Lalurorin da za ka iya fuskanta idan kana fama da rashin ƙarfin mazakuta

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, David Robson
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 7
Ko kun san cewa rashin ƙarfin mazakuta a tsakanin maza alama ce ta wasu lalurorin da za su iya faruwa da mutum, kamar: bugun zuciya, bugun jini, ciwon suga da kuma mantuwa?
Masu bincike na ganin cewa ya kamata masu fama da matsalar da kuma likitoci su mayar da hankali sosai kan lalurar.
Ana iya bayyana rashin ƙarfin mazakuta tsakanin maza a matsayin wata lalura mai yin kisan mummuƙe.
Wani bincike ya nuna cewa fiye da rabin maza waɗanda suka zarta shekara 40 na fama da rashin ƙarfin mazaƙuta, sai dai kaɗan ne daga cikin irin wadannan maza ke amincewa su tattauna matsalar da makusantansu.
A duk lokacin da aka kawo batun cikin fira, sai a mayar da shi wani abin raha, a maimakon tattaunawa kan illar da cutar za ta iya yi wa mutum a gaba.
To sai dai wani bincike na baya-bayan nan ya nuna cewa azzakari wata gaɓa ce da za ta iya samar da bayanai kan lafiyar mutum baki ɗaya, saboda haka rashin ƙarfin mazaƙuta zai iya zama alamar wasu cutuka da dama, kamar ciwon suga da na zuciya da bugun zuciya da kuma cutar mantuwa.
Emanuele Janini, masanin lafiyar jima'i a jami'ar Tor Vergata da ke birnin Roma na ƙasar Italiya, wanda a baya-bayan nan ya yi nazari kan wasu bayanan kimiyya, ya bayyana rashin ƙarfin mazaƙuta a matsayin "gargaɗi kan matsalolin da ke iya tasowa," gargaɗi kan ahtsarin da mutum zai iya faɗawa ciki a gaba.
Saboda haka bunƙasa hanyoyin binciken gano rashin ƙarfin maza zai iya bai wa likitoci damar gano wasu miyagun cutukan da namiji zai iya fuskanta kafin abin ya yi muni.
Sai dai ƙin yin magana kan matsalar rashin ƙarfin mazaƙuta da maza ke yi, shi ne babban abin damuwa.
Cutukan zuciya

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kamar sauran lalurori, gano girman lalurar rashin kuzari ga namiji ya dogara ne kan hanyar da aka bi wajen tantance matsalar, saboda haka sakamakon binciken ya banbanta, lamarin da kuma ke nuni da cewa yawaitar wannan lalura a tsakanin maza a sassan duniya ya kama daga kashi uku cikin ɗari zuwa kashi 76.5 cikin ɗari, wanda tazara ce mai yawan gaske.
Sai dai ɗaya daga cikin bincike mafi inganci da aka yi, wanda aka zaɓi mutane 1,200 da suka takardun tambayoyin da aka yi masu, ya cimma matsaya cewa kashi 39 cikin ɗari na mazan da suka kai shekara 40 su na fama da wani nau'i na lalurar rashin ƙarfin mazaƙuta, kuma yawan su yana ƙaruwa zuwa kashi 67 cikin ɗari idan suka kai shekara 70 a duniya.
A takaice, ana iya ɗaukar rashin ƙarfin mazaƙuta a matsayin wata lalura da ta ke da alaƙa da hanyoyin jini da kuma yanayin gudanar jini a cikin su.
A jikin mazakuta akwai wasau halittu biyu masu kama da soso da ake kira corpora cavernosa.
Akasari suna a kwance ne. Amma idan sha'awa ta motsa, ƙwaƙalwa tana aikewa da saƙo da ke sanya jijiyoyin mazakuta su buɗe kuma jini ya samu wucewa cikin sauƙi.
Idan suka buɗe, corpora cavernosa na miƙewa kuma hakan na sanya wa su matse jijiyoyin da ke shigar da jini cikin mazakuta, lamarin da ke janyo tsayawar jinin a ciki.
Kamar yadda balan-balan ke kumbura ya ƙara girma idan aka hura mashi iska, mazaƙuta na miƙewa kuma ya yi tauri.
Saboda haka, duk wani abu da ke iyakance kwararar jini ko taruwar jini a cikin jijiyoyin mazaƙuta zai yi mummunan tasiri ga miƙewar mazaƙutar da kuma daɗewar da za ta yi a miƙe.
Matsalolin damuwa na ƙara kawo wannan. Kuma idan suka haɗu da gajiya za su iya janyo tushewar hanyoyin jini sannan su hana tashin sha'awa yadda ya kamata ga namiji.
Haka nan kuma, gajiya da kanta tana da alaƙa da lafiyar ƙwaƙwalwar mutum, wadda za ta iya shafar yadda zai mayar da hankali domin samun gamsuwa a yayin jima'i
Lalurar zuciya da ƙwaƙwalwa

