KAI TSAYE, Labaran wasannin BBC Hausa na 10 - 16 Agusta 2026
Wannan shafi ne da ke kawo muku Labaran wasannin BBC Hausa na ranakun 10 - 16 Agusta 2026.
Rahoto kai-tsaye
Muhammad Buhari Fagge
Fulham ta Shea Charles daga Southampton £30m
Asalin hoton, Getty Images
Fulham ta amince da yarjejeniyar sayen Shea Charles kan fam miliyan 30.
Kungiyar Fulham ta cimma yarjejeniya da za ta kai darajar fam miliyan 30 domin daukar dan wasan tsakiya na Southampton, Shea Charles.
Idan ya wuce gwajin lafiya, dan wasan mai shekaru 22 zai koma Craven Cottage kan kwantiragin shekara biyar, kuma zai zama dan wasan Arewacin Ireland mafi tsada a tarihi.
Charles, wanda ya fara kwallonsa a Manchester City, ya kuma ja hankalin Leeds United, amma ya zabi komawa yammacin Landan domin maye gurbin Sasa Lukic, wanda ya koma Ipswich Town a makon da ya gabata.
Zai zama dan wasa na uku da Fulham ta dauka tun bayan nada sabon koci Alvaro Arbeloa, wanda ya jagoranci Real Madrid na rikon kwarya a ƙarshen kakar wasan da ta gabata.
Zuƙowar Arbeloa bayan tafiyar Marco Silva zuwa Benfica, ya sa Fulham ta dauki 'yan wasa biyu daga Real Madrid, wato ɗan gaba Gonzalo Garcia da ɗan wasan tsakiya Cesar Palacios, kafin yanzu ta kammala yarjejeniyar Shea Charles.
A karon farko Delap ya ci wa Chelsea kwallo tun Janairu
Asalin hoton, Getty Images
Liam Delap ya ci wa Chelsea kwallayensa na farko tun watan Janairu yayin da ƙungiyar Xabi Alonso ta tashi kunnen doki da Johor Darul Ta'zim a wasan ƙarshe na share fagen fara kakar wasa da suka yi.
Saboda suna da wasanni biyu a jere cikin kwanaki biyu, Alonso ya fitar da wata sabuwar tawaga gaba ɗaya daban da wadda ta doke AC Milan da ci 3-0 a Jakarta ranar Asabar.
Delap, wanda ya koma Stamford Bridge daga Ipswich a shekarar 2025, ya ci kwallaye biyu kacal a wasanni 41 da ya buga a dukkan gasa a kakar wasan da ta gabata.
Dan wasan mai shekaru 23 ya daidaita wannan adadi a wasan da suka buga da ƙungiyar Malaysia, inda ya ci duka kwallayen biyu daga bugun fenariti.
Fenaritin da dan wasan ya ci guda biyu ne suka bai wa Chelsea damar shiga gaba a wasan bayan da Arif Aiman ya fara zura wa masu masaukin baki kwallo tun a farkon wasan.
'Har yanzu Najeriya na da sauran dama'
Asalin hoton, Getty Images
Mai tsaron ragar Najeriya, Chiamaka Nnadozie, ta ce dole ne Najeriya ta “koma ta sake karatn ta nutsu” bayan ta kasa samun gurbin shiga gasar Kofin Duniya ta Mata ta FIFA 2027 da za a yi a Brazil.
Tawagar Super Falcons ta gaza kaiwa wasan kusa da na ƙarshe na gasar Kofin Nahiyar Afirka ta Mata WAFCON 2026 da ake yi a Morocco, bayan ta sha kashi da ci 1-0 a hannun Kamaru a wasan daf da na kusa da na ƙarshe ranar Lahadi.
Kamaru da ta kai wasan kusa da daf da na karshe, ya tabbata ta samun tikitin shiga Kofin Duniya mai zuwa da za a yi a Brazil tare da sauran ƙungiyoyin da suka kai wannan mataki: Aljeriya, Malawi da Morocco.
Wannan na nufin cewa Najeriya, wadda ita ce zakarar WAFCON ta bara, yanzu za ta fafata da Afirka ta Kudu a wasan neman gurbi ranar Alhamis domin samun damar shiga gasar neman cancantar shiga Kofin Duniya, wanda zai iya ba ta wata dama ta kaiwa babban taron kwallon ƙafa na duniya.
“Wannan ƙwallon ƙafa ce, wannan rayuwa ce,” in ji Nnadozie yayin da take magana da BBC World Service.
“Abin da ya faru ya riga ya faru. Dole mu ci gaba da ɗaga kawunanmu sama muna alfahari. Har yanzu akwai sauran sa rai, ba a gama komai ba.”
Najeriya ta halarci dukkan gasar Kofin Duniya ta Mata tara da aka yi a baya, tun daga gasar farko da aka gudanar a China a shekarar 1991.
Super Falcons ta kai wasan kwata-fainal a shekarar 1999, sannan ta kai zagayen ƙungiyoyi 16 na ƙarshe a gasanni biyu na baya-bayan nan.
Sai dai bayan rasa kambun WAFCON, tawagar Justin Madugu na buƙatar doke zakarun 2022, wato Afirka ta Kudu, domin ci gaba da kasancewa cikin fafutukar samun gurbi a gasar Kofin Duniya da aka faɗaɗa zuwa ƙungiyoyi 32.
Digne ya koma kungiyarsa ta farko PSG
Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan Faransa, Lucas Digne, ya kammala koma wa gwarzuwar zakarun nahiyar Turai, Paris Saint-Germain PSG daga Aston Villa.
