BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
KAI TSAYE, A shirye muke mu ɗauki tsawon lokaci muna yaƙi - Iran
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 12 ga watan Agustan 2026.
Yadda aka yi bikin Ronaldo da amaryarsa Georgina a Portugal
Fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa Cristiano Ronaldo ya auri abokiyar zamansa ta shekaru da dama, Georgina Rodríguez, wadda ta yi suna a matsayin abin koyi da kuma mai tasiri a shafukan sada zumunta, a wani bikin auren kotu da aka gudanar a Portugal.
Dabaru 3 na samun aiki mai maiƙo ba tare da alfarma ba
Tun bayan da labaran wasu ƴan biyu kuma ƴan gida ɗaya da suka samu aiki a kamfanin mai na Najeriya, NNPC ba tare da sani kowa ba ko kuma wani ya yi musu alfarma ba, ƴan Najeriya ke ta tofa albarkacin bakinsu tare da bayyana mamakinsu kan faruwar hakan.
Matakan soji uku da Amurka ta ɗauka waɗanda suka girgiza duniya
A tsawon shekaru Amurka ta jagoranci wasu matakan soji da suka kai ga kamawa da kisan jagororin wasu ƙungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi da kuma shugabannin ƙasashen da ake zargi da aikata miyagun laifuka.
Manyan dazukan Najeriya 6 da suka zama mafakar ƴanbindiga
Yayin da gwamnati da hukumomin tsaro ke ƙara ƙaimi wajen fatattakar masu aikata laifuka daga irin waɗannan wurare, har yanzu akwai wasu dazuka da ke ci gaba da zama sanannun mafaka ga ƙungiyoyin ƴanbindiga da sauran masu ɗauke da makamai.
Dalilan da suka sa na nace kan takarar Muslim-Muslim - Sheikh Jingir
Shugaban majalisar malamai ta ƙungiyar Izala, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya yi ƙarin haske kan matsayinsa da kalaman da ya yi game da tikitin takarar Musulmi da Musulmi.
G-100: Sabuwar haɗakar da ke da nufin kawar da Tinubu daga mulki
A baya-bayan nan yunƙurin da ƴan hamayya suka yi na haɗewa a jam'iyya ɗaya domin tunkarar babban zaɓen 2027 ya ci tura, inda ba tare da daɗewa ba suka sake tarwatsewa zuwa cikin wasu jam'iyyun daban-daban.
Yadda aka ɓoye Trump a akwatin abincin jirgin sama saboda tsoron Iran
Kafafen yada labaran Amurka sun ce an dauke shugaban Amurka daga tsohon Air Force One zuwa jirgin soja yayin da yake barin taron kungiyar tsaro ta NATO a Turkiyya a watan da ya gabata.
An yanke wa tsohon shugaban Syria Bashar al-Assad hukuncin kisa
Wannan shi ne hukunci na farko da aka yanke wa Assad, wanda ya tsere daga Damascus zuwa Moscow tare da iyalansa bayan an hamɓarar da gwamnatinsa a watan Disamban 2024.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Yamma, 19:29, 12 Agusta 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Rana, 13:59, 12 Agusta 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 12 Agusta 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Safe, 05:29, 12 Agusta 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Wasanni
KAI TSAYE, Ba ni da tabbas kan ci gaba da ƙwallon ƙafa - Messi
Wannan shafi ne da ke kawo muku Labaran wasannin BBC Hausa na ranakun 10 - 16 Agusta 2026.
Man Utd na son Endrick, Napoli na harin Gabriel Jesus
Coventry City na son karɓo aron ɗanwasan gaba na Chelsea Mykhaylo Mudryk, Barcelona za ta ci gaba da farautar ɗanwasan tsakiya na Manchester City Rodri yayin da Manchester United ke son ɗauko ɗanwasan gaba na Real Madrid Endrick.
Man City ta kusa mallakar Bouaddi, Madrid na son Zubimendi
Manchester City na dab da ɗaukar Ayyoub Bouaddi, Real Madrid na son Martin Zubimendi, yayin da Barcelona da Tottenham ke bibiyar Harry Kane.
