Yadda tumaki suka mamaye birnin Madrid

Flocks of sheep and goats are herded in the city centre of Madrid on October 20,

Asalin hoton, AFP

An wallafa

Sama da dabbobi 2,000 suka mamaye birnin Madrid domin bikin al'ada da ake gudanarwa duk shekara a Spain.

Babban birnin na Spain ya kasance tsohuwar hanyar da makiyaya ke ratsawa da dabbobinsu zuwa kudanci a lokacin hunturu.

Bikin da ake kira Fiesta de la Trashumancia, ya samu bunkasa daga hukumomi musamman masu kula da yawon shakatawa.

A 1994 aka fara gudanar da bikin, kuma an tsara shi ne domin girmama al'adun karkara.

Sheep line a road lined with tourists in the city centre

Asalin hoton, EPA

Hundreds of sheep are led through a street in downtown Madrid

Asalin hoton, EPA

Tsarin ya ba makiyaya damar ratsawa ta cikin birni tare da dabbobinsu.

Duk shekara, akwai kudi da ake biya tsakanin magajin gari da shugaban makiyaya domin ba dabbobin damar ratsawa ta cikin gari tare da ba su kariya.

Flocks of sheep are herded in front of the city hall in Madrid

Asalin hoton, AFP

Makiyayan da ke kora dabbobin sukan sa tufafi ne na gargajiya domin bikin.

Masu yawon bude ido kan fito domin kallon bikin da ake gudanarwa a ranar Lahadi inda ba a fiye samun cunkuson ababen hawa ba.

Flocks of sheep and goats are herded in the city centre of Madrid on October 20

Asalin hoton, AFP

Ana daurawa tumakin karaurawa domin bikin, inda karar ke karade birnin Madrid.

An fara bikin ne misalin karfe 10:30 na safe agogon kasar misalin karfe 8:30 agogon GMT.

Tumakin sun fara ne daga wani babban dandali da ake kira Casa de Campo.

Baya ga tumaki 2,000 akwai kuma kimanin awaki 100 a wajen bikin, kamar yadda kamfanin dillacin labaru na Reuters ya ruwaito.

A goat stares into the camera in a close-up shot

Asalin hoton, EPA

Dukkanin hotuna mallakin EPA da AFP ne.