Gwamnatin Kano na feshin magani kan coronavirus

Asalin hoton, KNSG
Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da shirin feshin magani a birnin baki daya tare da hadin gwiwar kamfanin Lee Group of Companies, a wani yunkuri na dakile cutar coronavirus.
Yayin da yake kaddamar da shirin a harabar gidan gwamnati, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce sun kaddamar da shirin ne albarkacin Ranar Tsafta ta kowace Asabar din karshen wata.
"Wannan wani yunkuri ne na tsaftace muhallinmnu. Muna yakar wannan annoba da duk abin da za mu iya. Saboda haka muke korarta daga muhallanmu kuma shi ya sa Ma'aikatar Muhalli ke da matukar muhimmanci a yanzu," Ganduje ya bayyana a wata sanarwa da mai magana da yawunsa Abba Anwar ya fitar ranar Asabar.

Asalin hoton, KNSG
Ganduje ya ce aikin tsaftace birnin zai kai ga kasuwanni da asibitoci da sauran wuraren taruwar jama'a.
Masu aikin tsaftace birnin sun fara da gidan gwamnati ne sannan suka wuce zuwa asibitin Muhammadu Abdullahi Wase (asibitin Nassarawa), inda gwamnan ya sanya ido kan aikin tare da wasu kwamishinoninsa.
Gwamna Ganduje ya kara da cewa dalilin da ya sa rufe iyakokin Kano bai shafi wasu muhimman abubuwa ba kamar kayan abinci shi ne, domin kar a gurgunta harkar kasuwancin jihar.
"Saboda kada mu gurgunta tattalin arzikin Kano, shi ya sa ba mu hana harkar kayan amfanin gaggawa ba irinsu abinci...Duk da cewa kasuwanni za su ci gaba da kasancewa a bude, muna kira ga mutane da su yi aiki da shawarwarin nesa-nesa da juna da kuma zama a gida."

















