Da gaske ne Sarki Sanusi ya faɗi darussa a jami'a? Ga abin da BBC ta gano

 Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, wanda kuma tsohon shugaban Babban Bankin Najeriya ne ya koma makaranta, inda ya fara karatun digiri na farko a fannin shari'a a jami'a mallakin jihar Kano.
Bayanan hoto, Sarautar Sarkin Kano na daga cikin mafiya daraja, wadda kuma ake girmamawa a ƙasar Hausa da kuma fadin Najeriya.
    • Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Wani faifan bidiyo ya karaɗe shafukan sada zumunta, inda aka ga wani matashi na iƙirarin cewa tawagar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ta isa harabar jami'ar da sarkin ke karatu domin "sulhuntawa" saboda an ba Sarkin "Carry Over".

An yaɗa bidiyon sosai a shafukan sada zumunta da dama, inda aka yi ta muhawara kan dalilin da zai sa Sarkin ya faɗi darasi cikin darussan da yake ɗauka.

An ji matashin a cikin gajeren bidiyon mai tsawon daƙiƙa 26 yana cewa: "Kamar yadda kuke gani, sarki aka ba carry over, shi ne ya zo da ƴan kombarsa, za a zo a sulhunta... Hattara lecturers."

Mai martaban dai ya koma Jami'ar Northwest da ke Kano domin karantar ilimin shari'a, inda ya fara karatunsa a farkon shekarar nan daga aji na biyu.

Dama tun bayan komawarsa, al'umma sun yi ta mamakin yadda zai ɗauki karatu a wata jami'a da ke cikin jihar Kano, watanni bayan kammala digirinsa na digirgir daga wata jami'a a birnin Landan na Birtaniya.

BBC ta binciki gaskiyar abin da ya faru, har aka ga tawagar Sarkin a ƙofar shiga wani ɗakin taro a tsangayar koyon aikin shari'a ta jami'ar.

Da gaske ne an ba Sarki Sanusi 'Carry Over' a jami'a?

Asalin hoton, ABBA BLOGGER/FB

Abin da ya sa Sarki Sanusi ya koma jami'a

Ba Najeriya kawai ba, Sanusi II, wanda shi ne Khalifan mabiya ɗariƙar Tijjaniya a ƙasar na da ɗimbin tasiri a ƙasashe maƙwafta, musamman na yammacin nahiyar Afirka.

Duk waɗannan na daga cikin abin da ya sa wasu ke ganin basaraken ya yi ƙasaitar da ta wuce ya shiga cikin ɗalibai masu ƙarancin shekaru domin yin karatun digiri na farko.

Sai dai a wata tattaunawarsa da BBC bayan kammala ɗaukar karatu a jami'ar ta Northwest University da ke birnin Kano a cikin watan Janairu, Muhammadu Sanusi II ya ce ya daɗe yana sha'awar karanta harkar shari'a.

Sarkin ya bayyana cewa duk da cewa ya riga ya samu digirin-digirgir (PhD) har yanzu yana da sha'awar yin karatun lauya.

Abin da BBC ta gano

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bayanan da BBC ta samu sun nuna cewa a lokacin da bidiyon ya yaɗu, ba a fara rubuta jarabawar ajin da Sarki Sanusi yake ba.

Majiyar ta shaida wa BBC cewa a wannan Talata - 10 ga watan Agusta - ne za a fara rubuta jarabawar, kuma har zuwa lokacin, Sarkin bai rubuta jarabawa ko ɗaya ba.

Kamar yadda aka gani a bidiyon da ya yaɗu sosai, dandazon jama'ar da ke tare da tawagar Sarkin sun yi masa rakiya ne a lokacin da ya je makarantar a matsayinsa na ɗalibi, "abin da ya sa aka ga taron jama'a da yawa."

An ce an ɗauki bidiyon ne a wani taron da ɗaliban Shari'a na jami'ar suka shirya ranar Asabar.

Sai dai, a cewar majiyar, ba wani abin damuwa ba ne ma ko da a ce Sarkin ya faɗi wani darasi a matsayinsa na ɗalibi.

