Abubuwa 6 da babu tabbas a kansu gabanin zaɓen Najeriya na 2027

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 7
Zaɓen Najeriya na ci gaba da ƙaratowa amma har yanzu akwai abubuwa da suka shige duhu, kuma takamaimai babu wani bayani kan halin da ake ciki.
Jam'iyyun siyasar ƙasar musamman manyan ƴan adawa na cikin tsaka mai wuya, sakamakon rikice-rikicen shugabanci da shari'o'i da suka dabaibaye su a kotu.
Ita ma hukumar zaɓe na cikin tsaka mai wuya kan wasu shari'o'i da ake jiran sakamakon su waɗanda take ganin za su iya dagula mata lissafi idan tsarin ya sauya. Amma kuma babu makawa sai an kawo ƙarshen waɗannan turka-turka kafin lokacin zaben, wanda za a fara daga watan Janairun 2027.
Ana shirin gudanar da zaɓen shugaban ƙasar ne a watan Janairun 2027, kuma tuni jam'iyyun siyasar ƙasa suka kammala fitar da ƴan takara a matakai daban-daban.
To waɗanne rikice-rikice ne suka dabaibaye shirye-shiryen zaɓen?
Makomar jam'iyyar ADC
Har yanzu tana kasa tana dabo a jam'iyyar ADC saboda rashin sanin makomarta a doron doka, musamman yadda aka riƙa yanke wasu hukunce-hukunce da ake ganin suna kawo mata tsaiko.
Jamiyyar dai tuni ta tsaida Atiku Abubakar a matsayin ɗantakarar ta na shugaban kasa a zaben na 2027, wanda ake ganin shi ne mafi karfi a cikin yan adawa. Rotimi Amaechi ne zai masa mataimaki.
A baya-bayan nan wata kotu ta umurci hukumar zaɓe ƙasar, INEC ta soke rijistar jam'iyyar ADC, da wasu guda huɗu - Accord, APP, AA, ADC da ZLP - saboda gaza cika sharuɗɗan da kundin tsarin mulki ya tanada.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ko da yike hukumar INEC ta ƙalubalanci matakin, inda kotun ɗaukaka ƙara ta dakatar da aiwatar da hukuncin kuma ta umarci INEC da kada ta ɗauki wani mataki na soke rajistar jam'iyyun.
Jam'iyyar ADC na fuskantar wata shari'ar da ta shafi rikicin shugabanci, inda har wata kotu ta taɓa ba da umurnin cire sunayen shugabanninta sakamakon ƙarar da Nafiu Bala Gombe ya shigar kan shugabancin David Mark.
Rikicin ya samo asali ne a watan Yulin 2025 lokacin da bayanai suka ce shugabannin jam'iyyar na asali sun yi murabus, inda aka naɗa David Mark a matsayin shugaban riƙon ƙwarya na jam'iyyar haɗaka, kuma manyan 'yan adawa irin su Atiku Abubakar da Peter Obi suka shiga ciki.
Sai dai Nafi'u Bala Gombe ya ƙalubalanci naɗin inda ya ce a matsayinsa na mataimakin shugaba na asali da ya rage, kundin tsarin mulki ya ba shi damar karɓar ragamar jam'iyyar.
Sakamakon takaddamar kotun, hukumar zaɓe ta INEC ta cire shugabancin David Mark na ɗan lokaci, lamarin da ya janyo cece-kuce da zargin cewa gwamnati mai mulki ”na amfani da hukumar don durƙusar da 'yan adawa”. Zargin da gwamnati ta musanta.
Daga baya ne INEC ta mayar da sunayen shugabannin ƙarƙashin David Mark ɗin bayan da kotun ƙoli ta soke matakin da kotun daukaka kara ta yi da farko, sannan ta umarci bangarorin biyu da ke shari’a da juna su koma babbar kotun tarayya domin gudanar da asalin shari’ar.
Masanan na ganin cewa dole sai irin waɗannan shari'o'i game da matsayin shugabancin ADCn ya zo karshe kafin ta san matsayarta a babban zaben kasar na shekara mai zuwa.
