Ƙasar da ke bayar da tallafi ga ma'auratan da ke son ƙarin haihuwa

Wasu iyaye da dansu
Bayanan hoto, Abin ihsanin zai ƙarfafa wa ma'aurata samun ƙarin ƴaƴa
    • Marubuci, Stephanie Hegarty
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Global Population Correspondent
    • Marubuci, Zsofia Paulikovics
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Magyarul
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Yayin da take zaune a kan bencin da ke ƙarƙashin wata bishiya a harabar jami'ar birnin Debrecen da ke gabashin Hungary, Barbara Elek na ci gaba da duba saƙonninta na imel.

Ita da mijinta Levi na jiran saƙon ko Barbara ta samu ciki sakamakon aikin dashen ƙwayoyin haihuwa karo na uku da aka yi mata kwanaki 10 da suka gabata.

"Idan ba a samu nasara ba, tabbas zai zama abin tashin hankali," kamar yadda ta shaida wa shirin mata na BBC Global Women.

Tashin hankalin nata ba ya takaita ne kawai kan baƙin cikin rashin samun ɗa ba.

A maimakon haka ita da Levi za su iya fuskantar matsalar kuɗi idan ba ta samu cikin ba.

Kamar dai sauran matasan ma'aurata a Hungry, Barbara ma'aikaciyar jin ƙai da Levi ƙwararren mai girki, za su iya samun dubban daloli a matsayin bashin marar ruwa da samun tallafin gwamnati idan suka alƙawarta samun ƴaƴa biyu.

Amma a lokacin da suka fahimci cewa ba za su iya samun ciki ta hanyar da aka saba samu ba, abubuwa sun fara taɓarɓare musu.

Idan suka kasa tabbatar da cewa suna da juna biyu nan da watan Nuwamba, za su iya fuskantar biyan bashin da suka karɓa haɗe da kuɗin ruwa mai yawa - wani abu da zai iya laƙume kusan rabin abin da suke samu.

A couple walks hand in hand. The woman holds a blue binder. Behind them you see a building with a sign reading 'assisted reproduction centre' in Hungarian.
Bayanan hoto, Kamar sauran ma'auratan Hungary, Barbara da Levi ka iya fuskantar bazaranar biyan bashi da ruwa idan ba su samu haihuwa ba.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Cikin shekara 16 da suka gabata, ƙarƙashin jagorancin tsohon firaministan ƙasar Viktor Orbán, Hungary ta riƙa bayar da tallafin ga ma'auratan da suka samu juna biyu a wani mataki na ƙarfafa gwiwar samun ƙarin haihuwa a ƙasar.

Wannan ya ƙunshi bashi da sharaɗin ƙara shi dangane da yawan yaran da ma'auratan za su haifa, idan kuma suka haifi yara uku ta za a yafe musu bashin kacokan.

Hungary ta keɓe kashi 4 zuwa 5 na arzikin da take samu a cikin gidan kan waɗannan matakan, kusan dala biliyan 16 wanda ya kai adadin da ƙungiyar tsaro ta Nato da buƙaci mambobinta su kashe kan tsaronsu.

Máté da Ági Gorondy wasu iyaye ne masu ƴaƴa biyar ƴan ƙasa da shekara 10.

Sun yi amfani da wannan dama na tallafin haihuwa wajen gyra gidansu tare da sayen dalleliyar mota.

Máté, ta amfana da rangwamen harajin da ta riƙa samu wanda ya riƙa ruɓanya bayan kowace haihuwa.

A matsayinta na uwar yara fiye da biyu, an cire mata biyan haraji a duk kudin da ta samu.

"Waɗannan tsare-tsaren gwamnati sun taimake mu wajen samun ƙarin yaƴa tare da tallafa wa iyalinmu,'' a cewar Máté.

.
Bayanan hoto, Máté Gorondy ya ce bayar da tallafin ya ƙarfafa musa gwiwa shi da matarsa wajen samun ƴaƴa.

Ta ce a ƙauyensu da ke wajen Budapest, babban birnin ƙasar, an samu ƙaruwar ma'auratan da ke haihuwar yara huɗu zuwa biyar.

A ɗan lokacin nan an samu ƙarin haihuwa a Hungary daga kashi 1.25 zuwa kashi 1.61 nan da 2020.

