KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 18/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 18/06/2026

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Jiragen ruwa sun fara wucewa ta mashigar Hormuz

    jiragen ruwa

    Asalin hoton, Getty Images

    Manyan manhajojin da ke bibiyar sufurin jiragen ruwa sun ce aƙalla jirage huɗu sun wuce ta mashigar Hormuz bayan da Amurka da Iran suka sanya hannu kan yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙi tsakaninsu.

    Jirgi na farko da ya fara wuicewa ta mashigin ɗauke da gas na ɗauke da tutar Faransa, daga nan sai uku da ke ɗauke da tutar Saudiyya.

    A ƙarƙashin yarjejeniyar, Iran za ta buɗe mashigar Hormuz sannan Amurka za ta janye rufewar da take yi wa tasoshin ruwan Iran.

    Tun baya fara yaƙin, Iran ta rufe mashigar, wadda ta nan ne ake fitar da kashi 20 cikin 100 na man fetur ɗin duniya.

    Masana dai sun ce yaƙin ya fito da hatsarin dogara da hanya ɗaya wajen fitar da mai zuwa kasuwannin duniya.

  2. Babban sifeton ƴansandan Najeriya ya umarci ƙara jami'ai a makarantun Katsina

    ƴansanda

    Asalin hoton, Getty Images

    Babban sifeton ƴansandan Najeriya, Olatunji Disu, ya bayar da umarnin ƙara ƙarfafa tsaro a makarantun jihar Katsina, a wani ɓangare na kare ɗalibai da malamai da kuma gine-ginen daga barazanar tsaro.

    Babban mataimakin sifeton ƴansandan mai lura da harkokin mulki da kuɗi, DIG Sulaiman Abdul ne ya bayyana haka lokacin wata ziyarar aiki ta kwana biyu da ya kai jihar, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    DIG Abdul ya ce an ɗora wa rundunar yansandan jihar alhakin ƙarfafa sanya idanu da yawaita sintiri a kusa da makarantun jihar, da ƙarfafa hanyoyin tattara bayanan sirri, da kuma ci gaba da kasancewar jami'an tsaro a harabar makarantun jihar.

    Ya ƙara da cewa an ɗauki matakin ne domin daƙile ayyukan ɓata-gari, da inganta ayyukan kai ɗaukin gaggawa, tare da tabbatar da cewa makarantun sun samu kariya, domin ci gaba da harkokin koyo da koyarwa.

    Jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya na cikin jihohin ƙasar da ke fama da matsalar ƴanbindiga masu satar mutane domin karɓar kuɗin fansa.

    A ƙarshen makon da ya gabata ne tsohon babban janar ɗin sojin Najeriya ya mutu a hannun ƴanbindiga bayan kwashe kwanaki a hannunsu, tare da matarsa, kodayake daga baya jami'an tsaro sun kuɓbutar da matar.

  3. Farashin mai ya ci gaba da faɗuwa bayan cimma yarjejeniyar Amurka da Iran

    Farashin man fetur na ci gaba da sauka a kasuwannin duniya bayan Amurka da Iran ta sanya hannu kan yarjejeniyar cikin daren da ya gabata.

    Yarjejeniyar ta ƙunshi buɗe mashigar Hormuz, wadda ta kasance ɗaya daga cikin hanyoyin fitar da mai zuwa kasuwannin duniya.

    A farkon mako an riƙa sayar da gangar mai samfurin Brent kan dala 86.80, yayin da a yanzu ake sayar da shi kan dala 74.80

  4. Yarjejeniyar Amurka da Iran ta ƙunshi kawo ƙarshen hare-hare a Lebanon

    hayaki

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Hayaƙi ya turnuƙe sama a kudancin Lebanon bayan rahotonnin hare-hare ta sama

    Saɗarar farko ta yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin Amurka da Iran ta ƙunshi cewa Amurka da ƙawayenta za su ayyana ''kawo ƙarshen ayyukan soji na dindindin cikin gaggawa'' a duka ɓangarori ciki har da Lebanon.

