Kotu ta ɗaure mutumin da ke tara buhunan ba-haya a ƙofar gidansa a Kano

Asalin hoton, Mahmud Bashir
- Marubuci, Mansur Abubakar
- Aiko rahoto daga, Kano
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 3
Wata kotu a arewacin Najeriya ta yanke hukuncin ɗauri na mako biyu ga wani mutum bayan maƙwaftansa sun yi ƙorafi kan yadda yake tara buhunan ba-haya a ƙofar gidansa, lamarin da ke cutar da mazauna unguwar.
Maƙwafta ne suka kai ƙarar Mohammed Sa'idu kotu a birnin Kano, bayan sun ce warin ya buwaye su.
Mai shari'a Halima Wali ta yanke hukuncin a tsare mutumi na tsawon wata huɗu sannan an buƙaci ya biya tarar naira 100,000.
Ta bayyana abin da ya aikata a matsayin barazana ga lafiyar maƙwaftansa.
Mallam Sa'idu, wanda ke aikin yashe masai, yana sayar da ba-hayar ne ga manoma wadanda ke amfani da shi a matsayin taki – wani abu da manoma da dama ke amfani da shi, sai dai ba kowa ne ya sani ba.
Mai unguwar yankin Musa Abdullahi ya shaida wa BBC cewa "Ina ganin ya tara kimanin buhu 50 na ba-haya a ;lokacin da mutane suka kawo min ƙorafi".
Maƙwafta sun ce warin ya yi muni ta yadda ba su iya hutawa cikin kwanciyar hankali a cikin gidajensu.
Ɗaya daga cikin wadanda ya kai ƙorafin, Mallam Samaila Inuwa ya shaida wa BBC cewa sun so su warware matsalar cikin lalama.
"Mun masa magana a kan batun, amma ya ƙi dainawa," in ji Inuwa.

Asalin hoton, Mahmud Bashir
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A kotu, Mallam Sa'idu ya amince cewa ya yi laifi ta hanyar jefa rayuwar mutane cikin haɗari.
Kafin sanar da hukuncin kotu, mai shari'a Wali ta ziyarci ƙofar gidan Sa'idu da kanta domin gane wa idanunta buhunan kashi da ya tara.
Ta umarci Sa'idu ya kwashe duk wasu buhunan ba-haya da ya jibge daga ƙofar gidan nasa, sannan ta buƙace shi ay ɗauki alƙawarin cewa ba zai sake yin hakan ba.
Mallam Inuwa ya ce rayuwarsu ta nganta tun bayan kai batun kotu.
"A yanzu kam muna zaune lafiya lau a unguwarmu ba tare da mummunan wari ba," in ji shi.
Mai unguwar ya ce tun farko ya fara tsoma baki kan lamarin a lokacin da Sa'idu ya fara jibge buhunan ba-haya a ƙofar gidan.
"A lokacin da ya fara, na yi masa magana, sai ya kwashe su kuma ya daina, amma ban san lokacin da ya sake ci gaba da jibge su ba."
Ya ce daga nan ne maƙwafta suka yanke shawarar zuwa kotu kai-tsaye domin miƙa lamarin a hannun mahukunta.
Abdullahi ya vce gidansa na da nisa daga wurin da mutumin ke jibge ba-hayan, shi ya sa warin bai kai wa gidansa, amma duk da haka ya fahimci ƙorafin maƙwaftan.
"Manufata ita ce na ga kowa na zaune lafiya a wannan unguwa," in ji shi.
Ya ƙara da cewa "za mu sake yin zama da shi da maƙwaftan idan an sako shi."









