Zwelini Mkhize ya sanar ranar Juma'a cewa mutum biyun da suka mutu dukka sun fito ne daga lardin Yammacin Cape, inda daya ya mutu a asibitin kudi na biyun kuma a asibitin gwamnati.

    Ya kara da cewa ya zuwa yanzu yawan mutanen da suka mutu sun wuce 1,000, inda ya ce nan gaba kadan za a bayar da kididdiga.

    Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da kasar ta aiwatar da dokar kulle ta kwana 21 a ranar Juma'a domin takaita yaduwar cutar coronavirus.

    Tuni dai jami'an tsaron kasar suka fara shawagi don ganin jama'a na martaba dokar rufe kasar da aka dauka ta ba shiga ba fita har tsawon makwanni uku aiwatar da dokar rufe makwanni uku.

  6. Coronavirus: Kamfanin BUA Group ya bayar da gudunmowar N1bn

    Abdul Samad

    Asalin hoton, Bua Group Twitter

    Bayanan hoto, Abdul Samad Rabi'u da Aliko Dangote

    Kamfanin BUA Group ya sanar da bayar da gudunmowar naira bilyan daya ga gwamnatin Najeriya domin yaki da cutar coronavirus.

    Mai kamfanin na BUA Group, Abdul Samad Rabiu wanda ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya kara da cewa baya ga kudin, kamfanin ya kuma bayar da kayan aiki da suka hada da injina da na'urorin gwaji da sauransu ga jihohi 9 na kasar.

    Jihohin dai su ne Lagos da Kano da Adamawa da Edo da Kwara da Rivers da Abia da Akwa Ibom da kuma Sokoto.

    Abdul Samad ya kuma ja hankalin sauran kamfanoni masu zaman kansu da su tallafa wa gwamnati wajen ganin an dakile wannan annoba, inda ya kara da cewa kamfanin nasa zai bayar da naira bilyan dayar ne ta hanyar babban bankin Najeriya.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  7. Coronvirus: China ta hana 'yan kasar waje shiga kasar

    China

    Asalin hoton, AFP/GETTY

    Kasar China ta sanar da hana 'yan kasar waje shiga kasar ko da kuwa suna da iznin zama a kasar.

    Har wa yau, Chinar ta takaita yawan jirage dauke da 'yan kasar da ke shiga China zuwa daya a mako, sannan kuma ta hana a cika jirgi dankam.

    Duk da cewa yanzu ne China ta samu mutanen da suka kamu da coronavirus a cikin gida ranar Juma'a, kusan dukkan sabbin mutanen da suka kamu da cutar sun same ta daga kasashen waje.

    A ranar Alhamis an samu sabbin mutanen da suka harbu da cutar guda 55 a fadin kasar, inda 54 sun harbu da cutar a kasashen waje.

  8. Amurka ta zarta China yawan masu coronavirus

    Donald Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Yanzu ta tabbata cewa Amurka ta yi wa China fintinkau wajen yawan mutanen da ke dauke da cutar cornavirus.

    Amurka dai ya zuwa yanzu na da mutum 85,500 da ke dauke da cutar.

    Wasu sabbin alkaluma da jami’ar Johns Hopkins University ta tattara sun nuna Amurkar ta wuce China da kimanin 4000.

    China dai na da wadanda suka kamu da cutar 81,782, inda a baya Italiya take rufe mata baya da 80,589.

    To sai dai har kawo yanzu, China da Italiya na gaba da Amurkar wajen yawan masu mutuwa sakamakon cutar ta coronavirus, inda mutum 3,291 suka mutu a China yayin da kuma 8,215 suka mutu a Italiya.

    Ita kuwa Amurka mutum 1,300 ne ta rasa sakamakon wannan annoba.

    Wannan karuwar yawan alkaluman na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da shugaba Donald Trump ya sanar da cewa kasar tasa ba da dadewa ba za ta yaki cutar coronavirus.

  9. Budewa

    Coronavirus

    Jama'a da fatan an wayi gari lafiya. Yaya muka ji da darurar coronavirus? Allah ya takaita mana. Da fatan za ku ci gaba da kasancewa da shafin bbchausa.com domin samun bayanai da dumi-duminsu dangane da annobar ta coronavirus a Najeriya da ma sassan duniya

  10. Rufewa

    Masu bin mu a wannan shafi anan muka kawo karshen labarai da rahotanni kai tsaye kan coronavirus a duniya a yau.

