Shin Kannywood na fina-finai game da matsalolin arewacin Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja.
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 3
Kannywood na ɗaya daga cikin manyan masana'antun shirya fina-finai a Afirka, musamman a Arewacin Najeriya.
Tun bayan kafuwarta, masana'antar ta taka muhimmiyar rawa wajen nishaɗantar da al'umma tare da isar da saƙonni kan al'adu, addini, zamantakewa, da ɗabi'u.
Arewacin Najeriya na fuskantar matsaloli da dama da suka shafi zamantakewa da ci gaba, kamar rashin tsaro, talauci, rashin aikin yi, ƙarancin ilimi, matsalolin kiwon lafiya, shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da sauransu.
Waɗannan matsaloli na ci gaba da shafar rayuwar al'umma ta fannoni daban-daban, lamarin da ya sa ake buƙatar hanyoyi masu inganci na wayar da kai da ƙarfafa tattaunawa a kansu.
Fina-finan Hausa da saƙonni
Fina-finai na daga cikin muhimman hanyoyin sadarwa da ke iya bayyana waɗannan matsaloli tare da nuna musabbabinsu, illolinsu, da hanyoyin magance su.
Wannan ya sa ake tunani tare da kallon Kannywood a matsayin wata hanya da za a yi amfani da ita wajen haskaka matsalolin da suka fi addabar al'ummar Arewa, tare da ƙarfafa masu kallo su yi tunani da ɗaukar matakan da suka dace.
Sai dai akwai muhawara kan ko Kannywood na mayar da isasshen hankali ga irin waɗannan matsaloli ko kuwa ta fi karkata ga jigogin soyayya da aure. Wannan ya haifar da tambayoyi game da irin gudummawar da masana'antar ke bayarwa wajen tattauna muhimman batutuwan ci gaban al'umma da kuma tasirin fina-finanta wajen samar da sauyi.
A ɗaya ɓangaren kuma, masana'antar ta daɗe tana fama da matsalolin rashin kasuwanci da rashin tabbas, musamman a harkokin kasuwancinta da kuma ciyar da ita.
Masu ruwa da tsaki a masana'antar - waɗanda su ne suke riƙe masana'antar - yawanci da kuɗinsu suke amfani, wanda hakan ya sa dole suke fara tunanin mayar da kuɗinsu da cin riba.
Amma duk da haka waɗanne jigo ne ya fi yawa a masana'antar? sannan shin tana da rawar takawa wajen magance wasu daga cikin matsalolin arewacin Najeriya, inda yawancin ƴaƴanta suka fito?
'Suna ƙoƙartawa, amma...'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dr Muhsin Ibrahim, malami ne a Jami'ar Cologne da ke Jamus ya ce tambayar ko masana'antar tana taimakawa wajen magance matsalolin da arewacin Najeriya ke fuskanta tambaya ce wai wahalar amsawa.
"A kimiyyance, wannan tambaya ce mai wahala amsawa. Na farko, sai mun san mene ne ya lalace. Sannan sai mun yi bincike, kafin mu iya sanin ya gyaru ko a'a, sannan mu ƙara binciken alaƙar gyaran ta Kannywood," in ji shi.
Sai dai Mushin, wanda fitaccen mai sharhi kan harkokin Kannywood ne ya ce masana'antar na ƙoƙari wajen kawo maudu'an da suke damun masu kallonta.
Ya ƙara da cewa, "Ba duk matsalar da take a Amurka ko Jamus ce matsalar masu kallon Kannywood ba."
Da ake tambaye shi game da rawar da masana'antar ke takawa wajen magance matsalolin rashin kiwon mai lafiya mai inganci da ili da taɓarɓarewar tarbiya da suke damun yankin, sai akwai fina-finan da aka ƙoƙarta.
"Game da inganta kiwon lafiya, an nuna haka sosai a 'Garwashi'. Na ga tallar wani fim daga kamfanin Abnur Entertainment mai suna 'Burin Zuciya'. Yana magana ne kan aure tsakanin masu ɗauke da ciwon sikila duk da kuwa an musu kashedi game da hakan. Don haka suna ɗan taɓawa a hankali a hankali," in ji Muhsin.
Ya ƙara da cewa masu shirya fina-finan suna ɗan ƙoƙari wajen irin waɗannan finafinan da kake faɗa.
"Ka ga kamar fim ɗin 'Ruwan Dare'; ka ga yana magana ne a kan ilimi. Za ka iya alaƙanta shi da neman ilimi. Akwai 'Ɗan Birni' na Fulalu, shi kuma yana magana ne a kan noma. Akwai misalai kaɗan-kaɗan."
A game da irin ƙoƙarin da suke yi idan aka kwatanta da matsalolin yankin, Dr Muhsin ya ce "tabbas ba sa mayar da hankali sosai kan irin waɗannan matsaloli, wanda kuma mayar da hankali a kansu zai yi matuƙar tasiri kan masu kallonsu, wato Hausawa."
A wata tattaunawarsa da BBC a game da fim ɗin 'Gida Badamasi', Falalu Ɗorayi ya ce ganin yadda Najeriya take a ciki a yanzu, "akwai buƙatar fina-finai masu nishaɗantarwa cikin barkwaci.
"Kuma shirin Gidan Badamasi na taka rawa a wannan fagen wajen ɗebe kewa da saka farin ciki a zukatan mutane."
Sai dai daraktan ya ce baya ga barkwanci, shirin zai taɓo matsalolin da al'umma ke fama da su a arewacin Najeriya kamar garkuwa da mutane.
"Yanzu kusan matsalar tsaro ce ta fi damun ƴan Najeriya, don haka ne muka shigo da batun garkuwa da mutane, inda ake garkuwa da Alhaji Badamasi duk tsananin son kuɗinsa," in ji shi.
Falalu ya ce sai da suka gudanar da bincike sosai kan yadda ake yi idan an yi garkuwa da mutane, "domin mu isar da saƙon cikin hikima da basira," in ji shi.
"Mun yi fashin baƙi sosai kan garkuwa da mutane bayan bincike da nazarin da muka yi. Sannan mun fito da wani abu kan batun ƙabilanci a harkar, da ma fito da abin da ya kamata a yi idan an kama mutum da ma hanyoyin magance matsalolin tsaro."