Ko Najeriya na da damar zuwa Gasar Kofin Duniya ta mata bayan shan kashi?
Shan kashi da Najeriya ta yi a hannun tawagar mata ta Kamaru ya ɗasa shakku kan damar da Najeriyar ke da ita ta zuwa Gasar Kofin Duniya ta Mata da za a yi a 2027 a ƙasar Brazil.
Aston Villa da Roma na son Endrick, Arsenal na tuntuɓar Barcola
Aston Villa na son aron Endrick, yayin da Harry Kane ke shirin tsawaita kwantiraginsa a Munich, ita kuwa Arsenal ta fara tuntuɓar Barcola.
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Hanyoyi uku da Amurka za ta iya tsoma baki a zaɓen Najeriya
A wasu lokuta, jami'an Amurka kan bayyana matsayarsu kan zaɓen wata ƙasa, su yi kira ga gwamnati da ƴan siyasa su mutunta dimokuraɗiyya, ko kuma su yi amfani da takunkumi kan waɗanda ake zargi da take haƙƙin ɗan'Adam ko lalata tsarin zaɓe.
Auren gata a Kano: Ƙalubalen da ake fuskanta wajen tantance masoyan gaskiya da na bogi
Tsawon kwanaki, titunan birnin sun cika da hayaniyar shagulgula, inda amare da danginsu ke shirya kayayyakin aure tare da halartar wasu tarurruka da shirye-shirye da aka tanada musu.
Rundunar ƴansanda ta tabbatar da kashe jami'anta 10 a artabu da ƴanbindiga a Kebbi
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 11 ga watan Agustan 2026.
Yadda ake haihuwar yaran da 'ba su da asali' a Sudan
Jariran da aka haifa sakamakon fyaɗe ba sa samun takardar shaidar haihuwa, wanda ke nufin suna cikin matsaloli na rayuwa.
Trump ya bukaci Iran ta biya diyyar sojojin Amurka da fararen hular da ta kashe
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 10 ga watan Agustan 2026
Da gaske ne Sarki Sanusi ya faɗi darussa a jami'a? Ga abin da BBC ta gano
BBC ta bincika gaskiyar abin da ya faru, har aka ga tawagar Sarkin a ƙofar shiga wani ɗakin taro a tsangayar koyon aikin shari'a ta jami'ar.
Wane ne Mohsen Rezaei sabon shugaban majalisar tsaron Iran?
Sabon shugaban zai taka muhimmiyar rawa wajen tsara yadda Iran za ta tafiyar da rikicinta da Amurka da kuma Isra'ila.
Me Sheikh Jingir ya ce kan takarar Muslim-Muslim da ya janyo masa suka?
A ƙarshen makon nan ne kafar sada zumunta da ma kafafen yada labarai suka ɗauki ɗimi da musayar yawu da cece-kuce kan kalaman da shugaban majalisar malamai ta ƙungiyar Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi dangane da takarar Muslim-Muslim.
Abianosa de Muñoz: Ƙauye a ƙasar Spain da za a yi dare biyu a rana ɗaya
Ƙauyen Abianosa de Muñoz na ƙasar Spain na shirin fuskantar wani dare na musamman, duk da cewa a yanzu kusan babu mazauna a ƙauyen.
'Lalurar al'aurata da ba na jin kunyar bayyana ta'
A duniya baki ɗaya, ƙiyasin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da aka fitar a shekarar 2024 ya nuna cewa kusan mutum miliyan 846 masu shekaru tsakanin 15 da 49 na ɗauke da cutar ƙurajen ala'aura da ake ɗauka da hanyar jima'ia.
Yadda za ku gane naman mushe in kun gan shi a kasuwa
Mahaucin ya ƙara da cewa da zarar an buɗe nama, gogaggen mahauci da ya gani zai gane cewa dabbar ta mutu.
Nawa sojan Najeriya da ke bakin daga zai riƙa karɓa a wata?
Sai dai bayan albashin sojojin, akwai alawus-alawus da ake biyan sojoji a ɓangarori da dama na aikin.
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.






























































