Man city ta kusan daukar Maresca, Bayern Munich za ta sake tattaunawa da Olise

Enzo Meresca

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Enzo Meresca
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester City na gab da cimma matsaya kan kudin da zata biya Chelsea domin ta samu damar nada Enzo Maresca (Guardian)

Chelsea na zawarcin dan wasan Liverpool Florian Wirtz wanda ya taka leda a karkashin sabon kocin kungiyar, Xabi Alonso a Bayer Leverkusen amma duk wata yarjejeniya da dan wasan Jamus mai shekara 23, zai kulla ta dogara ne kan idan dan wasan Argentina Enzo Fernandez, mai shekara 25, ya bar Stamford Bridge.(Football Insider), external

Dan wasan Jamus Felix Nmecha na shirin barin Borussia Dortmund kuma Liverpool da Manchester United duk suna zawarcin dan wasan mai shekara 25.( Teamtalk), external

Watakila Newcastle ta sayar da dan wasan Jamus Nick Woltemade, mai shekara 24, inda Aston Villa da Dortmund da Atletico Madrid na cikin wadanda suke son daukarsa. (AS - in Spanish), external

Brighton ta inganta tayin fam miliyan 45 da ta yi wa dan wasan Tottenham da Croatia Luka Vuskovic mai shekara 19. (Mail), external

RB Leipzig na sa ran Paris St-Germain za ta nemita domin ta sayar mata da dan wasan Ivory Coast Yan Diomande, mai shekara 19, bayan ta ki amincewa da tayin farko na yuro miliyan 100 daga Liverpool. (Bild - in German), external

Idan dan wasan Ingila Elliot Anderson,mai shekara 23 ya koma Manchester City to wannan zai iya sa Nottingham Forest ta dauko dan wasan Italiya Davide Frattesi mai shekara 26 daga Inter Milan wadda ita kuma ke son ta kamala cinikin sayan dan wasan Liverpool Curtis Jones mai shekara 25 (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Bayern Munich za ta yi kokarin sake tattaunawa da Michael Olise kan kwantaraginsa yayin da Real Madrid da PSG ke zawarcin dan wasan Faransa mai shekara 24.(AS - in Spanish), external

Real Madrid ta musanta rahotannin da ke cewa wakilanta sun tuntubi bangaren Olise (Sport - in Spanish), external

Juventus na son ta siyar da dan wasan Canada Jonathan David, mai shekara 26, kuma ta tsayar da farashin Yuro miliyan 30 akansa.(Corriere dello Sport - in Italian), external

PSG na son yuro miliyan 40m a kan Randal Kolo Muani kuma dan wasan Faransa mai shekara 27 ya kosa ya koma Juventus, wadanda suma suke zawarcin dan wasan Atletico Madrid Alexander Sorloth, mai shekara 30. (Corriere dello Sport - in Italian), external