Asalin hoton, Getty Images
A lokuta da dama, rashin ƙarfin mazaƙuta alama ce ta wata rashin lafiya da ta fi wannan muni. Daga cikin su akwai lalurar atherosclerosis wadda ke sanya hanyoyin jini su yi tauri kuma su ƙanƙance, kuma wannan matsala na janyo cutar zuciya.
Tunda jijiyoyin mazaƙuta na cikin mafi ƙanƙanta a jikin mutum, su ne suke saurin sauyawa idan aka samu wannan sauyi, don haka ɗaukewar sha'awa ga namiji na daga cikin alamomin farko na ciwon zuciya.
Binciken baya bayan nan wanda ya yi nazari kan bayanai daga mutane 154,794 ya nuna cewa kashi 59 cikin ɗari na maza masu lalura rashin karfin mazakuta sun fi kamuwa da cutar jijiyoyin zuciya, sai kashi 34 cikin ɗari daza su iya fama da lalurar bugun jini.
Michael Carroll, ƙwararre a kan kimiyyar haihuwa a Jami'ar Manchester Metropolitan da ke Burtaniya kuma marubucin littafin "Your Testicles: The Science of How They Work and What They Mean for Your Fertility,'' ya tabbatar da cewa ƙarfin sha'awa da ƙarfin mazaƙuta na nuni da lafiyar zuciyar namiji.
Akwai hujjoji da ke nuni da cewa matsalar rashin ƙarfin mazaƙuta na iya zama alamar ciwon zuciya.
Wani bincike da aka yi a Taiwan ya nuna cewa kashi 68 cikin ɗari na mazan da aka gano suna da lalurar rashin ƙarfin mazaƙuta na iya yin fama da cutar mantuwa cikin shekara bakwai bayan gano suna da lalurar sha'awa.
Kamar dai yadda mazaƙuta ta dogara ga gudanar jini, ita ma ƙwaƙwalwa ta dogara ga shi domin samun kuzarin yin aiki da kuma tashe abubuwan da ba a buƙata.
Alaƙar rashin ƙarfin mazaƙuta da ciwon siga

Asalin hoton, Getty Images
Gano abin da ya janyo lalurar rashin ƙarfin mazaƙuta na da muhimmanci sosai ga mutanen da ke da haɗarin kamuwa da ciwon siga saboda mummunar illar da cutar ke yi wa sassa da dama na jiki.
"Akwai alaƙa mai kusanci sosai tsakanin ciwon siga da rashin ƙarfin mazaƙuta,'' in ji Bogdan Flajo, wani mai bincike a cibiyar Sant Pau Research Institute ta Barcelona. "Maza masu ciwon siga nau'i na 2 na da matuƙar haɗarin yin fama da lalurar rashin ƙarfin mazaƙuta."
Flacho ya ƙara da cewa wani bincike ya tabbatar da cewa masu fama da dukkan matsalolin biyu na cikin babban haɗarin kamuwa da cutukan ƙwaƙwalwa da kuma na rashin gani ko makanta.
Maganin da za a iya yi

