Abubuwan da suka faru a Nigeria da sassan duniya kan coronavirus
Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma wasu sassan duniya, musamman rahotanni kan annobar coronavirus.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail
Labarai da dumi-dumi, Shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriya ya kamu da coronavirus
Shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriya Muhammad Babandede ya kamu da cutar coronavirus.
Shugaban ya tabbatar wa BBC hakan a safiyar Lahadi inda ya ce sakamakon gwajin da aka yi masa ya nuna cewa yana dauke da cutar.
Ya ce a makon da ya gabata ne ya dawo daga kasar wanda hakan ya ga cewa ya kamata yayi gwajin wannan cuta.
Shugaban ya bayyana cewa tuni ya killace kansa a gida.
Manyan biranen Najeriya 12 da coronavirus ta bulla
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar da ke yaki da yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta bayyana cewa a halin yanzu, mutum 97 ne suka kamu da cutar coronavirus a jihohi 11 na Najeriya sai kuma Abuja babban birnin kasar.
Tun bayan bullar cutar a kasar, mutum uku sun warke mutum daya kuma ya mutu.
Ga jerin jihohin da cutar ta bulla da kuma yawan mutanen da ta harba:
Lagos- 59
FCT- 16
Ogun- 3
Enugu- 2
Ekiti- 1
Oyo- 7
Edo- 2
Bauchi- 2
Osun-2
Rivers-1
Benue- 1
Kaduna- 1
Farawa
Bayani kan maƙala
Marubuci, Mustapha Musa Kaita
Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist
Masu bibiyarmu a wannan shafi barkanmu da wannan rana ta Lahadi. A yau ma za mu ci gaba da kawo muku labarai da rahotanni kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya musamman kan labaran da suka shafi annobar coronavirus.
Sai da safenku
Jama'a rahotannin kai-tsaye sun zo karshe a yanzu amma za mu ci gaba a gobe Lahadi idan Allah ya kai mu.
Umar Mikail ke cewa mu kwana lafiya.
Coronavirus ta kashe mutum fiye da 30,000 a duniya
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wata ma'aikaciyar lafiya take kula da mai dauke da Covid-19 a kasar Czech Republic
Mutane masu rai da suka ransu sakamakon annobar coronavirus, wadda ke haddasa cutar Covid-19, sun zarta 30,000 a duniya baki daya, a cewar alkaluman Jami'ar Johns Hopkins.
Italiya ce ta fi samun wadanda suka mutu da mutum 10,023.
A yau Asabar kasar Spain ta ce wadanda suka mutu a kasar 5,690 ne.
Sabbin bayanai daga Gabas ta Tsakiya
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Jami'an lafiya na yin gwajin coronavirus a Iran
Abin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya:
A Iran, daya daga cikin kasashen Covid-19 ta fi yi wa illa, za a kebe kashi 20 cikin 100 na kasafin kudin kasar na shekara domin yaki da annobar, in ji Shugaba Hassan Rouhani. A cikin awa 24 da suka gabata, mutum 139 ne suka mutu, jiumulla 2,517 a fadin kasar
Kungiyoyi a kasar Falasdinu sun janye zanga-zangar da suka shirya yi a mako zuwa a kan iyaka da Isra'ila saboda fargabar yaduwar coronavirus a yankin mai dandazon al'umma
Kasar Qatar ta bayar da rahoton mutum na farko da cutar ta kashe da kuma karin 28 da suka harbu - wadanda suka kamu sun kai 590 a kasar
Labarai da dumi-dumi, Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya kamu da coronavirus
Gwamnan iihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ce ya kamu da cutar coronavirus.
Gwamnan ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi ranar Asabar, inda ya ce ya killace kansa.
Kazalika ya ce har yanzu bai fara nuna alamun cutar ba.
"A farkon makon nan ne na yi gwajin cutar Covid-19, kuma sakamakon ya fito a yammacin yau. Ina mai bakin cikin shaida muku cewa ina dauke da cutar," in ji El-Rufai a wani bidiyo da gwamantin Kaduna ta wallafa a Twitter.
"Kamar yadda hukumomin lafiya suka tsara kan abin da mai dauke da cutar ya kamata ya yi, na killace kaina. Mataimakin gwamna zai ci gaba da jan ragamar kwamitin musamman kan Covid-19 sannan zan ci gaba da bayar da bayanai lokaci zuwa lokaci."
Nasir El-Rufai ya yi kira ga al'ummar jihar Kaduna su ci gaba da bin dokar da gwamnatinsa ta kafa a jihar da kuma shawarwarin hukumomi domin kare kansu daga Covid-19.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Labarai da dumi-dumi, An yi wa Garba Shehu gwajin Coronavirus
Malam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce an yi masa gwajin cutar coronavirus.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Asabar da daddare, Malam Garba Shehu, ya ce sakamakon gwajin da aka yi masa ya nuna cewa ba ya dauke da cutar.
