Abubuwan da suka faru a Nigeria da sassan duniya kan coronavirus

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma wasu sassan duniya, musamman rahotanni kan annobar coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Yadda ranar Juma'a ta kasance a nahiyar Asiya

    Yadda ranar Juma'a ta kasance a nahiyar Asiya

    • Hukumomin Koriya Ta Kudu na ta rokokn mutane da su zauna a gida bayan da aka samu karin mutum 91 masu dauke da cutar, lamarin da ya sa yawan masu ita ya kai 9,332. Firai Minista Chung Sye-kyun ya shaida wa maneman labarai cewa ya fahimci tun da bazara ta zo zai yi wa mutane wahala su yi ta zama a cikin gida ba fita, amma ya ba da shawarar cewa ''gara a yi hakuri a sha wahalar hakan maimakon a ci gaba da fuskantar barazanar wannan annoba har tsawon lokaci.''
    • Firai Ministan Pakistan Imran Khan ya sanar da cewa zai kaddamar da wata tawaga ta matasa da ake kira Corona Relief Tigers, wadanda za su rarraba abinci ga mutanen da aka tursasa wa zama a gidajensu, a cewar wata jaridar kasar.
    • An umarci mazauna Tokyo babban birnin Japan da su zauna a gida a karshen mako, hakan ya jawo an samu dogwayen layuka a shagunan sayar da kaya don mutane na rububin yin cefane. Gwamnan birnin Yuriko Koike ya yi gargadi cewar Tokyo na gab da fukantar tashin hankalin karuwar wadanda za su kamu da cutar
    • Miliyoyn ma'aikatan kamfanoni a Bangladesh suna fuskantar barazanar yunwa bayan da masu sarin kayayyaki daga Turai da Amurka suka soke odar kayayyakin da suka yi, a cewar shugaban masu masana'antun yin kayayyaki a Bangladesh.
  2. Coronavirus: Mutum 969 sun mutu a rana daya a Italiya

    Mutum 969 ne suka mutu cikin sa'a 24 a Italiya sakamakon coronavirus, kuma mace-macen su ne wadanda suka fi na ko yaushe da aka taba samu yawa a kasar.

    Hakan na nufin zuwa yanzu mutum 9,134 ne cutar ta kashe a kasar.

    Tun da fari dai shugaban shukumar WHO Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce ''karancin kayayyakin aiki na yaki da cutar'' na daga cikin manyan barazanar da ake fama da ita wajen ceto rayuka.

    Italiya ce kasar da cutar ta fi muni a Turai. Kusan komai ya tsaya cak kuma mutane na kunshe a gidajensu kamar yadda aka yi umarni.

    Tun da fari a ranar Juma'a, hukumomi sun yi gargadi cewa, akwai yiwuwar aka kara tsawon lokacin matakan hana zirga-zirgar zuwa 3 ga watan Afrilu.

    Italy

    Asalin hoton, EPA

  3. Labarai da dumi-dumi, Adadin wadanda suka mutu a Italiya ya karu

    Italiya ta tabbatar da mutuwar mutum 969 sakamakon coronavirus cikin awa 24, jumullar wadanda suka mutu sun kai 9,134 a kasar.

    An samu sabbin wadanda suka kamu har 4,401, jumullarsu 66,414 a fadin kasar a yanzu.

    Wannan ne adadi mafi girma na rana daya a mace-macen da aka taba samu daga annobar coronavirus.

  4. Fafaroma zai gabatar da addu'o'i na musamman kan coronavirus

    Fafaroma Francis

    Asalin hoton, AFP

    Fafaroma Francis zai gabatar da addu'o'in 'Urbi et Orbi' a ranar Juma'a, wadanda aka saba yin su a ranakun Easter da kuma Kirsimeti.

    "Muna so mu mayar da martani ga wannan annoba da addu'a ta musamman," wani sako da aka wallafa a shafin Fafaroma ya bayyana a shafin Twiter.