    Kuna iya zuwa kasan shafin don karanta wadanda suka wuce.

    Sai kuma gobe da misalin 9 na safe idan Allah Ya kai mu.

    A madadin dukkan wadanda suka sa hannu a aikin na yau kamar Usman Minjibir da Umar Mika'il da Nasidi Adamu Yahaya, ni Halima Umar Saleh nake cewa Allah Ya ba mu alkhairinSa.

  11. 'Yan sanda sun fara korar mutane a titunan Abuja

    Abpkin aikinmu Yusuf Ibrahim Yakasai ya ga yadda 'yan sand ke korar mutane da su tafi gidajensu a wasu titunan Abuja da misalin karfe 9.30 na dare.

    Hakan dai wani mataki ne na tursasawa mutane bin dokar takaita zirga-zirga don hana yaduwar coronavirus.

  12. Coronavirus: Yanzu lokaci ne na kishin kasa da sadaukarwa

    Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya ce yanzu lokaci ne da ya kamata a dauki mataki a yi kishin kasa da sadaukarwa da kuma hada kai don yakar annobar Covid-19.

    Jonathan ya fadi hakan ne a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis.

    Ya ce ''A matsayinmu na kasa daya, namu labarin shi ne tarihin irin nasarorin da muka samu a lokacin da muke fuskantar wani kalubale na kasa ko na duniya.

    ''A shekarar 2014, ta hanyar sadaukarwa ne da hadin kai muka yaki annobar cutar Ebola.

    ''A yau duniyarmu na fuskantar wani kalubale na duniya da ke yi wa zaman lafiyarmu da fatanmu da walwalarmu barazana.

    ''A fadin duniya yanayin duk ya zama na tsoro da fargaba na irin ta'asar da sabuwar makiyiyarmu coronavirus za ta yi mana,'' a cewar tsohon shugaban Najeriyar.

    Jonathan

    Asalin hoton, Twitter

  13. Bayanai na baya bayan nan a Afirka kan coronavirus

    Kasashen nahiyar Afirka sun zage dantse a kokarinsu na hana yaduwar coronavirus.

    Har yanzu ba a samu yaduwar cutar sosai a nahiyar ba - mutum 2,700 ne suka kamu da cutar a kasashe 46.

    Ana fargabar adadin mutanen da suka kamu da cutar a Afirka zai karu cikin gaggawa saboda yadda ake samun yada cutar tsakanin mutum da mutum, da rashin isassun kayan kula da lafiya a akasarin kasashen da ke nahiyar

    Ga bayanai na baya bayan nan kan coronavirus a Afirka:

    • Uganda ta haramta zirga-zirgar ababen hawa nan take, lamarin da ya haddasa tsoro da fargaba a babban birnin kasar, Kampala. Jami'an tsaro sun rufe kasuwanni a babban birnin kasar kuma titunan birnin na Kampala sun kasance fayau babu kowa.
    • Najeriya, wacce ita ce kasar da ta fi yawan jamaa a Afirka inda take da akalla mutum miliyan 200, ta ce za ta haramta zirga-zirga a cikin kasar, ko da yake har yanzu bata fadi ranar da za ta yi hanin ba.
    • A kasar Kenya, wacce ita ce ma fi karfin tattaliin arzikin Gabashin Afirka, Shugaba Uhuru Kenyatta ya sanar da sanya dokar hana fitar dare daga ranar Juma'a.
    • Kazalika shugaban Kenya ya yarda a rage albashinsa da kashi 80 cikin dari, a yayin da kasar ke shirin fuskantar kalubalen tattalin arzikin da mutane za su fada a ciki - sannan ya nemi sauran jami'an gwamnati su yarda a rage albashinsu.
    • Idan muka sake komawa Najeriya, gwamnati ta karbi gudunmawa, ciki har da takunkuman rufe fuska 100,000, daga attajirin nan dan kasar China Jack Ma
    • A Afirka ta Kudu, fitaccen malamin addinin Kirista Andy Buchan ya ce ya kamu da Covid-19, yayin da kafafen watsa labaran kasar suka bayar da rahoton cewa dole mutumin da ya ci $426,000 a caca ya jira sai harkoki sun koma yadda suke kafin a ba shi garin kudinsa. Za a rufe kasar tsawon mako uku daga ranar Alhamis da daddare kuma mutane sun yi tururuwa a kantuna domin sayen kayayyakin bukata.
      Uganda ta haramta zirga-zirgar ababen hawa nan take,

      Asalin hoton, AFP

      Bayanan hoto, Uganda ta haramta zirga-zirgar ababen hawa nan take,
    • Labarai da dumi-dumi, An samu karin mutum 14 da suka kamu da coronavirus a Najeriya

      Hukumar hana yaduwar cutuka ta Najeriya ta ce an samun karin mutum goma sha hudu da suka kamu da cutar covid-19.