"Idan ma ya samu 'carry over', ai ba wani abin damuwa ba ne."

Bayanan da BBC ta samu sun nuna cewa, babu wanda ke da damar ganin sakamakon jarabawar wani ɗalibi saboda "ana tura wa kowa sakamakonsa ta adireshin imel ne".

Hakan na nuna cewa babu yadda wani zai ga sakamakon da wani ya samu idan ba sun tattauna ba, tun da ba a wallafa shi a allon sanarwa kamar yadda matashin ya yi iƙirari.

"Tun muna aji ɗaya ba a taɓa wallafa sakamakon jarabawarmu a allon bayani ba," in ji wani ɗalibin nazarin shari'a da ke aji ɗaya da sarkin.

Wasu daga cikin ɗaliban da ke karatu tare da sarkin sun sake tabbatar da cewa Sarki Sanusi bai faɗi wata jarabawa ba.

A bayanan jadawalin rubuta jarabawar da BBC ta samu, Sarkin zai fara rubuta jarabarawarsa ta farko a wannan zangon karatu ne a ranar Talata saboda "wasu kwasa-kwasan da yake ɗauka sun sha bamban da na wasu a ajin".

Abin da masarautar Kano ta ce

Masarautar Kano ma ta yi watsi da bidiyon da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, inda a wata sanarwa da sakataren ofishin Sarkin, Muhammad Ado ya fitar, ya ce zargin da ke cikin bidiyon ba gaskiya ba ne, inda ya ce Sarkin yana kan hanyar kammala karatunsa da matakin farko wato 'First Class'.

Ya ce an ɗauki bidiyon ne a wani taro da ɗaliban Shari'a na jami'ar suka shirya ranar Asabar.

"Mun halarci wani taro da ɗaliban Shari'a na jami'ar suka shirya ranar Asabar, kuma wani ɗalibi ne ya ɗauki bidiyon. Amma ba gaskiya ba ne.

An danganta bidiyon da wasu matasa da ake zargin sun ɗauke shi tare da yaɗa shi a matsayin wasa.

ABBA BLOGGER/FB

Asalin hoton, ABBA BLOGGER/FB

Tarihin Muhammadu Sanusi II

An haifi Muhammadu Sanusi II a jihar Kano da ke arewacin Najeriya a ranar 31 ga watan Yuli a shekarar 1961.

Sanusi II ya yi karatun firamare ne a makarantae St. Annes da ke Kaduna, sannan ya koma King's College da ke Legas, inda ya yi sakandare tsakanin 1973 zuwa 1977.

Ya samu digirinsa na farko a fannin tsimi da tanadi a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya a 1981, sannan ya yi digiri na biyu a shekarar 1983, inda ya koyar da wani ɗan lokaci.

Ya koma Jami'ar Khartoum da ke Sudan, inda ya karanci nazarin addinin musulunci.

Bayan ya koyar da tsimi da tanadi tsawon shekara biyu a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, sai ya soma aikin banki a shekarar 1985 tare da Icon Limited, daga bisani kuma yai aiki tare da bankin UBA da kuma First Bank.

Ya kai matsayin Babban Darakta a bankin First bank a watan Janairun shekarar 2009, daga bisani kuma aka naɗa shi gwamnan babban bankin Najeriya na 10 a watan Yunin shekarar 2009.

Sanusi II ya yi karatun digirinsa na uku wato PhD a ɓangaren shari'a a London, inda ya yi nazari a kan "Codification of Islamic Family Law as an Instrument of Social Reform: A Case Study of the Emirate of Kano and a Comparison with the Kingdom of Morocco."

A zamanin Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, shugaban ya dakatar da shi daga matsayin gwamnan Babban Bankin Najeriya a ranar 20 ga watan Fabrairun shekarar 2014 bayan da aka zarge shi da sakaci wajen harkar kuɗi.

Mahaifinsa Muhammadu Lamido Sanusi ya riƙe muƙamin babban sakatare a ma'aikatar harkokin ƙasashen wajen Najeriya, bayan ya riƙe mukamin Jakadan Najeriya a ƙasashen Canada da Belgium da China.

Kuma jika ne ga Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na ɗaya.