    Zaman addu'ar da zai dauki tsawon awa guda, zai fara ne daga karfe 6:00 agogon Najeriya sannan zai gudana ne daga saman ginin Peter's da ke Fadar Vatican.

    Urbi et Orbi na nufin "zuwa ga birni da duniya".

  5. Sabbin mutum hudu sun kamu da coronavirus a Ethiopia

    Habasha

    Asalin hoton, Getty Images

    Kasar Habasha wato Ethiopia, ta bayar da rahoton karin mutum hudu da suka kamu da coronavirus, wadanda suka zama 16 jumulla a kasar.

    Sabbin mutanen sun hada da wanda aka samu a wajen babban birni Addis Ababa - wani dan shekara 61 a Adama, kilomita 100 daga Addis Ababa.

    Sauran su ne wani dan shekara 71 dan kasar Mauritius, da kuma wasu mata biyu 'yan Habasha 'yan kasa da shekara 30.

  6. An kama ma'aurata saboda yada labaran karya kan coronavirus

    Tanzania

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Mutum 13 ne suka kamu da coronaviurus a Tanzania

    'Yan sanda a Dar es Salaam, babban birnin Tanzania, sun ce sun kama wasu ma'aurata bisa zargin yada bayanan karya game da cutar coronavirus.

    Kwamishinan 'yan sandan birnin, Lazaro Mambosasa ya ce mata da mijin suna tafiya ne a cikin motar haya yayin da suka dinga aibata gwamnati a makon da ya gabata.

    Ya ce ma'uratan suna bata tunanin al'umma ne.

    "Sun ce coronavirus ba gaskiya ba ce sannan kuma gwamnati ba ta da abincin da za ta ciyar da dalibai, saboda haka take fakewa da annobar domin rufe makarantu," Mista Mambosasa ya fada wa 'yan jarida.

    Shugaban 'yan sandan ya kara da cewa, bayan jin haka ne ran sauran fasinjoji da ke cikin motar ya baci sannan suka umarci direban da ya nufi ofishin 'yan sanda mafi kusa, inda a nan ne suka mika su ga 'yan sanda.

    Mista Mambosasa ya ce an kammala bincike kan Elias Mwita, mai shekara 29 da kuma Rosemary Elias Mwita, mai shekara 41 kuma ana shirin gurfanar da su a gaban kotu.

    Zuwa yanzu Tanzania ta tabbatar da mutum 13 da suka kamu da coronavirus, takwas daga cikinsu 'yan kasar ne, biyar kuma 'yan kasar waje, mutum daya ya warke.

  7. Coronavirus: Wadanda ke mutuwa a Birtaniya na karuwa

    Mutanen da coronavirus ta kashe a Birtaniya sun karu daga 578 zuwa 759, a cewar Sashen Lafiya na kasar.

    Wannan ce karuwar mace-mace mafi girma a rana guda da aka fuskanta a Birtaniya.

    Ya zuwa yanzu mutum 14,579 ne aka tabbatar sun kamu da cutar, ciki har da Firai Minista Boris Johnson da Yarima Charles.

  8. Coronavirus: Tsoffin ma'aikatan jinya 7,000 za su koma aiki a Birtaniya

    Unguwar zoma da ma'aikatan jinya 7,000 da suka yi ritaya sun amimnce su koma bakin aiki a Birtaniya domin taimakawa a yaki da annobar coronavirus.

    Hukumar da ke kula da ma'aikatan jinya a kasar ta ce wadanda suka bar aiki shekara uku da suka wuce za su iya saka hannu kan rajijstar aiki kan Covid-19 ta wucin gadi.

    Za a tantance tsoffin ma'aikatan sannan a ba su damar taimakawa a yaki da coronavirus.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  9. Coronavirus: Yadda manyan masallatan Juma'a na Abuja suka kasance

    Abuja
    Bayanan hoto, Babban masallacin Abuja

    Za a iya cewa babu wani masallacin Juma'a da ke birnin Abuja da aka yi sallar Juma'a a cikinsa a yau din nan.