ADC dai ta nace cewa wajibi ne ta fafata a zaɓen ƙasar da ke tafe.
Shari'ar INEC
Akwai wata shari'a tsakanin INEC da jam'iyyun siyasar ƙasar mai matuƙar muhimmanci, kuma masana na ganin cewa dole ne a warware ta cikin hanzari kafin zaɓen 2027 domin kauce wa rugujewar daukacin tsarin zaɓen ƙasar.
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ɗaukaka ƙara a kotu ne domin ƙalubalantar hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, wanda ya soke ikon hukumar na kayyade wa'adin gabatar da jerin sunayen mambobi da 'yan takara na jam'iyyun siyasa.
Lokacin da INEC ta fitar da jadawalin babban zaɓen shekarar 2027, ta gindaya cewa lallai duk jam'iyya ta miƙa rajistar mambobinta kafin ranar 10 ga Mayu, 2026, sannan su kammala zaɓen fidda gwani kafin 30 ga Mayu, 2026.
Sai dai jam'iyyar Youth Party (YP) ce ta kai INEC ƙara gaban kotu inda ta ƙalubalanci wannan matakin da ta ce ya saɓa wa doka, kuma jam'iyyun siyasa na da dama har zuwa watan Satumba. Kotun ta amince da buƙatar, amma INEC ta ƙalubalanci matakin a kotun ɗaukaka ƙara.
Fitar da sunayen ƴan takara

Asalin hoton, Getty Images
Jam'iyyar APC na daga cikin jam'iyyun da ke fuskantar ƙalubale wajen fitar da sunayen ƴan takara bayan da ake ganin ”tana jan kafa”, wasu daga cikin wadanda suka lashe zaɓukan fitar da gwani na zargin cewa jinkirin ba su takardun shaidar lashe zaben fitar da gwani wata “maƙarƙashiya ce” ake kitsawa.
Sun yi ta ƙorafin cewa tun bayan kammala zaɓukan an kasa sakin sunayen halastattun waɗanda za su yi wa jam'iyyar takara a matakai daban-daban, kuma ba a ba su satifiket da ke tabbatar musu da nasarar ba.
Shugaba Tinubu wanda ke neman wa'adi na biyu kaɗai aka ba tutar lashe zaɓen fitar da gwanin da jam'iyyar ta gudanar.
Ana ganin dole jam'iyyar ta kawo ƙarshen jan ƙafar da take yi kafin wa'adin wallafa sunayen ya kammala.
Su ma wasu daga cikin jam'iyyun adawar ƙasar har yanzu suna fama da rikice-rikice wajen tausasa zuciyar wasu daga cikin ƴan jam'iyyarsu kafin fitar da sunayen, sakamakon yadda suke zargin ba a yi musu adalci ba.
Alal misali jam'iyyar NDC ta su Rabiu Kwankwaso da Peter Obi, wadda Seriake Dickson ke jagoranta, ita ma tana fuskantar irin wannan ƙalubale na jinkirin fitar da sunayen ƴan takararta a matakin gwamna da wasu ƴan majalisa a faɗin ƙasar.
Dukkanin jam'iyyun sai sun kammala fitar da sunayen tare da miƙa su ga hukumar INEC wadda za ta wallafa sunayen.
Sai dai ita jam'iyyar APC ta ce jinkirin da aka samu na ƙoƙarin yi wa kowa adalci ne.
Bala Ibrahim, daraktan yada labarai na jam'iyyar APCn na kasa, ya shaida wa BBC cewa ƙorafe-ƙorafen da ke gaban jam'iyyar na bukatar lokaci don a gudanar da cikakken bincike kansu.
Haɗewar ƴan adawa
Ganin yadda kusan dukkan jam'iyyun adawar ƙasar ke fama da rikici, ana hasashen wata kila su yi yunkurin dunƙulewa waje guda gabanin zaɓen 2027 idan suna son ƙalubalantar jam'iyya mai mulki ta APC.
Jam'iyyun dai sun sha zargin cewa APC ke kitsa rigingimu a cikinsu domin ganin ba su samu adawa mai ƙarfi a zaɓen ƙasar da ke tafe ba. Amma jam'iyya mai mulki ta sha musanta zargin.
