KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 21/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Lahadi 21/06/2026.

Skip Bidiyo and continue reading
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal
  • xxx

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida

  1. Firaministan Pakistan ya isa Switzerland kan tattaunawar Iran da Amurka

    .....

    Asalin hoton, PMO

    Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif, ya isa ƙasar Switzerland domin halartar tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da Amurka, kamar yadda ofishinsa ya sanar.

    Shugaban Rundunar Sojin Pakistan, Field Marshal Asim Munir, na tare da shi a wannan tafiya, inda su biyun za su shiga cikin zaman tattaunawar.

    Pakistan ta kasance babbar mai shiga tsakani a tattaunawar zaman lafiya da ake yi tsakanin Iran da Amurka a ‘yan watannin da suka gabata.

    Tun da farko, Ma’aikatar Harkokin Wajen Pakistan ta bayyana cewa wakilai daga Amurka da Iran, tare da masu shiga tsakani daga Pakistan da Qatar, ne za su halarci wannan taro.

  2. Amurka na neman Iran ta amince da binciken nukiliyarta a musayar dala biliyan 6

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka na neman Iran ta amince da bai wa masu binciken Majalisar Ɗinkin Duniya damar duba cibiyoyin nukiliyarta, a madadin hakan kuma a ba ta damar amfani da wani ɓangare na kudaden da aka ƙwace mata, ciki har da dala biliyan 6 da ke Qatar.

    Rahoton Axios, wanda ya ambato majiyoyi guda biyu na yankin, ya ce Amurka na son a kammala zagayen farko na tattaunawa da wannan yarjejeniya wato Iran ta gayyaci masu bincike zuwa wuraren nukiliyarta.

    An bayyana cewa waɗannan cibiyoyi sun taɓa zama wuraren da Amurka da Isra’ila suka kai hare-hare a baya, kuma ba a kai irin wannan bincike ba tun watan Yuni 2025.

    A musayar wannan amincewa, Amurka na shirin ba Iran damar samun wasu daga cikin dukiyarta da aka ƙwace a ƙasashen waje, inda za a fara da asusun dala biliyan 6 da ke Qatar.

    Rahotannin sun ce za a takaita amfani da kuɗin ne ga sayen kayayyakin jin-ƙai kamar abinci da magunguna, ba tare da amfani da shi a wasu harkoki ba

    A lokaci guda, tattaunawar za ta kuma mayar da hankali kan batun shirin nukiliyar Iran da kuma ƙoƙarin cimma tsagaita wuta a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Sai dai rikicin da ke faruwa a Lebanon na barazana ga nasarar wannan shiri.

    Mataimakin Shugaban Amurka, JD Vance, ya ce wannan rikicin na iya kawo cikas ga tattaunawar.

    A baya, Isra’ila da Hezbollah sun amince da tsagaita wuta a ranar Juma’a domin kauce wa tangarɗa ga tattaunawar amma kuma Isra;ila ia keta yarjejeniyar.

  3. Oyebanji na APC ya lashe zaɓen gwamnan Ekiti

    ....

    Asalin hoton, Biodun Oyebanji/Twitter

    Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Ƙasa (INEC) ta ayyana Gwamna Biodun Oyébanji a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Ekiti da aka gudanar ranar Asabar 20 ga Yuni, 2026.

    Shugabar tattara ƙuri’u, Farfesa Adenike Oládìjì, ta sanar da sakamakon da sanyin safiyar Lahadi, inda ta bayyana cewa Oyébanji na jam’iyyar APC ya samu ƙuri’u 319,224.

    Ɗan takarar jam’iyyar PDP, Wọlé Olúyẹdẹ, ne ya zo na biyu da ƙuri’u 40,543, yayin da ɗan takarar ADC, Dáré Bẹ́jìde, ya samu ƙuri’u 12,872.

    Gaba ɗaya, ‘yan takara 14 ne suka fafata a zaɓen, kuma Oyébanji ya samu nasara a dukkan ƙananan hukumomi 16 na jihar.

    A babban birnin jihar, Ado Ekiti, jam’iyyar APC ta fi ƙarfi inda Oyébanji ya samu ƙuri’u 38,026, wanda ya nuna gagarumar nasara a duk fadin jihar.

    Da wannan sakamako, Oyébanji ya sake lashe zaɓen gwamna karo na biyu, abin da ya zama tarihi a jihar saboda ba kasafai gwamnoni ke samun nasarar wa’adi biyu a jere ba tun daga kafuwar jihar a 1996.

    Bayan sanar da nasarar, gwamnan ya gode wa al’ummar jihar Ekiti, yana mai cewa wannan babbar amincewa ce daga jama’a ga aikin da gwamnatinsa ke yi.

  4. Assalamu alaikum

    Barka da zuwa shafin BBC Hausa na kai-tsaye.

    Kamar kullum, yau ma za mu muku labaran abubuwan da ke faruwa game da yaƙin Iran da wasu muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a wannan rana ta Lahadi.

    Za ku iya yin tsokaci a shafukanmu na sada zumunta: Facebook, X, instagram, YouTube da kuma zaurenmu na WhatssApp.