Dalilan da suka sa na nace kan takarar Muslim-Muslim - Sheikh Jingir

Shugaban majalisar malamai ta ƙungiyar Izala, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya yi ƙarin haske kan matsayinsa da kalaman da ya yi game da tikitin takarar shugabancin Najeriya da zai zama na Musulmi da Musulmi a matsayin shugaban kasa da mataimakinsa.
A hirarsa da BBC, shehin malamin ya ce ya daɗe yana goyon bayan hakan tun kafin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A ƙarshen makon nan ne kalaman da shugaban majalisar malaman ta ƙungiyar Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi dangane da takarar Muslim-Muslim suka haifar da zazzafar muhawara musamman a arewacin kasar.
Yayin wani jawabi ranar Asabar a Kano a lokacin walimar bikin auren gata da gwamnatin Kano ta shirya ga ma'aurata 1,500 da ta ɗauki nauyin aurensu a faɗin jihar, Sheikh Jingir ya ce bai taɓa da-na-sanin zaɓen Musulmai a matsayin shugaba da mataimakinsa ba.
A tattaunawarsa da BBC a yammacin ranar Talata, Sheikh Jingir ya ce goyon bayansa ga tikitin Musulmi da Musulmi bai taƙaita ga Shugaba Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima ba kuma dama ya yi tsammanin zai sha suka lokacin da ya yi kalaman.
Sheikh Jingir ya ce duk wani ɗan siyasar da ya yi imani da irin ra'ayinsa kan abin da ya kira "wahalhalun da Musulmi" a Najeriya suka fuskanta, zai goya masa baya.
"Ni ba Tinubu nake tallatawa ba, Musulunci nake tallatawa... Ni musulunci na ba ta Tinubu ba ce... to wannan ita ce ribar tawa".
Malamin ya ƙara da cewa bai ga dalilin da zai sa Kiristocin Najeriya su yi kira ga mabiyansu su zaɓi ɗan takarar da suka yi imani da shi, amma shi kuma a ce ba shi da damar bayyana wa Musulmi wanda ya kamata su zaɓa ba.
Ya ce kalamansa ba za su tunzura kowa ba kamar yadda ake yaɗawa, saboda ya ba kowa shawarar abin da zai yi kuma kowa yana da ra'ayinshi.
"Ina da ƴancin in ce a zaɓi musulmi, in ce a yi Musulunci."
Ya ce yana da damar bai wa Musulman Najeriya shawara kan yadda za su yi amfani da haƙƙinsu na zaɓe, kuma matsayinsa kan tikitin Musulmi da Musulmi tsohon ra'ayi ne da ya daɗe yana da shi.
Sheikh Jingir ya ƙara da cewa abin da ya sa yake ci gaba da magana kan Shugaba Tinubu da kuma kira ga goyon bayan tikitin shi ne, matakin da shugaban ya ɗauka na tsayawa takarar shugaban ƙasa tare da abokin takararsa Musulmi.
Sheikh Jingir ya ce ya nace kan wannan batu ne saboda yadda ya zo a addini cewa "musulmi ɗan'uwan musulmi ne".
Malamin ya ce yana da hujjojin kan matsayarsa a yake ganin ya kamata a mara masa baya kan ra'ayinsu.
Ya ce saboda Allah ya hore masa jama'ar da zai ja hankalinsu, shi ya a yake faɗakar da jama'a cewa siyasar da ake yi addini ce, dalilin da ya sa yake amfani da mimbarinsa wajen faɗan abin ya yarda gaskiya ne.
"In dai mutum ya san gaskiya yake faɗa, to duk wani zage-zage da surutu kar ya yi shiru, ya yi ta nanatawa... shi ya sa nake ta nanatawa".
Malamin ya ce dama ya san zai sha suka kan matsayarsa shi ya sa bai damu da abin da ake ta faɗa ba, shi dai burinsa ya faɗi gaskiya.
"Ko ƙyaras ban damu ba."