To amma a shekaru ukun da suka gabata yawan haihuwar ya kuma raguwa zuwa kashi 1.31, ba kamar lokacin da aka ɓullo da shirin tallafin ba.

A cewar Timothy P. Carney, babban mai bincike a cibiyar nazarin kasuwanci ta Amurka, da ya rubuta litattafai da yawa kan raguwar haihuwa ya ce ''wani ɓangare na matsalar shi ne muna kambama yadda ake samun kuɗin.

Ba Hungray ce kawai ƙasar da ta yi yunƙurin bunƙasa yawan haihuwa ta hanayr bayar da tallafin kuɗi.

Yawan haihuwa a Koriya ta kudu ta kai kashi 1.19 a shekarar 2008, ɗaya daga cikin ƙasashen da ake samun ƙarancin haihuwa a duniya.

Tun lokacin ƙasar ta kashe kudan dala biliyan 290 domin neman haihuwa da nufin bunƙasa yawan al'umarta.

Iyaye a ƙasar kan samun tallafin jarirai da ya kai tsakanin dala 27 zuwa 40,000, tsakanin biyu zuwa haihuwa, kuma jariran kan samu tallafin kudi a kowane wata.

To amma yawan haihuwa a Koriya ta Kudu ya ragu a wancan lokacin, inda ya kai kashi 0.8 a 2025.

.
Bayanan hoto, An yi wa Barbara allura domin taimaka mata samun ciki.

Barbara da Levi sun haɗu da juna shekara tara da suka wuce, a lokacin suna farkon shekarunsu 20 sannan suka yi aure.

Sun ƙuduri aniyar haifar yara biyu, domin samun dala 33,000 na bashin samun haihuwa a 2020.

Yayin da suka gaza samun juna biyu ta hanyar da aka saba, sai aka tura su wani asibitin gwamnati da ke bayar da tallafin dashen ƙwayoyin haihuwa (IVF), mai nisan tazarar tafiyar sa'a ɗaya da rabi daga gidansu.

Domin kauce wa tarar da za ta biya idan ba ta samu ciki ba, Barbara na buƙatar tabbatar da gwamnati cewa ta ta yi duk mai yiwuwa domin ta samu cikin, amma ba ta samu ba.

Sau biyar ya kamata a yi mata dashen ƙwayoyin haihuwa, kuma zuwa yanzu an yi mata sau uku, amma shiru.

'
Bayanan hoto, Antónia Miskolczi na ganin cewa tallafin da ƙasar Hungary ke bai wa mutane ya sa suke neman ƴaƴa.

Sai dai bayan ɗaukar tsawon lokaci suna jiran sakamakon dashen ƙwayoyin haihuwar, Barbara da Levi sun samu mummunan labari cewa dashen nasu bai yi nasara ba.

Hakan ba yana nufin ba za su iya samun ɗa kawai ba, hatta bashin da za su riƙa biya a kowane wata zai ninka.

Kuma ba su kaɗai ba ne, akwai ire-irensu da dama.

Babban bankin Hungary ya yi ƙiyasin cewa akwai ma'aurata 25,000, kuma kashi ɗaya cikin biyar na ma'auratan ƙasar da suka karɓi bashi tsakanin 2019 zuwa 2021 da ba su samu haihuwar ba za su biya bashin mai cike da ruwa a wannan shekara.

Sabuwar gwamnatin Hungary da za fara mulki a watan Afrilu, ta bayyana cewa za ta tsawaita wa'adin da aka keɓe wa ma'auratan domin samun ƴaƴan, kuma ta ce tana aiki domin samu mafita ga waɗanda ba su samu haihuwar ba.

Wani matsi da gwamnatin za ta shiga shi ne ko za ta iya ci gaba da bayar da tallafin haihuwar ba.

Tsarin ya samu karɓuwa a ƙasar. Don haka dakatar da shi ka iya janyo cece-ku-ce a ƙasar,' a cewar Antónia, wanda ya ce "mutane sun riga sun gina rayuwarsa da tsare-tsarensu a kan tallafin.

'.

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Allunan da ke tallata janye haraji da ma'auratan da suka ƙudiri aniyar samun ƙarin haihuwa.
t.
Bayanan hoto, .