Manchester City: Sergio Aguero zai iya yin jinyar wata biyu, in ji Pep Guardiola

Manchester City striker Sergio Aguero lies down after injuring his knee against Burnley in June

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sergio Aguero bai buag wasa 12 ba tun da ya ji rauni a karawarsu da Burnley ranar 22 ga watan Yuni
    • Marubuci, Daga Simon Stone
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport
  • An wallafa

Kocin Manchester City Pep Guardiola yana fargabar cewa Sergio Aguero ba zai buga wasan wata biyun farko na gasar Firimiya ba.

Aguero ya ji rauni a gwiwarsa a fafatwar da suka yi da Burnley ranar 22 ga watan Yuni.

Hakan ne ya sa dan kasar Argentina bai buga wasanni 10 ba da City ta fafata a cikinsu a gida da kuma wasanni biyu na Zakarun Turai a watan Agusta.

Guardiola ya ce ba shi da tabbas kan ko dan wasan na City mai shekara 32 zai iya samun sauki nan da watan Nuwamba.

"Mun san cewa raunin da ya ji yana da girma," in ji Guardiola.

"Har yanzu bai yi atisaye ko daya tare da mu ba kuma Sergio dan wasa ne da ba ya warkewa daga rauni da wuri. Ya dade yana jinya, don haka watakila sai nan da wata daya ko biyu zai warke sarai."

Dan wasan da ya maye gurbin Aguero, Gabriel Jesus, ya zura kwallo biyar a wasa 12 da ya buga a karshen kakar wasan da ta wuce.

Guardiola zai sanya sabon dan wasan da ya sayo Ferran Torres a fafatawar da za su yi da Wolves ranar Litinin. Sai dai shi dan wasan ne da ke murza leda a gefe, don haka watakila Raheem Sterling ya maye gurbin Jesusu.