"Wannan abin da kuka ji manufata kenan, kuma ba na nadama, kuma ba ranar farawa...kira kan musulunci,"
Ya ce shi yana kare shugaba musulmi mai nagarta ne ba tare da la'akari da wanda ke kan mulki ba.
Wane ne Sheikh Yahaya Jingir?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Yahaya Jingir daya ne daga cikin manyan malaman addinin Musulunci da suka yi shuhura a Najeriya.
Malamin mazaunin Jos a jihar Filato, shi ne shugaban majalisar malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah wa Iqamatus Sunnah (Jibwis) ta kasa reshen Jos.
JIBWIS kungiya ce da aka samar tun a shekarun 1970 karkashin jagorancin wani shahararren malamin addinin Musulunci Sheikh Isma’ila Idris domin yada koyarwar addinin Musulunci tsantsa bisa tsari na magabata tare da yaki da duk wasu abubuwan da ake ganin kirkira ce a cikin addini.
Kungiyar ta samu goyon baya daga fitaccen malamin addinin Musulunci na Najeriya Sheikh Abubakar Mahmud Gumi.
Tun gabanin zaben Najeriya na 2023, Sheikh Yahaya Jingir ya ja hankalin al’umma bayan ayyana goyon bayansa karara kan takarar Bola Tinubu, bayan da ya dauki Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa.
A Najeriya ba kasafai malaman addini ke fitowa kai-tsaye suna nuna bangaren da suke goyon baya ba a harkar siyasa.
Sai dai Sheikh Jingir bai taba boye goyon bayansa ga Tinubu ba, kuma yana cewa ya yi hakan ne kasancewar Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima duk Musulmai ne.
Tun bayan komawar Najeriya tafarkin dimokuradiyya a shekarar 1999, zaben 2023 ne na farko da ya samar da shugaban kasa da mataimakinsa mabiya addini daya, a kasar wadda ke da dimbin mabiya addinin Musulunci da kuma Kiristanci na rayuwa a tare.
A mafi yawan lokuta shugaban kasa Kirista kan zabi Musulmi a matsayin mataimakinsa, yayin da shugaban kasa Musulmi kan zabi Kirista a matsayin mataimaki.
Sai dai duk da cewa Tinubu da Shettima sun yi nasarar lashe zabe a 2023, hadin Musulmi da Musulmi da suka yi na ci gaba da tayar da kura da kuma haifar da muhawara a fadin kasar.
A cikin watan Yulin da ya gabata shugaba Tinubu ya sake zaben Kashim Shettima a matsayin wanda zai zame masa mataimaki a takarar shugaban kasa da zai sake yi a 2027, wanda tuni jam’iyyarsa ta APC mai mulki ta ba shi takarar.
Hukumar kare haƙƙin ɗan'adam ta Najeriya ta buƙaci a kama Sheikh Jingir
Kafin bayanin shehin malamin, hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Najeriya ta yi Allah wadai da kalaman da malamin addini Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi, inda da ta ce za su rura wutar ƙiyayya da rarrabuwar kawuna a tsakanain addinai.
Hukumar ta buƙaci Sufeto-Janar na 'Yan Sanda, Hukumar DSS da sauran hukumomin da abin ya shafa su kama tare da gurfanar da Sheikh Jingir kan zargin furta kalaman ƙiyayya da tunzura jama'a.
Shugaban hukumar, Tony Ojukwu a wata sanarwa, ya ce kalaman malamin, waɗanda suka yaɗu a wani bidiyo, suna yin kira ga siyasar wariya ga wasu addinai da kuma amfani da kalmar "kafirai".
Ya ce hakan ya saɓa wa ƙa'idojin daidaito da zaman lafiya tsakanin ƴan Najeriya, kuma hakan na iya haddasa tashin hankula.
Hukumar ta kuma yi kira ga malamai, sarakuna da 'yan siyasa da su guji kalaman rarrabuwar kawuna, inda ta ƙara da cewa za ta ci gaba da sanya ido kan yadda ake gudanar da shirye-shiryen zaɓen 2027.











