Arsenal ta kammala daukar Matt Turner

Matt Turner

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Arsenal ta kammala daukar mai tsaron ragar tawagar Amurka, Matt Turner daga New England Revolution.

Mai shekara 28, ya koma Gunners kan kwantiragin da zai dade a Emirates, zai bar buga gasar kwallon kafar Amurka ta Major League Soccer.

Dan wasan ya tsare ragar New England Revolution karo 102 a kaka shida da ya yi a kungiyar.

A shekarar 2020 an zabe shi a matsayin dan wasan da yafi taka rawar gani a New England.

Ya wakilci Amurka wasa 18, yana cikin wadanda suka samu gurbin shiga gasar kofin duniya da kasar za ta fafata da za a yi a Qatar a bana.

Za a fara gasar kofin duniya tsakanin Nuwamba zuwa Disambar 2022.