Bayern ta kammala daukar Sadio Mane

Sadio Mane

Asalin hoton, Bayern Munich

An wallafa

Sadio Mane ya kammala komawa Bayern Munich kan fam miliyan 35 daga Liverpool kan kwantiragin kaka uku.

Liverpool za ta karbi fam miliyan 27.4 da karin yuro miliyan shida kan yawan buga wasanni da karin yuro miliyan uku kan rawar da zai taka da nasarorin da Bayern za ta samu.

Tun farko Liverpool ba ta sallama tayi biyu da Bayern ta yi wa Sadio Mane ba, dan kwallon tawagar Senegal, wanda yarjejeniyarsa zai kare a Anfield a karshen kakar da za mu shiga.

Mane ya koma Liverpool kan fam miliyan 34 daga Southampton a Yunin 2016, ya kuma ci wa kungiyar Anfield kwallo 120 a wasa 269, wanda a kakar da aka kare ya zura 23 a raga a dukkan fafatawar da ya yi mata.

Dan kwallon tawagar Senegal ya taimaka da Liverpool ta lashe Champions League da Premier League, shi ne ya ci fenaritin da Senegal ta lashe kofin Afirka a karon farko a Fabrairu a Kamaru.

A makon jiya Liverpool ta tabbatar da daukar dan kwallon tawagar Uruguay, Darwin Nunez daga Benfica kan fam miliyan 64.