Asalin hoton, Getty Images
Wani bincike da aka yi a gidauniyar kula da masu lalurar al'aura ta Birtaniya ya nuna cewa fiye da rabin maza masu fama da lalurar rashin ƙarfin mazaƙuta ba su iya bayyana kansu domin neman magani saboda kunya da fargaba.
Kuma kashi 20 cikin ɗari na waɗanda aka tattara bayanan su domin binciken sun ce gara su daina shan barasa na tsawon wata guda a kan su je gaban ƙwararren likita domin bayyana mashi matsalar tasu.
Carroll ya gamsu cewa ya kamata duk namijin da ke fama da lalurar rashin ƙarfin mazaƙuta ya nemi taimakon likita.
Bayan samun sauƙin wasu abubuwa masu alaƙa da ƙwaƙwalwa, zai kuma bayar da damar tattaunawar kai tsaye da ƙwararru domin ceton rayuwar mai lalurar.
Ya ce: "Ɗaukar matakin gaggawa domin magance matsalar abu ne mai matuƙar amfani."
Yana da muhimmanci a jaddada cewa ɗaukewar sha'awa ko rashin ƙarfin mazaƙuta ba lalura bace da ba a iya magancewa.
Magunguna irin sildenafil (ko Viagra) yana taimakawa wajen buɗe hanyoyin jini a mazaƙuta, kuma wasu ƙwararru sun ce masu amfani da irin wannan magunguna za su samu sauƙin wasu matsaloli masu janyo ciwon zuciya, ciki harda rage haɗarin samun bugun zuciya.
Sai dai kuma har yanzu babu wani bincike mai zaman kansa da ya tabbatar da wannan iƙirari. (Yana da kyau a sani cewa dama can an ƙirƙiro da maganin Viagra ne domin magance matsalolin zuciya masu alaƙa da hawan jini, kafin daga baya aka gano yadda yake ƙara ƙarfin sha'awa da ƙarfin mazaƙuta.
Tattaunawa da likita kan matsalar rashin ƙarfn mazaƙuta zai bayar da damar a yi bincike kan abubuwan da ke janyo lalurar, waɗanda ake kamantawa da irin masu janyo cutukan zuciya da hawan jini.
Haka kuma zai zai bayar da damar gano sauran matsaloli masu alaƙa da shi, kamar ƙibar wuce ƙima da sauran cutuka.
Kiyaye cin abinci mai kyau kuma mai amfani da kuma motsa jiki na taimakawa sosai wajen sauƙaƙe wanna lalura, amma ga masu ciwon siga, hanyar ɗaya tilo ita ce yin abubuwan da za su daidaita matakin sigan.
Duk da haka, Martinez da Flajo sun jaddada cewa har yanzu kimiyya na gwaji ne domin samar da cikakken maganin lalurar rashin ƙarfin mazaƙuta ko ɗaukewar sha'awa. Don haka akwai sauran jira.
Banbance na'oin ɗaukewar sha'awa da rashin ƙarfin mazaƙuta na buƙatar dogon lokaci domin bincike da nazari saboda wasu halayya da ake yi masu janyo matsalar, kamar yawaita kallon hotuna da bidiyon batsa ko kuma matsalar damuwar ƙwaƙwalwa mai alaƙa da jima'i.
Carroll ya ce: "Idan mutum yana da ciwon siga ko kuma ciwon zuciya, alaƙar ciwon nasa da kuma rashin ƙarfin mazaƙuta a bayyane take.
Amma ga yanayin da halayyar mutum ce, kamar shan barasa ko taba ko kuma kallon batsa suka janyo matsalar, to akwai gagarumin aiki kafin magance ta, saboda mazan da ke irin wannan hali ba su cika amincewa su canza daga halin nasu ba.''
Rashin ƙashi a mazaƙuta

Asalin hoton, Getty Images
Bayan muhimmancin da aka lissafo a baya, Janini na wani bincike kan illolin da matsalar za ta iya janyo wa, ta la'akari da cewa mazauta na da muhimmanci sosai ga lafiyar namiji.
Ɗan Adam ya ɗan banbanta da sauran halittu irin birrai, domin shi mutum yanayin gudanar jini ne ke janyo ƙarfin mazakutarsa.
Sauran halittu masu kama da mutum suna da wani ƙashi mai suna baculum wanda ke tallafawa sha'awarsu da ƙara ƙarfin mazaƙutar su a lokacin jima'i.
Saboda haka ne gamsuwar waɗancan halittu a wajen jima'i ba ta da wata alaƙa da sauran lafiyar jiki, kamar yadda ake da ita a jikin mutum.











