Matashiyar da ta ci alwashin ceton macizai daga illar ɗan'adam

Girl hold snake wit palm tree for di back

Asalin hoton, Adesola Ikulajolu/BBC

Bayanan hoto, Manufar Okikiola shi ne ta ceci macizai
    • Marubuci, Adesola Ikulajolu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Pidgin
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

A Najeriya matsalar cizon maciji ta yawaita duk da cewa ba kodayaushe ne ake jin labari ba, musamman waɗanda ke faruwa a yankunan karkara, to amma wata matashiya mai suna Taiwo Okikiola na faɗakar da mutane kan macizan da amfaninsu a muhalli.

Babu wanda zai so ya ci karo da saran maciji, musamman a ƙasashen Afirka, inda ba a cika samun magungunan cizon maciji ba.

Akwai wasu mutanen da ba sa son ganin maciji ko kaɗan, kuma da zaran sun gan shi, babu abin da za su yi sai su kashe shi.

To Amma Okikiola na ganin cewa macizai na da nasu amfanin kuma ya kamata a riƙa kare su damin kiwon lafiya.

Takan bayyana kanta a matsayin masaniya a kan dabbobi masu jan-ciki.

Tana ceton macizai daga bil'adama, tana kama su sannan ta kai su cikin daji.

Alƙaluma daga cibiyar bincike kan cizon maciji ta Najeriya sun nuna cewa akan samu saran maciji kimanin 20,000 a kowace shekara.

Haka nan an tabbatar da cewa kimanin mutum 2,000 ne ke mutuwa sanadiyyar saran maciji a kowace shekara saboda ƙarancin maganin dafin maciji.

Manufar Okikiola shi ne ta tabbatar an kare macizai ta yadda za su rayu kuma a riƙa samun maganin dafin maciji daga gare su, wanda hakn zai tseratar da ran mutane da dama.

'Maciji magani ne'

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A ƙasashen Afirka da dama, musamman Najeriya, wani labari da aka yi amanna da shi, shi ne cewa macizai na da haɗari.

Wasu ma har suna alaƙanta macizai da aljanu, wasu kuma na kallon su a matsayin dabbobi masu tattare da mugun abu, hakan ya sanya mutane da dama ba su son ko zuwa kusa da maciji.

Amma Okikiola ta yanke shawarar yin karatu kan fannin macizai, ɗabi'unsu da kuma yadda za a kare su.

Yayin da ƴan Najeriya da dama ba za su so je kusa da maciji ba, ita Okikiola tana da wata manufa guda ɗaya: tana son mutane su kyautata zato kan macizai domin halittu ne masu magani.

"Maciji dabba ce da ke harkokinta, tana neman abinci da inda za ta zauna, shi ya sa muke ganin su kusa da gidajenmu. Idan kuka lura za ku ga cewa maciji na da amfani sosai wajen magani. Maciji na magani sosai."

Okikiola ta ce tana kallon macizai a matsayin dabbobi na daban, kuma yanzu ta kwashe shekara 5 tana neman ilimi a kansu, wato irie-iren macizai da kuma halayyarsu.

Amma hakan ya sanya wasu mutanen suna tsangwamarta idan suka gano cewa tana ta'ammali da macizai.

"Wannan ya sa idan wasu mutanen suka gan ni suke kira na da matsafiya, wasu kuma su ce ina da matsala, amma ni na san abin da nake yi, kuma ina yi ne domin amfanin kowa," in ji ta.

"Ba kare macizai kawai nake son yi ba, ina so na sauya yadda mutane ke kallon su, amma fa wadanda ke da mugun dafi, wadanda ke kashe mutane a Najeriya suna da hadari," a cewar matashiyar.

Woman put snake for neck, she raise her hand wit palm tree for back

Asalin hoton, Adesola Ikulajolu/BBC

Bayanan hoto, Okikiola ta yanke shawarar nazartar ɗabiun macizai

"Ya kamata a samu maganin dafin maciji a kowane asibiti"

Aikin Okikiola bai tsaya kan nazarin yadda za ta sarrafa maciji kawai ba, domin tana kuma nazari kan yadda za a samar da maganin dafin maciji a ƙasar.

A watan Janairun 2026, ƴan Najeriya sun kadu da mutuwar wata matashiyar mawaƙiya Ifunanya Nwagene, wadda aka fi sani da Nanyah.

Bayanai sun nna cewa maciji ne ya sari matashiyar ƴar shekara 26 a gidanta, kuma ta yi ƙoƙarin ganin ta ceci rayuwarta ta hanyar garzayawa asibitoci somin samun magani.

Masu sharhi a shafukan sada zumunta sun ce asibitocin da ta je sun ƙi karɓar ta saboda rashin maganin saran maciji.

Wannan ya haifar da zazzafar muhawara kan batun maganin dafin maciji a Najeriya, kuma Okikiola ta ce nau'ukan macizai daban-daban na samar da dafi mabambanta.

Haka nan kuma likitoci ba za su iya amfani da maganin dafin maciji iri ɗaya kan dukkanin saran maciji.

Ta ce domin sanin wane irin maganin dafi za a yi amfani da shi wajibi ne a san irin macijin da ya yi saran.

Samun maganin dafin maciji babban ƙalubale ne a Najeriya kasancewar babu shi a asibitoci, musamman waɗanda suka fi kusa da al'umma.

"Abin mamaki ne a ce a shkarar 2026, babbar ƙasa a Afrka kamar Najeriya amma mutane na mutuwa saboda saran maciji, kuma abin tausayi ne a ce ba za a iya samun maganin dafin maciji a ƙananan asibitoci ko kuma kantunan sayar da magani ba."

A shekarar 2017, Najeriya ta kashe kuɗi dala 192,000 kan shirin magance saran maciji, amma mutane da dama na ganin cewa hakan bai isa ba idan aka kwatanta da miliyoyin mutanen da ke fama da saran maciji, musamman a yankunan karkara.

Ƙasar Afirka ta Kudu ita ce ta gaba wajen samar da maganin dafin maciji a Afirka, kasancewar ƙasar na da nau'uka kimanin 150 na macizai, to sai dai Okikiola ta ce ba za a iya amfani da magani ɗaya a kan mutane daban-daban na.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce mutane miliyan 5.4 ne ke fama da saran maciji a faɗin duniya, inda ake samun mutum 81,410 na mutuwa a sakamakon haka.