Abubuwan da muka sani kan yarjejeniyar Iran da Amurka

...

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Bayan da aka sanar cewa Iran da Amurka sun cimma wata yarjejeniyar fahimtar juna, kamfanin dillancin labarai na Mehr ya wallafa wasu sabbin bayanai kan daftarin yarjejeniyar fahimtar juna mai kunshe da sharuɗɗa 14, inda ya ambato wata majiya da ke kusa da tawagar Iran ɗin.

Wannan taƙaitaccen rubutun yana jaddada mahimman buƙatu da yawa a cikin sakin layi na farko: kawo ƙarshen yaƙi a kowane fage, gami da Lebanon; cikakken ɗage shingen cikin teku; buɗe mashigar Hormuz a cikin kwanaki 30; da kuma dakatar da takunkumin sayar da mai. Iran ta kuma jaddada aniyar ta na kin ƙera makaman nukiliya.

Ɗaya daga cikin sharuɗɗan ya kuma ƙunshi cewa, dole ne a saki dala biliyan 24 na kadarorin Iran da aka daskarar a cikin kwanaki 60, a daidai lokacin da aka kammala tattaunawar, tare da bai wa Iran rabin kuɗaɗen kafin a fara tattaunawar.

An kuma wallafa wata maƙala a cikin harshen Larabci a kafafen yaɗa labarai na Larabawa wanda kusan ya yi kama da na kamfanin dillancin labarai na Mehr, amma ba a taƙaita ko rarraba shi ba, inda aka yi shi a matsayin cikakkiyar maƙala.

Sai dai gidan talabijin na Channel 12 na Isra'ila ya wallafa taƙaitaccen bayani mai ɗauke da abubuwa 12 da suka yi kama da na kamfanin dillancin labarai na Mehr, inda babban abin da ya bambanta shi ne cewa ba a ambaci adadin "dala biliyan 24" ba dangane da sakin kadarorin Iran da aka daskarar.

Sa'a guda bayan wallafa wannan rubutu a kamfanin dillancin labarai na Mehr, Donald Trump ya mayar da martani a kan sa cikin fushi, inda ya rubuta a shafinsa na sada zumunta cewa: "Sharuɗɗan da Iran ta bayana wa ƙafafen yaɗa labaran ƙarya ba su da alaƙa da sharuɗɗan da aka amince da su a rubuce. Abin da suka faɗa ciki har da maganar shiriritar da suka yi game da tabbacin cimma yarjejeniya, ba shi da wata alaƙa da gaskiya. Ba su da wani aminci a wurin tattaunawa, ba su san abin da ake kira tattaunawa cikin aminci ba. Abin mamaki."

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kafar yaɗa labarai na intenet ta Tabnak ta wallafa wani rubutu mai taken "Cikakken bayani na yarjejeniyar fahimtar juna, wanda aka ce shi ne na ƙarshe."

Wannan rubutun yana da bambance-bambance masu mahimmanci da dama daga na kamfanin dillancin labarai na Mehr, kuma bai ambaci adadin "dala biliyan 24" ba kuma kawai ya ambaci sakin daskararun kadarori ne. Bugu da ƙari, rubutun da kamfanin dillancin labarai na Mehr ya wallafa ya bayyana cewa, "dole ne a ba da rabin wannan adadin ga Iran kafin a fara tattaunawa," yayin da rubutun Tabnak ya bayyana cewa, za a saki kadarorin da aka daskarar "a yayin da ake ci gaba da tattaunawa.

Bayan haka, jaridar Bloomberg News ta buga wani rubutu da Amurka ta bai wa wasu ƙasashe a matsayin asalain yarjejeniyar fahimtar juna da Iran a taron G7 da aka yi a Faransa.

Wannan rubutu ya bayyana a matsayin rubutun Ta'mnak na Turanci, kuma ba shi da bambanci da shi sai yadda ake fassara wasu kalmomi. Daga baya CNN ta buga irin wannan rubutu da ta ce wani jami'in Amurka ne ya bayar.

Duka rubutun biyu, ba shakka, sun bayyana cewa dole ne kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wannan yarjejeniyar. Dukkansu sun haɗa da samar da kuɗaɗe har dala biliyan 300.

Kwanaki biyu da suka gabata, Mista Trump ya sake musanta hakan a shafukan sada zumunta, inda ya rubuta cewa, "Dala miliyan 300 da aka ce za a biya Iran labari ne na ƙarya," wanda ko shakka babu abin da shugaban Amurka ke nufi da "Biliyan 300."

Mataimakin Mr. Trump, J.D. Vance, bai musanta hakan ba, amma ya ce ana ci gaba da aiwatar da cikakkun bayanai kan yarjejeniyar ta fahimtar juna.

Ya ce Amurka ba ta fitar da ruyawar ƙarshe na yarjejeniyar bisa buƙatar Iran kaɗai ba har ma da buƙatar masu shiga tsakani.

A jiya ne Donald Trump ya bayyana cewa ba shi da wani ƙudirin zuba jari a Iran.

Amurka ta ce za ta fitar da rubutu na ƙarshe a wani biki na da za a yi a ƙasar Switzerland a ranar Juma'a.

Har yanzu dai ƙasashen biyu ba su fitar da wata takarda da ta ƙushi yarjejeniyar a hukumance ba, amma sun ambaci wasu sharuɗɗan da ke ƙunshe a cikin ta.