An yi watsi da tayin Arsenal na siyen Monga, RB Leipzig na harin Barry

Jeremy Monga

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

An yi watsi da tayin Arsenal na farko, na siyen ɗan wasan Leicester City da Ingila Jeremy Monga, daya daga cikin ƴan wasan da ƙungiyar ta jima tana son ɗaukowa. (Telegraph - subscription required)

Haka kuma Gunners ɗin na shirye-shiryen tayin siyen ɗan wasan Paris St-Germain Bardley Barcola. (Independent)

RB Leipzig sun tuntubi Everton kan siyen ɗan wasan Faransa Thierno Barry. (Times - subscription required)

Real Madrid na duba sake gina ƙungiyar ta hanyar siyen ɗan wasan tsakiya, da masu tsaron gida, inda ɗan wasan Chelsea da Ajantina Enzo Fernandez ke kan gaba cikin ƴan wasan da Madrid din ke son ɗaukowa. (ESPN)

Har yanzu Everton ba su kai ga samun tayin ɗan wasan su Barry ba a hukumance, sai dai idan aka sami wani tayi daga ɓangaren RB Liepzig ko wata ƙungiyar ta daban, shugabancin ƙungiyar ta Everton zai yanke hukuncin yadda za a ci gaba da tattaunawa. (Liverpool Echo)

Tottenham na kan shirinta na siyen ɗan wasan Anderlecht da Belgium Nathan De Cat, yayin da Manchester United ke cikin jerin ƙungiyoyi da ke zawarcin dan wasan. (Teamtalk)

Liverpool ta sake sabunta aniyarta na siyen ɗan wasan Juventus da Faransa Khephren Thuram. (Corriere dello Sport via Football Talk)

Haka kuma Liverpool na son siyen ƴan wasan tsakiya da na baya, da na gefe, wanda hakan ya janyo sakin jadawalin bukatar siyar ɗan wasan Osasuna da Sipaniya Victor Munoz kan Euro miliyan 40 kwatankwacin fam miliyan 34.5. (Football Insider)