Dabaru 3 na samun aiki mai maiƙo ba tare da alfarma ba

..

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanya ranar 12 ga watan Agustan kowace shekara ta zama ranar matasa, inda ake duba ƙalubalen da ke damun su da kuma hanyoyin warware matsalolin.

A ƙasashen Afirka irin su Najeriya, babbar matsalar da ta damun matasa ita ce ta rashin aikin yi a tsakanin miliyoyinsu.

Sai dai kuma tun bayan da labaran wasu ƴan biyu kuma ƴan gida ɗaya da suka samu aiki a kamfanin mai na Najeriya, NNPC ba tare da sani kowa ba ko kuma wani ya yi musu alfarma ba, ƴan Najeriya ke ta tofa albarkacin bakinsu tare da bayyana mamakinsu kan faruwar hakan.

Ana dai ganin hakan ba ya rasa nasaba da irin halin da ake ciki a Najeriya na wahalar samun aiki da kuma zarge-zargen rashawa da cin hanci da alfarma a lokutan ɗaukar aiki.

Hakan ya sa miliyoyin matasa a ƙasar ke yin ƙasa a gwiwa wajen neman aiki a wuraren da ake yi wa kallon masu tsoka ne saboda tunanin cewa wuri ne da aka tanadarwa ƴaƴan manya.

BBC ta tuntubi Malam Abdulƙadir Ibrahim wanda ke aiki a sashen ɗauka da gudanarwar ma'aikata a wata ma'aikata a Abuja domin bayar da shawarwari kan hanyoyin da ya kamata matasa su bi domin samun aiki ba tare da sanin wani ko wata ba a wuri.

Abdulƙadir Ibrahim ya lissafa dabaru guda biyar da ya ce duk mai neman aiki ya kamata ya bi sau da ƙafa domin samun aiki ba tare da sanin kowa ba.

1) Cancanta da ƙwarewa

..

Asalin hoton, Getty Images

Cancanta na nufin mai neman aiki ya dace da irin abubuwan da ake buƙata da ya jiɓanci irin karatun da masu daukar aikin ke neman. Misali mai digiri ɗaya ake buƙata ko mai digiri biyu ko kuma uku.

Sannan ana duba ajin digiri misali ana neman mai digiri mai daraja ta ɗaya ko ta biyu ko kuma ba a rarrabe ba.

"Shi kuma wannan yana farawa ne tun daga rayuwar jami'a. A nan ne mutum zai tabbatar da ya samu ajin digiri mai kyau."

Ƙwarewa: Wannan na nufin abin da mutum ya iya yi saboda ilimi, horo ko gogewar aiki da ya samu.

Cancanta da ƙwarewa sun sha banban duk da cewa suna da alaƙa. Yayin da cancanta ke nufin takardun shaida ko ilimin da mutum ya samu kamar digiri, difloma ko satifiket, ita kuma ƙwarewa na nufin abin da mutum zai iya yi a aikace.

Misalan ƙwarewa:

  • Sarrafa kwamfuta
  • Kwarewa a sarrafa AI
  • Rubutu

2) Inganta tarkardar neman aiki (CV)

..

Asalin hoton, Getty Images

Bayan mallakar dukkannin cancanta da ƙwarewa da ake buƙata a aikin da kake nema, abu na gaba shi ne tsara cancatar da ƙwarewar a cikin takardar neman aiki da ake kira da CV, wanda hakan ne zai ba ka damar tallata kanka har masu ɗaukar aikin su gayyace ka domin jarrabawar ɗaukar aiki.

"Yanzu ba kamar a shekarun baya ba ne dangane da abin da ya shafi takardar neman aiki da ake kira da "CV", inda ya siffanta abin da ake buƙata a takardar," in Abdulƙadir Ibrahim.

Abdulƙadir ya kuma zayyana wasu hanyoyi na gamsuwa da kyawun takardar ta CV.

  • Ya kasance a taƙaice
  • Mai tsari
  • Ya nuna ƙwarewarka da nasarorin da ka samu.
  • Ka daidaita CV ɗinka da aikin da kake nema ta hanyar fito da ƙwarewarka ta dace da aikin da ake nema.

3) Shiryawa domin jarrabawar ɗaukar aiki

..

Asalin hoton, Getty Images

Masanin ya ce dabara ta uku domin samun aiki ita ce shiri na musamman domin tunkarar ƙalubalen intabiyu kasancewar masu neman aiki da dama kan faɗi jarrabawar ɗaukar aiki ko da kuwa suna da cancanta sannan kuma takardar neman aikinsu ta CV ta yi kyau.

Shiryawa sosai domin tunkarar jarrabawar ɗaukar aiki na nufin mutum ya yi duk abin da zai taimaka masa ya amsa tambayoyi cikin ƙwarin gwiwa kuma ya nuna cewa shi ya fi dacewa da aikin.

Akwai kuma hanyoyin shiryawa kamar haka:

Ka binciki kamfanin

  • Ka san abin da kamfanin yake yi.
  • Ka san manufofinsa da ayyukansa.
  • Ka fahimci aikin da kake nema.

Ka sake karanta CV ɗinka

  • Ka tabbatar ka san duk abin da ka rubuta.
  • Ka shirya bayanin ƙwarewarka da gogewarka.

Ka yi atisayen amsa tambayoyi

Misali:

  • Ka faɗa mana game da kanka.
  • Me ya sa kake son wannan aikin?
  • Mene ne ƙarfinka da rauninka?
  • Ta yaya ka taɓa magance wata matsala a wurin aiki?

Ka tanadi misalai daga gogewarka

  • Maimakon ka ce "Ina da ƙwarewar jagoranci", ka kawo misalin lokacin da ka jagoranci wani aiki kuma aka samu nasara.

Ka kasance da ƙwarin gwiwa

  • Ka rinƙa magana a sarari.
  • Ka kalli masu tambayoyi idan kana ganawa da su kai tsaye.
  • Ka nuna ladabi da girmamawa.
Ko ana alfarma a ɗaukar aiki?
..

Asalin hoton, Getty Images

"E gaskiya ba za a ce ba a yi ba amma kuma ko da za a yi alfarma to sai an tabbata mutum na da dukkan cancanta da ƙwarewar da kamfani ke buƙata.

Misali, mai neman aiki A na da cancanta da ƙwarewa sannan shi ma mai neman aiki B yana da irinsu sak. To idan mai neman aiki B ya san wasu a wurin to zai iya samun alfarma ta sanayya," in ji Abdulƙadir Ibrahim.

Saidai kuma Abdulƙadir Ibrahim ya ce alfarmar da ake yi a kamfanoni masu zaman kansu ta banbanta da irin wadda ake yi a ma'aikatun gwamnati.

"A gwamnati za a iya ɗaukar wanda ba shi da cancanta da ƙwarewa a bar wanda yake da su. Sannan ma wasu lokutan ma ƴan siyasa ke kai mutanensu wurin ko da ba su cancanta ba."