    Wannan dai ya biyo bayan umarnin da hukumar birnin Abuja ta bayar da hana taron jama'a da suka wuce guda biyu da manufar yakar cutar coronavirus.

    Wakilin BBC Buhari Muhammad Fagge ya zagaya birnin na Abuja inda ya ce babu wani masallaci da aka sallar Juma'a a cikinsa.

    Ga hotunan manyan masallatan birnin da suka kasance fayau

    Abuja
    Bayanan hoto, Babban masallacin Abuja
    Abuja
    Bayanan hoto, Babban masallacin Abuja
    Babban masallaci
    Bayanan hoto, Babban masallacin Abuja
    Annur
    Bayanan hoto, Masallacin Annur da ke Abuja
    Annur
    Bayanan hoto, Masallacin Annur da ke Abuja
  10. Sakataren ma'aikatar lafiyar Burtaniya ya kamu da coronavirus

    Burtaniya

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakataren Lafiya na Burtaniya, Hancock ya kamu da cutar coronavirus..

    Kamar firai ministan kasar, Boris Johnson, Hancock ya killace kansa duk da cewa alamomin cutar da ke tattare da shi ba masu tsauri ba ne.

  11. Ba a yi sallar Juma'a ba a masallatan Kaduna

    Masallacin Khamis da ke Tudun Wada, Kaduna

    Masallatan Juma'a da dama a birnin Kaduna ba su yi sallar Juma'a ba, yayin da aka shiga Juma'a ta farko a cikin dokar hana fita a garin da gwamnati ta kafa.

    Masallacin Malam Khamis da ke kan babbar hanyar Nnamdi Azikiwe a Tudun Wada, na daya daga cikin masallatan ba su yi sallar ba.

    Sai dai wasu Musulmai sun yi jam'in sallar Azahar a kananan masallatan da ke cikin unguwanni a madadin sallar Juma'a.

    Mutane sun ci gaba garzayawa na'aurar ATM don cire kudi a birnin.

    Kaduna

    Kazalika, an sanya shingayen bincike a mahadar manyan tituna.

    Kaduna

    Gwamnatin Jihar Kaduna ta saka dokar hana fita tare da kulle iyakokin jihar ne, wadda ta fara aiki a yau Juma'a, domin hana yaduwar coronavirus.

  12. Jami'in gwamnatin Rasha ya kamu da coronavirus

    Wani jami'in gwamnatin Vladimir Putin na Rasha ya kamu da cutar coronavirus, kamar yadda fadar Kremlin ta tabbatar.

    Wata kafar yada labaran kasar ta rawaito mai magana da yawun shugaban yana cewa shugaban, mai shekara 67, yana ci gaba da aikinsa lafiya kalau.

    Rasha ta bayyana rahoton mutane mafi yawa na rana guda da suka kamu - 196 ne suka kamu - inda yanzu suka kai mutum 1,036 a fadin kasar. Mutum uku sun mutu.

  13. 'Ba sai an jira gwamnati ba a yaki da coronavirus'

    El-faruk

    Asalin hoton, El-faruk

    El-faruk dan jarida ne a Jihar Nasarawa da ke arewa ta tsakiyar Najeriya kuma ya jagoranci wani gangamin wayar da kan al'umma game da cutar coronavirus.

    Dan jaridar ya raba wa mutane takunkumin rufe hanci wato Face Masks kyauta sannan ya rika ba su bayanan yadda za su tsaftace hannayensu a garin Keffi, a yunkurin dakile yaduwar cutar ta Covid-19.

    "Abu irin wannan idan ya taso ba jiran gwammnati za a yi ba, kuma kamar yadda muke gani a kasashen da suka ci gaba gwamnati da daidaikun mutane na sayo irin wadannan abubuwa ko su fito da kansu don wayar da kan mutane," in ji El-faruk.

    Ya kara da cewa amma a Najeriya har yanzu ba su ga hakan ba, abin da ya sa shi ya dauki gabarar yin abin da zai iya yi daga aljihunsa.

    Ya zuwa yanzu mutum 65 ne suka kamu da coronavirus a Najeriya, uku sun warke, daya ya mutu.

