Sergio Aguero ya ci kwallo 400 a tamaula

Sergio Aguero

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Manchester City ta yi nasarar doke Bournemouth da ci 3-1 a wasan mako na uku a gasar cin kofin Premier da suka kara ranar Lahadi.

City ce ta fara cin kwallo ta hannun Sergio Aguero, shi ne kuma ya ci na uku wato biyu jumulla a wasan, kuma na 400 da ya ci wa kasarsa Argentina da Manchester City.

Raheem Sterling ma ya ci wa City kwallo a karawar, yayin da Harry Wilson ya zare kwallo daya da aka ci Bournemouth.

Wannan sakamakon ya kai Bournemouth ta koma ta 10 a teburin Premier, kuma a wasa tara baya da kungiyar ta yi da City ta kwashi kwallo 28 a raga.

Ita kuwa Manchester City ta koma mataki na biyu a kan teburin Premier da maki bakwai, biye da Liverpool ta daya mai maki tara.

Manchester City ta fara da dura wa West Ham United kwallo 5-0 a wasan makon farko, sannan ta buga 2-2 da Tottenham a karawar mako na biyu a Ettihad.

Ranar Asabar 31 ga watan Agusta za a fada gumurzun mako na hudu, inda City za ta ziyarci Southampton.