    Hare-haren Lebonon sun kasance wani ɓangare na yaƙin, yayin da Hezbollah mai samun goyon bayan Iran da Isra'ila ke zargin juna da karya yarjejeniyoyin tsagaita wuta.

    Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghaei ya bayyana a shafinsa na Telegram cewa idan Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare a Lebanon, Iran za ta ɗauki hakan a matsayin karya yarjejeniyar.

    Gidan talbijin na ƙasar ya ambato shi yana cewa ci gaba da kasancewar sojojin Isra'ila a Lebanon ka iya zama ''saɓa wa'' yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin.

  5. Japan na inganta ƙarfin sojin ƙasarta don hana ɓarkewar rikici

    Ministan Tsaron Japan ya shaida wa BBC cewa inganta ƙarfin sojin ƙasar na da matuƙar muhimmanci domin hana ɓarkewar yaƙi a yankin.

    Shinjiro Koizumi, ya ce dole ne ƙasar ta yi abin da ya dace da yadda yanayin tsaro yake a yankin domin tabbatar da zaman lafiya.

    Ya ce ƙara ƙarfafa ɓangaren tsaro da kuma ƙarfafa alaƙar Japan da Amurka na daga cikin abin da ya kira dabarar kariya mai matakai daban-daban.

    A wani sauyi da ƙasar ta yi daga tsoffin manufofinta, a baya bayannan ne ta dage haramcin da aka shafe shekaru ana yi akan fitar da makamai zuwa ƙasashen waje.

  6. Labarai da dumi-dumi, An ji ƙarar harbe-harbe a babban filin jirgin saman Nijar

    Sojoji

    Asalin hoton, EPA/US ARMY

    Mazauna Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar sun bayyana jin ƙarar harbe-harbe a babban filin jirgin saman birnin.

    Lamarin ya fara ne da misalin ƙarfe 6:00 na safe agogon ƙasar, kmar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato, yana mai cewa an shafe kusan sa'a guda ana jin ƙasar.

    An jin ƙarar harbe-harben daga ƙofar shiga filin jirgin, kamar yadda wasu shaidu biyu suka bayyana wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

    Jamhuriyar Nijar ta shafe fiye da shekara 10 tana fama da matsalar masu iƙirarin jihadi da ke kai hare-hare kan hukumomin ƙasar.

    Ko a watan Janairun wannan shekara ma masu iƙirarin jihadi sun kai wani harin a filin jirgin saman na Yamai, wanda ƙungiyar IS ta ɗauki alhakin kai shi.

    Kamar dai sauran makwabtanta Burkina Faso da Mali, Nijar na ƙarƙashin mulkin soji.

  7. Yarjejeniyar Amurka da Iran za ta fara aiki nan taken- Pakistan

    Pakistan ta ce yarjejeniyar da ka iya zama matakin farko na kawo ƙarshen yaƙin da ake tsakanin Amurka da Iran, za ta fara aiki nan take.

    Firaminista Shehbaz Sharif, ya ce Iran za ta buɗe mashigar Hormuz ba tare da ɓata lokaci ba, sannan kuma za a buɗe duk wasu tasoshin gaɓar ruwan Iran da Amurka ta rufe.

    Shugaba Trump ya ce ya sanya hannu kan jadawalin.

    Yarjejeniyar ta ƙunshi kawo ƙarshen faɗan da ake da ga kowanne ɓangare, sannan kuma a cewar Amurka Iran ta yi alƙawarin cewa ba za ta riƙa ƙera makaman nukiliya ba.

    Kakakin majalisar dokokin Iran kuma babban mai shiga tsakani na Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya yi magana da kafar talbijin ta ƙasar a kan batun a daren jiya Laraba inda ya kare yarjejeniyar.

  8. Sallama

    MAsu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Alhamis.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniyar ke ciki.

    Za ka iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta.