NiMet ta yi gargaɗin ambaliya a Sokoto, Kaduna, Neja da wasu jihohi 10 a watan Agusta

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi gargaɗin yiwuwar aukuwar ambaliyar ruwa a jihohi 13 tsakanin ranar 11 da 20 ga watan Agustan 2026.
Jihohin da ta ce ke fuskantar barazanar sun haɗa da Sokoto, Zamfara, Kebbi, Neja, Kaduna, Nasarawa, Adamawa, Filato, Benue, Kogi, Taraba, Cross River da Akwa Ibom.
Hukumar ta ce hasashen ya samo asali ne daga nazarin yawan ruwan sama da ake sa ran samu, yanayin danshin ƙasa, ƙarfin magudanan ruwa, yanayin ƙasa da kuma yanayin madatsun ruwa.
Ta yi gargaɗin cewa ambaliyar ka iya shafar yankunan da ke fama da ambaliya, ƙananan wurare, birane da kuma al'ummomin da ke kusa da koguna, lamarin da zai iya haddasa rufe hanyoyi da tsaikon sufuri.
NiMet ta kuma ce ambaliyar na iya lalata gonaki, amfanin gona da dabbobi tare da shafar wutar lantarki da hanyoyin sadarwa.
Hukumar ta shawarci jama'a su riƙa bibiyar hasashen yanayi da gargaɗin ambaliya, su guji wucewa ta hanyoyin da ruwa ya mamaye, yayin da ta buƙaci hukumomin agajin gaggawa da manoma su ɗauki matakan kariya domin rage illolin da ka iya tasowa.


