    El-faruk

    Asalin hoton, El-faruk

    El-faruk

    Asalin hoton, El-faruk

  14. Coronavirus: Masallatan Juma'a a Kano sun yi cikar kwari

    Juma'a

    An yi sallar Juma'a a kusan daukacin masallatan birnin Kano, inda jama'a suka cinkushe duk da cewa kwamishinan lafiyar jihar ya tattabatar wa da BBC cewa ma'aikatar kula da muhalli ta Kano ta yi feshi a dukkan masallatan na Juma’a.

    Kwamishinan ya kuma ce ma'aikatar tasa ta tabbatar mahalarta masallatan sun yi amfani da sinadarin nan na wanke hannu.

    Juma'a
  15. Abin da ke faruwa a Nahiyar Turai

    • Jamus ta fuskanci karuwar masu coronavirus, inda mutum 5,780 suka kamu a cikin awa 24, a cewar cibiyar Robert Koch Institute. Wadanda suka mutu sun karu da mutum 55, inda yanzu suka zama 253. Shugaba Angela Markel ta nemi a kara hakuri a yakin da ake yi sannan ta yi watsi da kiraye-kirayen da ake yi na sassauta hana fita da aka saka a makon nan.
    • A Faransa, Firai Minista Edouard Philippe ya ce annobar da ta fara a gabashin kasar yanzu ta cimma babban birnin Paris. Asibitoci ka iya shiga wani hali a birnin a cikin awa 24 zuwa 48, in ji Hospital Federation of France. Mutum kusan miliyan 1.2 sun fice daga yankin a makon da ya gabata. Mahukunta sun ce a makon da ya gabata, mutum 1,696 ne suka mutu, ciki har da 365 da suka mutu a rana guda.
    • Laifuka a biranen da aka hana zirga-zirga sun ragu da kashi 64 cikin 100 a watan Maris idan aka kwatanta da irin wannan lokaci a 2019, amma laifuka ta kafar intanet karuwa suke, a cewar ma'aikatar cikin gida. Hukumar 'yan sandan Turai ta bayar da rahoton cewa masu laifi sun fi harar kayayyakin tsafta na jabu da wayar hannu da kuma laifuka ta intanet.
    • Rasha ta bayar da rahoton mutum 1,000 da suka kamu da kuma uku da suka mutu. Ta umarci duka gidajen cin abinci da na shakatawa da su rufe daga ranar Asabar, sannan kuma mako mai zuwa an ayyana shi a matsayin "makon zaman gida".
    • Switzerland ma ta samu mutum 194 da suka mutu tun bayan faruwar annobar da kuma kusan mutum 1,000 da suka kamu cikin awa 24, a cewar hukumomin kasar.
    • A kasar Sifaniya, wasu kayan gwajin coronavirus da aka shigo da su daga China masu sauri guda 9,000, ba su taimaka ba.
  16. Labarai da dumi-dumi, Boris Johnson ya kamu da coronavirus

    Firai ministan Burtaniya, Boris Johnson ya kamu da coronavirus. Boris Johnson dai ya sanar da hakan ne a shafinsa na Twitter.

    Ya ce "' a jiya na samu wasu 'yan kananan alamun cutar coronavirus inda bayan gwaji ta tabbata cewa ina da cutar."

    Ya kara da cewa "yanzu haka ina killace amma zan ci gaba da jagorantar al'amuran gwamnati ta hanyar bidiyo."

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  17. Gwamnatin jihar Gombe ta rufe iyakokinta

    Gombe

    Asalin hoton, Gombe Government

    Gwamnatin jihar Gombe ta snaar da rufe iyakokinta a wani mataki na dakile bazuwar annobar coronavirus zuwa cikin jihar.

    Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya yayin wani jawabi ga manema labarai ya ce sun dauki matakin ne domin gudun 'yan jihar tasa su kwaso cutar daga wasu wurare ko kuma masu dauke da cutar su shigar da annobar jihar.

