Kofin Carabao : Liverpool za ta yi wasan ƙarshe da Chelsea

Luis Diaz ne ya ci wa Liverpool

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Luis Diaz ne ya ci wa Liverpool ƙwallon
An wallafa

Liverpool za ta kara da Chelsea a wasan karshe na cin Kofin Carabao bayan da ta yi nasarar fitar da Fulham daga gasar.

Kungiyar ta Anfield ta samu wannan nasara ne bayan da suka tashi kunnen doki - 1-1 a gidan Fulham, Craven Cottage, ranar Laraba da daddare, a wasansu na biyu.

Kasancewar a karawarsu ta farko a Anfield, Liverpool ta doke Fulham da ci 2-1, sakamakon ya kasance Reds din ta yi galaba da ci 3-2, wanda hakan ya sa za ta fafata a wasan na karshe a Wembley ranar 25 ga watan Fabrairu mai kamawa.

A karawar ta Laraba Luis Diaz ne ya ci wa Liverpool kwallonta a minti na 11, amma kuma Issa Diop ya farke wa mai masaukin bakin a minti na 76.

Dukkanin kungiyoyin biyu sun kai wasan zagaye na hudu a gasar cin kofin hukumar kwallon kafa ta Ingila, FA, inda a karshen makon nan Fulham za ta karbi bakuncin Newcastle a ranar Asabar, ita kuwa Liverpool za ta kasance a gida da Norwich ranar Lahadi.

Yanzu dai Fulham za ta ci gaba da neman damar ta ta farko ta kaiwa wasan karshena cin kofin na EFL a tarihi, da ba ta taba yi ba.

A ranar Talata ne Chelsea ta samu nasarar zuwa wasan na karshe bayan da ta doke Middlesbrough ta gasar kasa da Premier, wato Championship, wadda ta ci karawarsu ta farko 1-0.