A farkon haɗakar ADC dai dukkanin jiga-jigan adawar irin su Atiku Abubakar, Peter Obi, Rabiu Musa Kwankwaso, Rotimi Amaechi, Nasir El-Rufai sun haɗe waje guda.
Amma ba su jima ba kowa ya kama gabansa saboda abin da suka ce rikicin shugabanci ya jefa su a rashin tabbas game da sanin makomarsu.
Wasu kuma na kallon rarrabuwar da ‘yan adawar suka yi a matsayin wata dabara na gudun kada a musu illa a dunkule.
Masana na ganin cewa idan tura ta kai bango kuma aka samu jituwa ƴan adawar za su iya haɗewa waje guda domin tunkarar shigaba mai ci Bola Tinubu zaɓen 2027.
Takarar Jonathan

Asalin hoton, Getty Images
Jam'iyyar hamayya ta PDP bangaren Tanimu Turaki, ta bayyana tsohon Shugaban Kasar, Goodluck Jonathan, a matsayin wanda zai yi mata takarar shugaban ƙasa a zaben 2027.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da jam'iyyar ta rabu gida biyu, inda ɗaya ɓangaren da ke samun goyon bayan ministan Abuja Nyesom Wike ya tsayar da Sandy Onor a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.
Babu tabbas ko hukumar zaɓe INEC za ta amince da duk wasu bayanai da ɓangaren Turakin ya miƙa mata, saboda har yanzu shugabancin Abdulrahman Muhammad ne ke kan shafin hukumar zaɓen, dalilin da ya sa ake ganin ba lallai takarar Jonathan ɗin ta tabbata ba.
Dama an shigar da ƙara kotu ana neman a hana tsohon shugaban takara, amma kotun ƙolin Najeriya ta ce Jonathan na da hurumin sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a Najeriya.
Sai dai tun bayan da wakilinsa ya amshi shaidar takarar daga shugabancin ɓangaren Tanimu Turaki, ba a sake jin ta bakin Jonathan game da lamarin ba. Har yanzu kuma ba a san da wane ne zai yi takarar a matsayin mataimaki ba.
Masana a harkokin siyasa a ƙasar na ganin Jonathan na da damar shiga neman takarar shugabancin ƙasar kamar kowanne ɗan Najeriya, saboda yana da wa'adi guda na damar sake tsayawa takarar shugaban ƙasar.
Makomar NDC
Yadda aka yi rijistar jam'iyyar NDC ta su Peter Obi da Rabiu Kwankwaso na fuskantar turjiya bayan da aka shigar da ƙarar neman a soke jam'iyyar a gaban kotu.
Tsohon ɗan takarar gwamna a jihar Adamawa kuma jigo a jam'iyyar ADC, wanda ya yi yunƙurin kafa jam'iyyar ADA, Dr. Umar Ardo, ne ya maka jam'iyyar da kuma hukumar zabe ta INEC a kotu, inda ya ce yana da yaƙinin cewa jam'iyyar NDC ba ta cika ƙa'idojin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya shimfiɗa wajen rajistar jam'iyya ba.
Wata Kotu ce dai ta ba INEC umarnin yi wa jam'iyyar rijista bayan da hukumar zaɓen ta ƙi amincewa da ita a baya. Dr. Ardo ya ce NDC ba ta da sahihancin zama cikakkiyar jam'iyya kamar yadda yake a dokokin INEC.
"NDC ta je ta karɓi rajista ba tare da ta gabatar da buƙata a rubuce ba. Ba ta cika ka'idojin da INEC ta shimfiɗa ba, haka kuma ba ta bi tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya ba. Wannan ne ya sa na kai ƙara a kanta." kamar yadda ya bayyana a wata hira da DCL Hausa.
Yanzu dai ana jiran ganin hukuncin da kotun za ta yanke kan makomar NDC, wanda soke ta zai iya mayar da hannun agogo baya ga ƴan adawar ƙasar.