    Gwamnan ya kuma umarci ma'aikata daga mai mataki na daya zuwa na 12 da su yi aiki daga gida.

    Har wa yau gwamnan ya sanya naira milyan 500 domin yakar bazuwar cutar.

    Jihar ta Gombe dai ba ta da ko da mutum daya da ke dauke da wannan cuta, amma gwamnan ya ce yin rigakafi ne kawai zai hana annobar shiga jihar.

    Gombe ce jiha ta uku a jerin jihohin da suka rufe iyakokinsu bayan jihohin Kano da Kaduna.

  18. Coronavirus ta kashe 'yar shekara 16 a Faransa

    Fuskar wata matashiya mai suna Julie A 'yar shekara 16 ce ta karade shafukan intanet a kasar Faransa a yau Juma'a. Ita ce mafi kankantar shekaru da ta mutu sakamakon annobar coronavirus a kasar.

    'Yar uwarta mai suna Manon, ta yi gargadin cewa mutuwar 'yar uwar tata izina ce cewa cutar ta Covid-19 ba ta saurara wa kowa ba.

    "A makon da ya gabata ne Julie ta fara tari, sai kuma ya yi tsanani zuwa karshen mako. A ranar Litinin ne suka je ganin likita kuma a lokacin ne aka gano tana dauke da matsalar numfashi. Ba ta fama da wata cuta a baya," Manon ta fada wa jaridar Le Parisien.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    An kai Julie asibiti sannan aka sake mayar da ita wani asibitin a birnin Paris, inda aka sanya mata na'urar numfashi. Sai dai an makara saboda huhunta ya daina aiki.

    "Wajibi ne mu daina tunanin cewa cutar tsofaffi kawai take kamawa. Babu wanda zai tsira daga wannan cuta mai hayayyafa," in ji Manon.

  19. An yi sallar Juma'a a masallatai a Pakistan

    Lahore

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Pakistan har yanzu na shakkar bata wa shugabannin addini rai ta hanyar hana gudanar da sallolin a jam'i, sabanin mafi yawan kasashen musulmai da su dakatar da salloli a jam'i domin kaucewa yaduwar coronavirus.

    Akwai kusan mutum 1000 da suka harbu da cutar ta coronavirus, inda mutum takwas suka rasu.

    A ranar Alhamis ne dai gwamnatin ta bunta cewa akwai yiwuwar hana jama'a yin salloli a masallaci to sai dai ba ta yi cikakken bayani ba.

    Hakan dai na nufin gwamnatin na shakkar malaman addinin kasar da ke da karfin fada a ji.

    Har wa yau, ana alakanta rashin sanya dokar ne da kasancewar wannan watan na Sha'aban da wanda zai biyo masa wato Ramadan lokaci ne da malaman ke yin karatuttuka a masallatai wanda hana su na nufin tashin hankali.

    To sai dai gwamnatin yankin Sindh, inda nan ne ya fi samun masu dauke da cutar coronavirus ta dauki kwarya-kwarya dokar hana yin dandazon jama'a sallah a masallatai.

    Gwamnatin dai ta ce ka da masu sallah su wuce mutum biyar kacal.

    Ita ma gwamnatin lardin Balochistan ta sanar da irin wannan hani har zuwa 4 ga watan Afrilu.

    Pakistan

    Asalin hoton, Getty Images

  20. Coronavirus: Har yanzu wasu 'yan Australia na fita shan iska

    Australia

    Asalin hoton, Getty Images

    Duk da kiraye-kirayen sanya tazara ga juna da kebe kai, wasu jama'ar Melbourne na kasar Australia suna ci gaba da sharholiya a wuraren shakatawa.

    Australia dai na da masu dauke da cutar coronavirus fiye da 3000, inda ta yi dokar cewa duk mutmin da ya koma kasar daga kasar waje to sai an killace har na tsawon mako biyu a otal.

    Tuni dai gwamnatin kasar ta sanar da fitar da tallafin kudi $109bn domin shawo kan bazuwar cutar ta coronavirus.