Dan wasan bayan da ke buga bangaren hagu mai shekaru 33 ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru uku a filin wasa na Parc des Princes.
Digne, wanda ya koma Aston Villa daga Everton a shekarar 2022, ya shafe shekaru uku a PSG a farkon rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa.
Yanzu ya koma ƙungiyar bayan shafe shekaru takwas a Ingila, biyo bayan hukuncin kungiyar PSG na sharadin sakin dan wasan kan fam miliyan 8.5 da ke cikin kwantiraginsa.
Da yake magana bayan kammala cinikin, Digne ya ce “Ina matuƙar farin ciki da samun damar komawa Paris Saint-Germain bayan kyakkyawar gogewar da na samu a nan fiye da shekaru goma da suka wuce.
Ana sa ran Digne zai samar da karin zaɓi ga kucin kungiyar a matsayin ɗan bayan hagu, tare da ci gaba da fafatawa domin samun wuri da shi da Nuno Mendes.
Bafaranshe ya shiga ƙungiyar PSG wadda ta lashe gasar Zakarun Turai sau biyu a jere, inda ta fi kusa da nasarar baya-bayan nan bayan doke Arsenal da bugun fenariti a wasan ƙarshe na shekarar 2026.
Sai da na amince na maye gurbin Sir Alex a Man United - Mourinho
Asalin hoton, Getty Images
Bayan shekaru da dama na jita-jita, Jose Mourinho ya tabbatar da cewa ya amince ya maye gurbin Sir Alex Ferguson a Manchester United, kafin daga bisani ya sauya ra’ayi ya koma Chelsea.
Lokacin da Ferguson ya yi ritaya a shekarar 2013 bayan shekaru 26 a Old Trafford, ya ba da shawarar a naɗa David Moyes, wanda a lokacin shi ne kocin Everton, a matsayin magajinsa.
Wannan ne ya sa aka yi wa Moyes lakabi da “The Chosen One” wanda aka Zaɓa, har ma an rataye wani babban allo mai ɗauke da wannan suna a bangaren Stretford End na filin wasan kulob din.
Da yake magana a cikin wani sabon shirin tarihin rayuwarsa da za a fara nunawa a Netflix daga 11 ga Agusta, Mourinho ya ce:“Lokacin da na bar Real Madrid, na amince da zuwa Manchester United domin maye gurbin Sir Alex.”
Ferguson, wanda ya lashe Premier League 13 a matsayin kocin United, ya tabbatar da cewa an miƙa wa Mourinho aikin.
Ya ce: “Na zaunar da shi na yi masa bayanin halin da ake ciki. A ganina, ya amince da karɓi aikin. Amma cikin sa’o’i kaɗan komai ya sauya.”
Abin da ya sauya kuwa shi ne Mourinho ya ji cewa ba zai komawa Chelsea ba da aiki, inda a nan ne ya taba lashe kofunan Premier League a jere a shekarun 2005 da 2006.
Ferguson ya ƙara da cewa: “A wani dare ya kira ni yana kuka, sai ya ce, ‘Alex, ba zan iya karɓar aikin nan ba. Na riga na yi wa Chelsea alkawari kuma ba zan karya alkawarina ba.’
“Dalilin da ya ba ni na fahimta, amma duk da haka na ji ba dadi.”
Mourinho, mai shekaru 63, ya ce ya ji matuƙar karramawa da aka ba shi damar maye gurbin Ferguson saboda: “Manchester United ƙungiya ce mai matuƙar jan hankali.”
“Rashin damar zama kocin da zai gaji Sir Alex Ferguson abu ne mai raɗaɗi a gare ni, amma ban taɓa nadama ba domin shawara ce da na yanke a zuciyata.”
Bayan komawarsa Stamford Bridge a shekarar 2013, Mourinho ya lashe kofina uku na Premier League tare da Kofin League Cup.
A gefe guda kuma, an sallami David Moyes daga aikin bayan watanni goma kacal a matsayin kocin Manchester United.
Daga baya, Mourinho ya samu wata dama ta biyu ta jagorantar United a shekarar 2016, inda ya maye gurbin Louis van Gaal.
A tsawon shekaru biyu da rabi da ya yi a Old Trafford, Mourinho ya lashe League Cup da Europa League kafin a kore shi a watan Disamban 2018 biyo koma bayan sakamako da ƙungiyar ta samu.
Bruno Guimarães ya kammala komawa Arsenal
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, ,
Ko shakka babu, mafi girman cinikin sauya kungiya da aka yi a ƙarshen makon nan shi ne Arsenal da ta ɗauki Bruno Guimarães daga Newcastle kan kuɗi fam miliyan 75.
Dan wasan tsakiya na Brazil mai shekaru 28 ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru huɗu, tare da zaɓin ƙarin shekara guda, kuma ya bayyana wannan sauyin ƙungiya a matsayin ɗaya daga cikin “mafi wahalar hukunci” da ya taɓa yankewa a rayuwarsa.
Guimarães ya koma Newcastle ne a watan Janairun 2022 lokacin da ƙungiyar ke fuskantar barazanar faduwa daga gasar Firimiya.
Ya zama kyaftin na farko na Newcastle cikin shekaru saba’in da ya ɗaga wani babban kofin cikin gida, bayan da suka doke Liverpool a wasan ƙarshe na Kofin Carabao na shekarar 2025.
Barkanmu da rana
Masu bibiya barkanmu da wannan lokaci Muhammad Buhari Fagge ne ke fatan kasancewa da ku a wannan makon domin kawo labarai da rahotannin wasanni daga nan BBC.