"Ina ganin ya dace na yi adalci domin na kore fargabar da abokaina da 'yan uwa wadanda na yi mu'amala da su kwanan nan game da coronavirus. Masu yada labaran karya sun yi ta yamadidi da hauragiya a kaina da shugaban kasa wada nake yi wa aiki," in ji kakakin shugaban kasar.
Malam Garba Shehu na cikin manyan jami'an gwamnatin Buhari da suka fi yawan ganawa da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Malam Abba Kyari, wanda yanzu haka aka tabbatar yana dauke da cutar.
Hakan ne ya sa aka rika fargabar ko shi ma ya kamu da coronavirus.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Coronavirus: Abin da ya faru a duniya zuwa yanzu
Abubuwan da suka faru a yau zuwa yanzu:
A Najeriya, wadanda suka kamu da coronavirus sun kai 89 bayan an samu karin mutum takwas a ranar Asabar
Jihar Legas a Najeriyar dai, ta ce ta yi hasashen kusan mutum 39,000 ka iya harbuwa da cutar a jihar
Mutum 10,023 sun mutu a Italiya bayan mutum 889 sun mutu a rana guda. Yanzu kasar tana da mutum 92,472 da suka kamu - 70,065 na dauke da cutar a yanzu - 12,384 sun warke
A Birtaniya, mutum 260 sun mutu a rana guda, jumullarsu 1,019 kenan a yanzu
A Spain, mutum 832 ne suka rasu a rana guda, mutum 5,690 kenan jumulla da suka mutu. Sai dai lambar wadanda suke warkewa ma na kara girma, inda 12,285 daga cikin 72,000 suka warke
Shugaban Amurka Donald Trump ya fada wa 'yan jarida cewa yana tunanin saka dokar hana fita a Jihar New York da Connecticut da New Jersy
Sai dai Gwamnan New York Andrew Cuomo ya ce ba ma ya "son jin irin wannan zance baki daya" sannan ya ce bai ma san "me hakan yake nufi ba, ko zai iya yiwuwa a tsarin doka"
An bude birnin Wuhan na China, inda coronavirus ta fara bayyana, bayan kusan wata biyu ba shiga ba fita
Koriya ta Kudu ta ce mutanen da suka warke daga cutar sun fi wadanda suke kamuwa yawa a kasarta
Bankin GT ya bai wa Legas kyautar cibiyar killace masu coronavirus
Bankin Guarantee Trust (GT) ya damka wa gwamnatin Jihar Legas kyautar dakin killace masu cutar Covid-19 mai gado 110 a ranar Asaabar.
Ma'aikatar Lafiyar Jihar ce ta bayyana haka a shafinta na Twitter.
Legas ce cibiyar annobar coronavirus a Najeriya, inda a jihar ne mutum 59 cikin 89 da ke dauke da cutar a Najeriya suke.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Ga jerin jihohin da cutar ta bulla da kuma yawan mutanen da ta harba:
Legas - 59
Abuja - 14
Ogun - 3
Enugu - 2
Ekiti - 1
Oyo - 3
Edo - 2
Bauchi - 2
Osun -1
Rivers -1
Benue - 1
An fada wa Buhari hasashen wadanda ka iya harbuwa da coronavirus a Najeriya
Ministan Lafiya na Najeriya, Osagie Ehanire ya ce daga cikin abin da suka shaida wa Shugaba Muhammadu Buhari har da hasashen adadin wadanda za su iya harbuwa da coronavirus a Najeriya.
Ministan yana wannan batu ne jim kadan bayan sun fito daga tattaunawar da suka yi da shugaban kasar a ranar Asabar. Sai dai bai fadi adadin ba.
A ranar Alhamis ne Shugaba Buhari ya amince gwamnatin tarayya ta bai wa Jihar ta Legas tallafin naira biliyan 10 domin yaki da annobar, sannan a bai wa hukumar NCDC naira biliyan biyar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Labarai da dumi-dumi, Fiye da mutum 10,000 sun mutu a Italiya
Italiya ta sake fuskantar rana mafi muni, yayin da mutum 889 suka mutu a cikin awa 24.
Yanzu wadanda suka mutu a kasar sun kai 10,023 da kuma 92,472 da suka harbu da cutar ta coronavirus, sai kuma 12,384 da suka warke.
Coronavirus: An rufe coci a Abuja saboda keta doka
Hukumar babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja ta rufe wata coci a birnin a yau Asabar, bayan da jami'anta suka kai samame ana tsaka da taron addu'a.
An rufe cocin Christ Embassy da ke Jabi-Utako ne yayin da suke tsaka da addu'o'i da kuma daurin aure.
Tun a farkon makon nan ne hukumar FCTA ta bayar da sanarwar hana duk wasu taruka da suka hada da na sallar Juma'a da coci a yunkurin hana yaduwar coronavirus a birnin.
Zuwa yanzu mutum 14 ne aka tabbatar suna dauke da coronavirus a Abuja.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Wadanda suka kamu sun zarta 600,000 a duniya
Adadin wadanda suka kamu da coronavirus a duniya ya zarce 600,000, a cewar sabbin alkaluma.