      A sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Alhamis da daddare, hukumar ta ce 12 daga cikinsu a Lagos suke yayin da biyu kuma suke Abuja.

      Ta kara da cewa an gano shida daga cikinsu ne a wani jirgin ruwa, uku kuma matafiya ne a tsakanin jihohin kasar, daya kuma wanda ya yi mua'amala da mutumin da aka tabbatar yana da cutar ne.

      Kawo yanzu, an tabbatar da mutum 65 da suka kamu da cutar, yayin da uku suka warke sannan daya ya mutu.

      Kauce wa X
      Ya kamata a bar bayanan X?

      Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

      Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

      Karshen labarin da aka sa a X

    • Wani na hannun daman gwamnan Bauchi ya kamu da coronavirus

      Wani na hannun daman Gwamna Bala Muhammaed Kaura na Bauch, ya kamu da coronavirus, a cewar gwamnatin jihar.

      Shugaban ma'aikatan gwamnatin Bauchi Ladan Salihu ne ya tabbatar wa BBC da labarin. Sai dai hukumar NCDC ba ta kai ga sanar da sake samun bullar cutar daga Bauchi ba a hukumance.

      Mutumin na daga cikin mutane da dama da aka yi wa gwajin, wadanda ake zargin sun yi mu'amala da gwamnan, wanda aka gano yana dauke d cutar a ranar Talata.

      Ladan Salihu ya ce duk sauran mutanen gwajin ya nuna ba sa dauke da cutar.

      Sannan ya ce tuni aka bayar da umarnin takaita shiga gidan gwamnati ga mutanen da bai zama lallai su shiga ba.

      Dama tuni aka bai wa ma'aikatan gwamnatin jihar hutu wadanda suke daga mataki na 12 zuwa kasa.

    • Mutum 712 sun sake mutuwa cikin sa'a 24 a Italiya

      Mutum 712 sun sake mutuwa cikin sa'a 24 a Italiya, inda a yanzu yawan wadanda suka mutu a kasar ya kai 8,215.

      A jiya ma an sanar da mutuwar mutum 662 cikin sa'a 24, amma Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta kasar ba ta hada da mutum 50 da suka mutu a yankin Piedmont.

      Sabbin alkaluman sun nuna yadda aka samu kari kan mace-macen da aka yi a ranar Laraba.

      Hakan ya biyo bayan mutuwar mutum 743 a ranar Talata, da 602 a ranar Litinin, sannan 650 sun mutu ranar Lahadi, sai kuma 793 da suka mutu ranar Litinin.

      Yawan masu dauke da cutar ya sake karuwa zuwa 80,539 daga na baya da yake 74,386 - alkaluman su ne mafi yawa da aka samu tun ranar 21 ga watan Maris, in ji hukumar.

    • Labarai da dumi-dumi, Coronavirus ta kashe fiye da mutum 100 a Birtaniya a kwana guda

      A karon farko fiye da mutum 100 sun mutu sakamakon coronavirus a Birtaniya a kwana daya.

      Adadin mutanen da suka mutu ya tashi daga 475 zuwa 578, a cewar jami'an kiwon lafiyar kasar.

      An yi wa mutum 104,866 gwajin cutar, kuma a cikinsu mutum 93,208 ba sa dauke da ita yayin da mutum 11,568 suke da coronavirus.

    • Baya ba ta da kadan...Ministar Abuja ba ta dauke da coronavirus

      Ramatu Tijjani

      Asalin hoton, @DrRamatuAliyu

      Karamar Ministar Abuja, babban birnin Najeriya da muka rawaito cewa ta yi gwajin coronavirus sannan ta killace kanta, sakamakon gwajin ya nuna ba ta dauke da cutar.

