An ji ƙarar harbe-harbe a babban filin jirgin saman Nijar

Asalin hoton, EPA/US ARMY
Mazauna Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar sun bayyana jin ƙarar harbe-harbe a babban filin jirgin saman birnin.
Lamarin ya fara ne da misalin ƙarfe 6:00 na safe agogon ƙasar, kmar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato, yana mai cewa an shafe kusan sa'a guda ana jin ƙasar.
An jin ƙarar harbe-harben daga ƙofar shiga filin jirgin, kamar yadda wasu shaidu biyu suka bayyana wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Jamhuriyar Nijar ta shafe fiye da shekara 10 tana fama da matsalar masu iƙirarin jihadi da ke kai hare-hare kan hukumomin ƙasar.
Ko a watan Janairun wannan shekara ma masu iƙirarin jihadi sun kai wani harin a filin jirgin saman na Yamai, wanda ƙungiyar IS ta ɗauki alhakin kai shi.
Kamar dai sauran makwabtanta Burkina Faso da Mali, Nijar na ƙarƙashin mulkin soji.
A ranar 28 ga watan Janairun 2026 ɗin nan ma an samu harbe-harbe da fashe-fashe a kusa da babban filin jirgin sama na Diori Hamari da ke babban birnin na Niamey na Jamhuriyar Nijar.
Shaidun gani da ido sun tabbatar da aukuwar lamarin, sannan wasu faye-fayen bidiyo sun bayyana yadda wasu na'urorin kariya na sararin samaniya ke ta ƙoƙarin tare wasu abubuwa da ba a iya tantancewa da tsakar dare.
Daga baya dai komai ya lafa, kamar yadda aka ruwaito daga wani jami'in gwamnati, duk da cewa bai yi ƙarin haske ba kan lamarin ba.
Jamhuriyar Nijar dai tana fama da ƙungiyoyi masu iƙrarin jihadi da ke addabar sassan ƙasar kamar Boko Haram da ƙungiyar Jama'at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM), mai alaƙa da Al-Qaeda.
A baya-bayan nan ne hukumomi a jamhuriyar ta Nijar suka ƙaddamar da wani aikin rushe gidaje fiye da 26,000 da ke kusa da filin jirgin saman na Diori Hammani da ke birnin Niamey.
Hukumomin dai sun ce sun ƙudiri niyyar rushe gidajen ne bisa dalilan tsaro, wani al'amari da ya janyo tankiya tsakaninsu da ƴan ƙasar musamman mutanen da abin ya shafa.