A Nahiyar Turai, wadanda suka mutu sun wuce 20,000 - ita ma Jami'ar Johns Hopkins, wadda ke bin diddgin alkaluma kan annobar, haka ta bayyana.
Bayanan na zuwa ne kwana biyu bayan mutum sama da rabin miliyan sun kamu a fadin duniya.
Kasashe biyar da suka fi yawan adadin masu coronavirus:
Amurka - 104,865
Italya - 86,498
China - 81,996
Spain - 72,248
Jamus - 53,340
Labarai da dumi-dumi, Coronavirus: El-Rufai ya kama malamai biyu kan Sallar Juma'a
Asalin hoton, FACEBOOK/KADUNA STATE GOVERMENT
Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da kama wasu malamai biyu sakamakon bijirewa umarninta na hana Sallar Juma'a a jihar.
Tun a makon da ya gabata ne dai gwamnatin jihar ta dakatar da Sallar Juma'a da addu'o'in coci na ranar Lahadi da sauran taruka, a yunkurinta na dakile yaduwar coronavirus a jihar.
A wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya fitar, ya bayyana cewa malaman da aka kama sun hada da Malam Aminu Umar Usman da kuma Malam Umar Shangei wadanda aka kama a Malali da Unguwar Kanawa.
Ya bayyana cewa abin da malaman suka yi keta dokar jihar ne da kuma umarnin da manyan malamai suka bayar.
Labarai da dumi-dumi, Coronavirus: Karin mutum 8 sun kamu a Najeriya
Hukumar da ke yaki da yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta tabbatar da sabbin mutum bakwai da suka kamu da coronavirus a Legas sai kuma daya a Bauchi.
A halin yanzu mutum 89 ne aka tabbatar da sun kamu da cutar a fadin kasar inda tuni aka sallami mutum uku daya kuma ya mutu.
Ga jerin jihohin da cutar ta bulla da kuma yawan mutanen da cutar ta harba:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Bidiyo:Ganawar Buhari da hukumomin yaki da coronavirus a Najeriya
Ganawar Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya tare da Minsitan Lafiya Osagie Ehanire da kuma Chikwe Ihekweazu na NCDC a fadar Aso Villa da ke Abuja.
Mutum 81 ne hukumar NCDC mai yaki da cututtuka masu yaduwa ta tabbatar sun kamu da coronavirus a Najeriya - uku sun warke, daya ya mutu.
Bayanan bidiyo, Buhari ya gana da ministan lafiya kan coronavirus
Labarai da dumi-dumi, Wadanda coronavirus ta kashe a Birtaniya sun haura 1,000
Asalin hoton, Reuters
Yawan mutanen da suka mutu sakamakon coronavirus a Birtaniya sun kai 1,019.
Alkaluman baya-bayan nan da gwamnatin kasar ta fitar a ranar Asabar sun nuna cewa an kara samun mutum 260 da suka mutu, kari kan jumullar da ke da akwai a kasa ta mutum 759 da suka mutu a fadin kasar.
A yanzu haka akwai jumullar mutum 17,089 da aka tabbatar sun kamu da cutar a Birtaniyar.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin kasar ke ikirarin kara yawan gwajin cutar da take yi wa ma'aikatan lafiyar kasar musamman wadanda suka nuna alamun kamuwa da cutar da kuma wadanda suka yi tarayya da marasa lafiya.
Za a saki fursuna 1,540 a Nijar saboda coronavirus
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta ce za ta saki fursuna 15,40 daga gidan yari a yakin da take yi da yaduwar cutar Covid-19.
Adadin mutanen da suka kamu da coronavirus a kasar ya kai 18, uku daga ciki sun mutu.
Gwamnatin kasar ta kara karfafa matakan tsaro da suka hada da hana fita daga karfe 7:00 na yamma zuwa 6:00 na safe.
Har wa yau, gwamnati ta saka dokar hana shiga da fita a birnin Yamai na tsawon kwana bakwai, kumar dokar za ta fara aiki daga gobe Lahadi.
Kazalika, gwamnati za ta dauki karin ma'aikatan lafiya 1,500 duk a yunkurinta na hana yaduwar cutar.
Labarai da dumi-dumi, Coronavirus ta 'bulla' jihar Benue
Asalin hoton, Getty Images
An samu bullar coronavirus a jihar Benue da ke tsakiyar Najeriya.
Jaridar Daily Trust a kasar ta ruwaito cewa gwamnan jihar Samuel Ortom ya tabbatar da samun bullar cutar.
Sai dai har yanzu hukumar da ke yaki da yaduwar cututtuka ta kasar NCDC bata tabbatar da samun cutar ba a hukumance.
A halin yanzu akwai mutum 81 da suka kamu da cutar a Najeriya, inda tuni aka sallami uku sai kuma daya cutar ta yi ajalinsa.