      Hajiya Ramatu Tijjani Aliyu ta wallafa a shafinta na Twitter cewa: "Ina farin cikin sanar da dukkanin 'yan uwa da kawaye da abokan aiki, har ma da mutanen kirki 'yan Abuja, cewa gwaji ya nuna ba na dauke da Covid-19.

      "Na gode wa Allah da lafiyar da ya ba ni a irin wannan lokaci na jimami," in ji ministar.

      Da yawa daga cikin jami'an gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari sun yi gwajin cutar bayan an tabbatar shugaban ma'ikatansa, Abba Kyari, ya kamu da cutar a ranar Talata.

      Mutum 10 ne suka kamu da cutar a Abuja zuwa yanzu. Sauran sun su ne:

      • Lagos - 32
      • Ogun - 3
      • Ekiti - 1
      • Edo - 1
      • Bauchi - 1
      • Osun - 1
      • Oyo - 1
      • Rivers - 1
      Kauce wa X
      Ya kamata a bar bayanan X?

      Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

      Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

      Karshen labarin da aka sa a X

    • Bayanan baya-bayan nan kan coronavirus daga Afirka

      Coronavirus

      Asalin hoton, Getty Images

      Kasashen Afirka na ci gaba da daukar matakai don kare yaduwar annobar coronavirus.

      Har yanzu masu dauke da cutar a nahiyar ba su da yawa, mutum 2,700 ne suka kamu da cutar a kasashe 46.

      Akwai fargabar cewa yawan masu dauke da cutar zai karu saboda masu ita na iya shafa wa marasa ita, da kuma yanayin tsarin lafiya maras inganci da ake da shi.

      A cikin bayanan baya-bayan nan:

      • Najeriya wadda ta fi kowacce kasa yawan al'umma a nahiyar, ta ce mai yiwuwa ta hana tafiye-tafiye tsakanin jihohin kasar amma har yanzu ba ta bayyana lokacin da za ta yi hakan ba
      • Kasar Uganda ta haramta dukkanin tafiye-tafiye nan take, abin da ya janyo fargaba a zukatan jama'a a babban birnin kasar Kampala. Jami'an tsaro sun rufe wuraren kasuwanci a birnin sannan kuma tituna sun kasance fayau
      • A Kenya kuwa, kasar da ta fi kowacce karfin tattalin arziki a Gabashin Afirka, shugaban kasar ne Uhuru Kenyatta ya rage albashinsa da kashi 80 cikin 100 yayin da yake kokarin saita kasar kan tsauraran matakan yaki da coronavirus, kuma ya bukaci sauran jami'an hgwamnati da su yi hakan. Sannan kuma ya ayyana dokar hana fitar dare daga ranar Juma'a
      • A gefe guda kuma, kasar Jamus ta ce ba za ta biya kudin takunkumin rufe hanci ba da ta saya bayan kayan sun bace a filin jirgin saman Kenya
      • A Najeriya, gwamnati ta samu tallafin yaki da cutar ne da suka hada da takunkumin rufe hanci 100,000 daga bilioniyan dan kasuwar China, jack Ma
      • A Afirka ta Kudu, shahararren dan darikar Evangelica, Buchan ya ce ya kamu da Covid-19, yayin da shi kuma wanda ya lashe cacar naira miliyan 156 (dala 426,000) aka ce sai ya jira an dage dokar hana fita a kasar sannan ya karbi kudinsa. Dokar ta mako uku za ta fara aiki ne ranar Juma'a kuma tuni jama'a suka shiga firgici na sayayyar rashin kan-gado
    • Coronavirus: Shin an fita da Buhari da Abba Kyari kasar waje?

      Mai taimaka wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kan harkokin sada zumunta, Bashir Ahmad ya karyata labarin da ake yadawa cewar an fita da shugaban da shugaban ma'aikatan fadarsa Abba Kyari zuwa kasar wajen don yi musu maganin coronavirus.

      Bashir Ahmad na wannan magana ce sakamakon wani sakon murya da ake ta yadawa cewar an fita da Buharin da Abba Kyarin waje a asirce don neman maganin cutar.

      Ya ce an nadi sakon muryar ne don jawo rudani da fargaba a zukatan mutane.

      Ya amabaci sunan wani mutum da ya ce shi ya fara yada wannan labarin kanzon kuregen.

      Tuni dai sakon ya bazu a shafun sada zumunta a Najeriyar.

      Kauce wa X
      Ya kamata a bar bayanan X?

      Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

      Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

      Karshen labarin da aka sa a X