Ko ƴan jaridar Najeriya za su iya iya bin sojojin kasar filin daga?

Sojojin Najeriya

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Sojojin Najeriya
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Kungiyar 'yan jarida ta kasa a Najeriya ta yi maraba da wani shiri da gwamnati ke duba yiwuwar aiwatarwa na bai wa 'yan jarida damar bin tawagogin sojoji yayin da suke gudanar da ayyukansu a fagen daga, a wani mataki da ake ganin zai iya sauya yadda ake bayar da rahoto kan yakin da ake yi da ta'addanci a kasar.

Shirin na daga cikin kokarin gwamnatin Najeriya na inganta sahihancin rahotannin da ake samu daga yankunan da ke fama da rikici, tare da nuna irin kalubalen da jami'an tsaro ke fuskanta a yayin gudanar da ayyukansu na yaki da kungiyoyin masu dauke da makamai da kuma sauran barazanar tsaro da ke addabar sassa daban-daban na kasar.

An bayyana wannan kudiri ne a cikin wata sanarwa da Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya karanto a wani taron tattaunawa da kungiyar 'yan jarida ta kasar.

A cewar sanarwar, gwamnati na duba hanyoyin da za su tabbatar da cewa 'yan jarida za su samu damar yin aiki a fagen fama cikin tsari, ba tare da tauye ka'idojin tsaro ba, tare da tabbatar da cewa rahotannin da ke fitowa daga wuraren da ake gudanar da ayyukan soji sun kasance masu inganci.

Shugaban kungiyar ta NUJ na kasa, Alasan Yaya, ya bayyana goyon bayan kungiyar ga wannan yunkuri, yana mai cewa hakan zai iya taimakawa wajen kara fahimtar da jama'a kan kokarin da hukumomin tsaro ke yi a fannin yaki da rashin tsaro a kasar.

Ya ce idan aka tsara shirin yadda ya kamata, zai iya zama wata muhimmiyar hanya ta samar da rahotanni kai tsaye daga fagen fama, maimakon dogaro da bayanan da ake fitarwa bayan kammala ayyuka.

Masu sharhi kan harkokin yada labarai sun ce irin wannan mataki na iya zama muhimmin sauyi a dangantaka tsakanin kafafen watsa labarai da hukumomin tsaro a Najeriya, musamman a wannan lokaci da ake yawan sukar rashin sahihan bayanai daga yankunan da ke fama da rikici.

Sai dai kuma wasu na nuna damuwa kan batun tsaro, suna cewa bin sojoji kai tsaye zuwa fagen fama na iya jefa 'yan jarida cikin hadari, musamman a yankunan da ake fama da hare-hare da dagulewar matsalar.

A halin yanzu, ba a fitar da cikakken jadawalin fara aiwatar da shirin ba, amma ana sa ran za a ci gaba da tattaunawa tsakanin gwamnati, da rundunar soji da kuma kungiyoyin 'yan jarida domin samar da tsarin da zai yi daidai da ka'idojin tsaro da kuma 'yancin aikin jarida a kasar.

Matsalar tsaro dai na ci gaba da karuwa a Najeriya, inda ake fuskantar hare-hare a sassa daban-daban na kasar.

Ministan Tsaron kasar Christopher Musa, ya ce shirin na cikin matakan da gwamnati ke nazari domin tabbatar da cewa kafafen yada labarai na samun damar ganin ainihin yadda jami'an tsaro ke gudanar da ayyukansu, cikin tsarin da zai kare rayukan 'yan jarida da kuma kiyaye sirrin aikin soja.