Man City ta kusa mallakar Bouaddi, Madrid na son Zubimendi

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City na dab da kammala cinikin ɗan wasan tsakiyar Morocco, Ayyoub Bouaddi, mai shekara 18, daga Lille, wadda ta yi wa ɗan wasan kudi yuro miliyan 100, kwatankwacin fam miliyan 85. (Guardian)
Real Madrid na sha'awar ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Sifaniya wanda ya ci Kofin Duniya, Martin Zubimendi, mai shekara 25, daga zakarun Firemiya, Arsenal. (Football.London, external)
Ɗan wasan gaba na Brazil kuma na Arsenal, Gabriel Jesus, mai shekara 29, a shirye yake ya koma Napoli a wannan bazarar. (La Gazzetta dello Sport - in Italian)
Kungiyar AS Roma ta fara tattaunawa da wakilan ɗan wasan gefe na Brazil, Gabriel Martinelli, mai shekara 25, yayin da take nazarin yiwuwar ɗaukarsa daga Arsenal. (Mirror, external)
Barcelona da Tottenham Hotspur sun yi tattaunawa da Bayern Munich kan yiwuwar sayen ɗan wasan gaba na Ingila, Harry Kane, mai shekara 33, a wannan bazarar. (Teamtalk)
Manchester City na sane da sha'awar da Nottingham Forest ke nunawa ɗan wasanta na tsakiya daga Netherlands, Tijjani Reijnders, mai shekara 28, wanda ta saya daga AC Milan a bara. (Sky Sports)
Ɗan wasan gaba na Faransa kuma na Paris Saint-Germain, Bradley Barcola, mai shekara 23, ya amince da komawa Liverpool, duk da yunkurin da Arsenal ta yi a ƙarshe na kwace cinikin. (Sun)
Ɗan bayan Italiya na Inter Milan, Alessandro Bastoni, mai shekara 27, da kuma ɗan wasan tsakiyar Ingila na Crystal Palace, Adam Wharton, mai shekara 22, na ci gaba da kasancewa cikin jerin 'yan wasan da Real Madrid ke son saye a wannan bazarar. (Fichajes - in Spanish)
Ɗan wasan tsakiyar Denmark na Marseille, Pierre-Emile Hojbjerg, mai shekara 31, ya ƙi damar komawa Newcastle United. (Talksport)
Manchester United na nazarin yiwuwar ɗaukar ɗan bayan Jamus na RB Leipzig, David Raum, mai shekara 28, bayan ta gaza cimma yarjejeniya kan ɗan bayan hagu na Ingila, Lewis Hall, mai shekara 21, daga Newcastle United. (Teamtalk)












