Diflomasiyya kaɗai ba za ta kawo ƙarshen rikicin mashigar Hormuz ba - Iran

Asalin hoton, IRNA
Iran ta ce ba za a iya kawo ƙarshen rikicin da ke tattare da mashigar Hormuz ta hanyar diflomasiyya kaɗai ba, tana mai jaddada cewa dole ne a haɗa tattaunawa da amfani da ƙarfin ƙasa wajen kare muradunta.
Mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmail Baghaei, ya bayyana cewa diflomasiyya na taka muhimmiyar rawa wajen kare bukatun ƙasar, amma ba za ta wadatar ba muddin akwai abin da ya kira matsin lamba da takunkumin ruwa da Amurka ke amfani da shi.
A cewarsa, Iran na haɗa hanyoyin diflomasiyya da ƙarfin soja domin tunkarar ƙalubalen da take fuskanta, yana mai cewa wannan ne matakin da ƙasar ke ɗauka a halin yanzu.
Ya kuma ce duk da ci gaban tattaunawar Iran da Oman kan tsara hanyar zirga-zirga a mashigar Hormuz, hakan ba yana nufin za a sake buɗe mashigin gaba ɗaya ga zirga-zirgar jiragen ruwa ba.


























