Inter Milan ta dauki aron Lukaku daga Chelsea

Asalin hoton, Rex Features
Inter Milan ta amince da yarjejeniyar daukar aron Romelu Lukaku kan kaka daya daga Chelsea.
Chelsea ta dauki dan wasan mai shekara 29 daga Inter Milan kan fam miliyan 97.5 a Augustan 2021.
Kudin da zai buga wasannin aron zai kai fam miliyan 6.9 a Italiya.
Dan wasan tawagar Belgium ya ci kwallo 15 a dukkan wasannin da ya yi wa Chelsea a kakar da aka kamma ta bana.
Har da kwallo takwas a wasa 26 da ya zura a raga a gasar Premier League da Manchester City ta lashe.
Haka kuma an fahinci cewar Lukaku zai amince ya rage albashinsa, domin ya sake komawa Inter, wadda ya lashe Serie A da ita a 2020/21.
Yanayin tattalin arzikin kungiyoyin Italiya, ba zai sa Inter ta iya biyan albashin Lukaku ba, ko sayen dan wasan daga Chelsea.
Lukaku ya bar Chelsea ya koma taka leda a Everton kan fam miliyan 28 a 2014, wanda ya koma Stamford Bridge daga Inter a bara.
Chelsea ta sayi dan wasan daga kungiyar da ke buga Serie A a matakin wanda ta dauka mafi tsada a tarihi, kan kwantiragin kaka biyar.
Lukaku ya bayar da hakuri, bayan wata hira da ya yi, wanda ya ce baya jin dadin rawar da yake takawa karkashin koci, Thomas Tuchel, yana kuma son sake komawa Inter Milan nan gaba.
Chelsea wadda za ta buga Champions League a kaka mai zuwa ta kare a mataki na uku a Premier League, sannann ta rasa FA Cup da League Cup a hannun Liverpool a wasannin karshe a kakar da ta wuce.
Iner Milan, wadda itama za ta fafata a babbar gasar kofin Zakarun Turai, ta yi ta biyu a Serie A da AC Milan ta lashe karon farko, bayan kaka 11.









