Mane zai sa riga mai lamba 17 a Bayern Munich

Asalin hoton, Getty Images
Sadio Mane zai sa riga mai lamba 17 a Bayern Munich a kakar bana da za a fara cikin watan Agusta
A makon jiya dan wasan tawagar Senegal ya kammala komawa Bayern Munich kan fam miliyan 35 kan kwantiragin da zai kare ranar 30 ga watan Yunin 2025.
Mane wanda ya koma Jamus daga Liverpool ya sa riga mai lamba 10 a kungiyar Anfield, sai dai Leroy Sane ke amfani da ita a Bayern Munich.
Mane ya fada cewar ''Na zabi lamba 17 daga tarin da aka gabatar min a Bayern, ina fatan zan lashe kyaututtuka tare da abokan taka leda da wannan lambar.
Ina fatan fara shirye-shiryen tunkarar kalubalen kakar da za a fara tare da 'yan wasan kungiyar a kwanan nan''.
Kawo yanzu wadanda suka sa riga mai lamba 17 a Bayern Munich sun hada da Jerome Boateng da Mark van Bommel da Christian Ziege da kuma Thorsten Fink.
Mane ya koma Liverpool kan fam miliyan 34 daga Southampton a Yunin 2016, ya kuma ci wa kungiyar Anfield kwallo 120 a wasa 269, wanda a kakar da aka kare ya zura 23 a raga a dukkan fafatawar da ya yi mata.
Dan kwallon tawagar Senegal ya taimaka da Liverpool ta lashe Champions League da Premier League, shi ne ya ci fenaritin da Senegal ta lashe kofin Afirka a karon farko a Fabrairu a Kamaru.









